Previous Chapter -- Next Chapter
6) Fadin Gaskiya (قول الحق)
Wannan suna na Ɗan Maryama na musamman ya bayyana sau ɗaya a cikin Kur'ani (Sura Maryam 19:34). “Gaskiya” (al-Haqq) a cikin wannan suna yana sanya “Allah da kansa”, domin laƙabin “Gaskiya” (al-Haqq) ya zo sau da yawa a cikin Kur’ani a matsayin sifa da sunan Allah. Yana rike da dukkan hakkoki na rayuwa da lahira kuma shi ne tushen gaskiyar talikai.
Tun da Kristi shine Maganar Allah da aka bamu cikin siffa ta jiki, yana daidai da kalmar da ke fitowa daga bakin Maɗaukaki. Idan tushen Kristi shine “Gaskiya”, to, shi da kansa, “Gaskiya ne” kuma, domin gaskiya ce kaɗai za ta iya fitowa daga “Gaskiya”. Duk wanda ya kalli Kristi zai iya ganin Maganar Allah mai tafiya da gaskiyarsa a cikin siffar jiki.