Home -- Hausa -- 14-Christ and Muhammad -- 007 (The Signs of Muhammad and of Christ)
This page in: -- Cebuano -- English -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Yoruba
Previous Chapter -- Next Chapter
14. ALMASIHU DA MUHAMMADU
Gano a cikin Alkur'ani game da Almasihi da Muhammadu
6. Alamomin Muhammadu da na Kristi
Malaman musulmai suna da'awar cewa mu'ujizozin da Allah ya baiwa Muhammadu sune ayoyin Kur'ani a cikin Surori. Saboda haka, abubuwan al'ajabi na Muhammadu ba ayyuka bane amma kalmomi ne.
Kur'ani ya yi shaida a madadin Yesu, yana bayyana ayyukansa na musamman da manyan ayyukan warkarwa. Kristi bai la'anci makiyansa ba, kuma baiyi kama da azzalumi ba. Ya bayyana kansa a matsayin mabulbular alheri kuma tushen kauna da jinkai. Ikon Allah yafito daga gareshi ta wurin al'ajibai da yawa da yayi.