Grace and TruthThis website is under construction ! |
|
Home Afrikaans |
Home -- Hausa -- 20-For Readers of the Qur'an -- 091 (The Parable of the Royal Wedding Feast)
Previous Chapter -- Next Chapter 20. Ga masu karatun Kur'ani
LITTAFI 6 - KO KA SAN HIKIMAR KRISTI?
32. Misalin Bikin Daurin Aure“2 Za a iya kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa liyafa. 3 Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata zuwa biki, amma ba su yarda su zo ba. 4 Ya sāke aiki waɗansu bayi ya ce, ‘Ku faɗa wa waɗanda aka gayyata, Ga shi, na shirya abincin dare. shanuna da kibana duk an yanka su, an shirya komai; ku zo wurin biki.’ 5 Amma ba su kula ba, suka tafi, ɗaya ya tafi gonarsa, wani kuma ya tafi sana’arsa, 6 sauran kuwa suka kama bayinsa, suka wulakanta su, suka kashe su. 7 Sarki ya husata, ya aiki sojojinsa, suka hallaka masu kisankai, suka cinna wa birninsu wuta. 8 Sai ya ce wa bayinsa, ‘An shirya biki, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9 Saboda haka ku tafi manyan manyan tituna, duk waɗanda kuka samu a can, ku gayyace su zuwa wurin biki.’ 10 Sai bayin suka fita a titi, suka tattara dukan waɗanda suka samu, na mugunta da nagari. dakin daurin aure ya cika da baki. 11 Amma da sarki ya shigo ya leƙa masu baƙon abinci, sai ya ga wani mutum a can ba sa saye da tufafin biki, 12 sai ya ce masa, ‘Aboki, ta yaya ka shigo nan ba da tufafin biki?’ Sai ya kasa magana. 13 Sa'an nan sarki ya ce wa barorin, ‘Ku ɗaure shi hannu da ƙafa, ku jefa shi cikin duhu. A wurin nan za a yi kuka da cizon haƙora.’ 14 Gama ana kiran mutane da yawa, amma kaɗan ne aka zaɓa.” (Matiyu 22:2-14) |