Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":
Home -- Hausa -- 20-For Readers of the Qur'an -- 033 (The Miraculous Sign Of Allah)
This page in: -- Arabic? -- English -- French -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Somali -- Yoruba

Previous Chapter -- Next Chapter

20. Ga masu karatun Kur'ani
LITTAFI 4 - SUNAYE DA SIFFOFI NA KRISTI A CIKIN KUR'ANI

8) Alamar Allah ta Mu'ujiza (Ayatollah) (آية الله)


Wahayin Kur'ani ya furta cewa Kristi alama ce ta mu'ujiza ga 'yan adam kuma alamar Allah mai banmamaki ga talikai. Wannan gata tana nufin haihuwarsa ta musamman, rayuwarsa marar zunubi da hawan nasara zuwa sama. Dan Maryama ya ƙaunaci har ma masu tsananta masa, yana jinƙai ga matalauta kuma yana warkar da duk wani mara lafiya da ya zo wurinsa. Ya bayyana sirrin Allah, ya fuskanci munafukai na addini da gaskiya, ya gafarta ma wadanda suka kashe shi. Allah Ya sanya shi alama ga mala’iku da mutane domin su gani, a cikin Ɗan Maryama, kamannin nufin Allah. Kamar yadda Kristi ya rayu, kowane mutum ya kamata ya rayu domin ya cika nufin Allah.

Maganar Kur'ani game da Kristi a matsayin Ayatollah: Suratu Maryam 19:21; -- al-Anbiya 21:91; -- al-Mu'minun 23:50.

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on August 29, 2024, at 08:38 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)