Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":

Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 6 Unity of the Trinity

This page in: -- Arabic? -- Cebuano -- Chinese -- English -- French -- Georgian -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Kirundi -- Russian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Uzbek -- Yoruba

Previous booklet -- Next booklet

01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI

6 - Ta yaya za a Bayyana wa Musulmai Asirin Dayantakan Triniti?6.01 -- Ta yaya za a Bayyana wa Musulmai Asirin Dayantakan Triniti?

Duk wanda yayi magana da musulmi ba da dadewa ba zai gane yana daukan bangaskiyar mu cikin Allah Uba, Da da Ruhu Mai Tsarki ya zama zunubin da ba a gafartawa. A shahadan musulmai an nanata cewa babu wani allah sai Allah! Duk wanda yana gama mahalicci da Da ko Ruhu Mai Tsarki akan dauke shi a matsayin magabcin Allah da duka Mala’ikunsa (Surorin al-Baqara 2:97-98; al-Ma’ida 5:73).

6.02 -- Kin Amincewa Da Triniti Mai Tsarki A Islama

Kin amincewa da Triniti Mai Tsarki na musulmai na da fuskoki dabam- dabam. Za mu takaita wannan a abubuwanda zasu kafa tushe na tattaunawa da musulmai.

Muhammadu ya kalubalanci Kirsta: “kada kuce uku! Wannan zaifi muku alheri!” (Sura al-Nisa’ 4:171). “Ba za a taba samu uwar Allah ba balle ta haifi da daga wurin Allah” (sura al-Ma’ida 5:116). “Kada wani ya amince da wani mutum a matsayin Ubangijinsa” (Sura Al’imran 3:64; al-Tawba 9:31) “Allah ba Kristi bane” (Surorin al-Ma’ida 5:17, 72; al-tawba 9:31) “ga madaukaki zai zama karamar haki ne ya hallaka Kristi da uwarsa, in sunce su alloline” (Sura al-Ma’ida 5:17).

6.03 -- Kin Amincewaa da Allahntakan Yesu Kristi

Shaidar cewa Yesu Kristi ne Dan Allah an kishi sau 17 a Kur’ani (sura al-tawba 9:30). An kira Isa dan Maryama ne kawai amma ba kira shi Dan Allah ba. An dauke shi a halittaccen mutum ne kamar Adamu (Sura Al’mran 3:59). Allah ya Umurta: Ka kasance! Sai ya kasance (Surorin al-Baqara 2:117; Al’imran 3:47, 59; Maryam 19: 35). Wannan ba daidai ba ne, a Kur’ani Allah ya ce: “Mun hura ruhunmu a cikin ta (Maryama)”; haka aka halicci Isa a cikinta (surorin al-anbuya 21:91; al-Tahrim 66:12) Musulmai zasu iya gaskanta haihuwar Kristi tawurin budurwa Maryama, amma kuma sai su fadi wani abu sabanin shaidar bangaskiyar Krista cewa; An halicce shi, Allah bai haifeshi ba.

Kur’ani ya nuna cewa Kristi bawan Allah ne (surorin al’mran 3:172; Maryam 19:30), Manzon sa ne (Surorin al-Baqara 2:87; al’imran 3:49, 53; al-Nisa’ 4:157, 171; al-Ma’ida 5:75; al-an’am 6:6) kuma annabinsa (sura Maryam 19:30). Ya mika wuya ga Allah (Surorin al-Ma’ida 5:52, 117; al-tawba 9:31), yayi adu’a ga elohim (allahumma); (sura al-Ma’ida 5:114) Allah Ubangijinsa ne mai bashi umurni (Surorin Al’imran 3:51; Al-Ma’ida 5:72; 114, 117); Maryam 19:36; al-shura 42:13; al-zukhrfu 43:64).

A wadannan ayoyi hamsin na Kur’ani an tube wa Yesu Allahntakansa. Gargadin manzo Yahaya ya shafi Musulmai ma (I Yahaya 2:18-25; 4:1-5).

6.04 -- Kin Amincewa da Allahntakar Ruhu Mai Tsarki

Yana da kyau mu sani cewa Kur’ani ba bata wa Kristi suna ne yayi kadai ba, amma ya ce Ruhu Mai Tsarki halitta ne ba Allah ba. Allah ya furta sau da yawa yana cewa “Ruhunmu” (Surorin Maryam 19:17; al-anbiya 21:91; al-Thrim 66:12), kokuwa “ruhu na” (surorin sad 38:72; al-Ankabut 29:15), amma a kowane hali an dauki wannan a halitta ne ba Allah ba. A Islama babu wani Ruhu Mai Tsarki wanda shi kadai ne domin Allah daya ne ba biyu ba ko uku.

