Previous Chapter -- Next Chapter
Ayyukan Mugunta
Duk da irin wannan tunanin na hasken, har yanzu ban tabbata ba game da cetona. Kristi ya ce a cikin Yohanna 8:32:
"Za ku san gaskiya kuma gaskiya za ta 'yanta ku."
Lokaci ya yi da za mu san gaskiya, domin mu sami 'yanci cikin Yesu Almasihu. Yesu yana da iko mafi girma bisa kowa domin shi Ɗan Allah ne.
Ka tuna Romawa 14:12 ta ce, “Kowannenmu za ya ba da lissafin kansa ga Allah.”
Romawa 14:11 ta ce, “Na rantse, in ji Ubangiji, kowace gwiwa za ta durƙusa a gare ni.”
Kuma a cikin Filibiyawa 2:10 mun karanta cewa, “cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta rusuna”.
Ba zan iya lissafta dukan abin da na yi a cikin duhu ba, domin ayyukana suna da yawa. An yi ta munanan ayyuka da dama irinsu bokaye, laya, zobe, Baduhu, Bante, Shashautau, Kaudabara, Damara, Daga, Kambu, Guru, rubuce-rubuce a kan alkalami da shan ruwan da aka zuba a kan allo don goge rubutun. Akwai mugunta da yawa dangane da wannan. Amma muminai ku yi ƙarfin hali cewa yaƙinmu ba na jiki ba ne.
“ba gaba da nama da jini ba, amma gba da mulkoki, da ikoki, da masu mulkin duhun wannan duniyar” (Afisawa 6:12).
Game da dukkan laya da sauran iko da na ambata, dole ne in ce, da akwai ceto a Musulunci, da Musulmi sun dogara ga Allah maimakon dogaro da irin wadannan laya. Wadannan munanan ayyuka a tsakanin musulmi suna rushe duk wani ceto a Musulunci. Wani abu da ya kamata a yi la'akari kuma shi ne cewa duk wani bokanci, tunani mai wuce gona da iri, hasashen tunani da duk wani iko na asirce ba su da wani tasiri a kan Kirista cikin Almasihu, domin a ko da yaushe jinin Yesu yana wanke kowane hari na duhu da haske ko da yaushe yana nuna kan kowane mai bi. Idan ana kiran siffar Kirista a cikin calobash ko madubi, kawai za ku ga HASKE, kuma wannan shine. hasken Kristi! Allahumma Amin! Wannan tabbaci ne na fifikon Haske akan ikon duhu. Yayin da kuke karantawa, kar ku manta da kiran Yesu Kiristi, wanda yake son mai karanta wannan saƙon ya fara auna kansa ko kanta. Shaidar da ke biyo baya tana da ban mamaki da cike da tausayi.