An bayyana a litattafan Islama cewa Jibrai’lu shine ruhu daga wurin Allah (surorin al-Baqara 2:97 – 98; al-tahrim 66:4) wanda ya kai wahayin Ubangijinsa zuwa ga Zakariyya, Maryama, Isa da Muhammadu. An nuna shine “ruhu na mai tsarki”, wanda ya karfafa Yesu yayi mu’ujjizansa (Surorin al-Baqara 2:87, 253; al-Ma’ida 5:110; al-Nahl 16:102). A Islama wannan ruhu bawan Allah ne a karkashin umurnin sa (surorin al-qadar 97:4; al-Isra’ 17:85; al-shura 42:52), wanda yake aikata umurninsa da aminci (sura al-shu’ara 26:193). Musulmai suna girmama shi sosai, ko da shike basu san ko wanene shi.

6.05 -- Menene aka Rasa a Islama?

In mun bi wannan ‘yar gajeruwar gabatarwa, wadanda suna iya tunani na ruhaniya zasu gane wadansu ka’idodi na tattaunawan mu da musulmai: A Islama baza a iya samun Uba, ba Da ba Ruhu Mai Tsarki (Sura al-Ihlas 112:1-4).

‘Babu kariya na ruhaniya a karkashin kulawa na Allah Uba, babu dangantaka na kut-da-kut da madaukaki, babu tabbacin gafarar duka zunubai, babu yiwuwan yarda da Triniti Mai Tsarki (I korintiyawa 12:3; Romawa 8:8-12, 15-16), babu albarkar Ruhu (Galahyawa 5:16-26) kuma babu begen rai madawwami (Yahaya 11:25-26). In da ba a yarda da Ruhu Mai Tsarki, babu tunani na ruhaniya babu kuma rayuwar Krista.

Banda kokarin mu na yi wa musulmai bishara, naciya cikin adu’a ya zama tilas ne saboda Yesu Kristi zai shirya mutane tawurin Ruhunsa kuma ya basu ikon sauraron maganarsa, su gane, kuma su aikata. Babu wanda zai iya bayyana asirin Triniti ga musulmi sai in Ruhu Mai Tarki ya sa bukata a cikinsa na neman Allah na gaskiya, da kuma shiri ya saurari Maganarsa kuma ya sami haske na ruhaniya da kan haskaka duhu wanda yake cikin zuciyar mutum.

In muna bukatar bayyana bishara ga musulmai kada mu ji haushi da kiyayya wanda ruhu mai gaba da Kristi wanda zai yi da kai. Kaunar Kristi yafi dukan sarkokin Islama karfi. In kana neman abin muhawara da zai taimakeka ka bayyana dayantakan Triniti Mai Tsarki ga musulmai, ga hanyoyi guda biyar:

6.06 -- Shaidar Tsohon Alkawali Akan ‘Dayantakan’ Trinity Mai Tsarki

A Attaura da Annabawa zamu ga a wurare da dama an yi ambaton Allah Dayane cikin uku. Shaidar Tsohon Alkawali yana da muhimmanci ga musulmi wanda yake da sha’awa domin yana nuna cewa ba Krista ne suka kirkiro batun Triniti ba amma, yana bayyana yadda Allah yake kafin kafawan duniya.

Ayoyi na farko a Baibul sun bada shaida akan Triniti:

A sa’ad da Allah ya fara halittar sama da duniya, duniya bata da siffa sarari ce kawai, duhu kuwa yana lullube da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. Allah yace, ‘Bari haske ya kasance’”, (Farawa 1:1-3).

A cikin wannan gabatarwa na Baibul, mun karanta game da Allah, Ruhunsa da kalmarsa. Marubucin bisharar Yahaya ya shaida cewa Allah ya halicci duniya tawurin Yesu, kalmansa da ya zama jiki (Yahaya 1:1-4).

Aya ta farko a Baibul zata jagorance mu rokon Allah da ya aiko da ruhunsa yayi shawagi a bisa musulmai, iyalansu, kauyuka, birane da kasashen su. Allah ya bude tunaninsu da shirya zukatansu har lokacin da Allah zai ce “Bari haske ya kasance”, sai kuwa ya kasance!

A Farawa 1:26 Allah ya ce: Bari Mu yi mutum cikin siffarmu da kamannin mu!

Allah (elohim) wani lokaci yana magana cikin jam’i (mu) wanda yana nuna yiwuwan Triniti. Yahudawa da musulmai sukan kira wannan bautan alloli da yawa. A tattaunawarsa da wakilai na Krista daga Wadi Najran (arewacin Yemen), Muhammadu ya tabu sosai da wannan aya har bayan haka ya bar Allah ya shiga magana cikin jam’i a Kur’ani.

ELOHIM, wanda shine sunan Allah a Ibrananci jami’ne “El” na nufin iko, girma da karfi (Matiyu 26:64), “him” na nufin “su”, saboda akan iya karanta Elohim kamar haka “Mai iko jam’i ne” Kalma “Allah” a Islama za’a iya gane shi daidai haka, har a iya karanta “al-el-hu” ya zama “shi mai iko” (Mutum daya kadai)! Allah na Baibul dayantuwa cikin Jam’i ne, Muhammadu ya karbi kalma Elohim cikin harshen larabci yayi amfani da shi a “Allahumma” sau biyar a muhimman wurare a Kur’ani (surorin al’lmran 3:26; al-Ma’ida 5:114; al-anal 8:32; Yunis 10:10; al-zumar 39:46). A gareshi, sunan Allah a Tsohon Alkawali, ya iya zama mabudi na amsar adu’oi.

A Farawa 18:1-3 mun karanta cewa mutane uku sun ziyarci Ibrahim. Amma ya kira su: “Ubangiji na” wanda mufuradi ne. A littafin kidaya 6:24-27, zamu sami albarkar Haruna, a cikinta an ambaci “Ubangiji” sau uku. Wadansu ikklesiyu sun danganta wannan da albarkan Uba, albarkar Da da albarkar Ruhu Mai Tsarki, a matsayin albarka na Ubangiji “daya”.

A Zabura 2:1-4, mun karanta akan tawayen mutum daga Ubangiji da shafaffen sa (Masihu). Amma a mai iko ya yi musu dariya sa’annan ya bada kalma guda: “kai da na ne, Yau ne na zama mahaifinka” (Zabura 2:7) wannan budi an yishi ne wajen shekaru 1,000 kafin zuwan Yesu Kristi. Wannan na nuna fitowar Dan a fili daga cikin Uba cikin ruhaniya kafin kafa duniya, wanda bai kamata a kuskure shi da haihuwa cikin jiki daga Maryama ba. Yesu ya rayu da dadewa kafin bayyanuwarsa a jiki. Shi Allah madawwami ne daga Allah madawwami! (Yahaya 1:14; Filibbiyawa 2:6-7).

Ishaya 9:6, Misali ne da ke bada hasken dayantaka na triniti”. Gashi, an Haifa mana da! Mun sami yaro! Shi zai zama mai mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al’ajabi” “Allah madaukaki”, “Uba madawawami”, “sarkin salama”.

Wannan aya na bayana cewa Da na alkawali ba Mai bada shawara da Madaukaki bane kadai, amma Uba Madawwami ne da kansa ya zama mutum. Ta yaya aka sami mahaifin jariri wanda shine jaririn da kansa? Wannan budi na musamman an saukar da shi kimanin shekaru 700 kafin Yesu ya rayu cikin jiki a duniya. Wannan nassi babban shaida ne na kasancewar Triniti.

Zabura 110:1 Ya bayyana wannan dawwamammen gaskiya. An rubuta: Ubangiji ya ce wa Mai girma, Sarkina, “zauna nan a dama na, Har in sa makiyanka a karkashin sawayenka”.

Ikklesiya ta farko ta fahimci wannan aya a alkawalin da ya bayyana komawar Yesu a sama da sarautarsa (Matiyu 26:64; Ayukan Manzanni 2: 25, 34; I korintiyana 15:25; Filibbiyawa 2:8-9; Ibraniyawa 10:12-13). Dan ya zauna tare da Uban akan kursiyi (Wahayin Yahaya 3:21) duka suna mallakar duniya a dayance. Tunda Dan ya gama fansar dan adam, Uba zai sa duk makiyansa “a karkashin sawayensa!” Wannan alkawali ya hada da kowane iko da ke gaba da Kristi-wannan na kiranmu zuwa bangaskiya cikin nasarar Allahnmu.

Wadanda suke magana da musulmai su nanata alkawarai da suke a Tsohon Alkawali don bayyana dayantakan Kristi da Ubansa, domin cikarsu a Sabon Alkawali zai iya zama “tilas” ga musulmi mai aminci ya yarda da su. Duk inda Allah ya umurta, dolene a aikata ba jinkiri. In yayi alkawali, babu shakka zai tabbata. Babu wanda zai hana cikar wahayinsa. Ga wadansu musulmai, alkawaran Allah 333 na Tsohon Alkawali da aka cikasu a Sabon Alkawali zasu iya zama kakkarfan shaida na dayantakan Triniti Mai Tsarki. Wadannan alkawarai da cikarsu, ya kamata a karanta kuma a haddace su.

6.07 -- Shaida Ta Sabon Alkawali Ga Dayan Takan Trinity Mai Tsarki

Litattafan Bishara guda hudu, wasikun manzanni da Wahayin Yahaya suna cike da koyaswa akan dayantakan Uba, da Da, da Ruhu Mai Isarki. In mun sami musulmai wadanda suke shirye su karanta Linjila, sai mu karfafa zancen dayantaka na Triniti. Musulmai da Yahudawa sun fahimci Allah “Makadaici ne”. Wadansu Krista sukan nanata akan alloli uku. Dole su tuba su koma ga ’ya’yan Ibrahim saboda su koyi yadda zasu iya bayyana dayantakan Triniti Mai Tsarki a cikin tunaninsu.

Matiyu 1:23; Gashi, budurwa zata yi juna biyu, ta haifi da, za’a kuma sa masa suna immanuwel’ (Ma’anar Immanuwel kuwa, Allah na tare da mu).

Immanuwel daya ne cikin sunaye 250 na Yesu a cikin Baibul shi cikakken Allah ne kuma cikakken mutum a lokaci guda. A cikinsa Allah ya kasance tare da mu. Wannan alkawali a Ishaya 7:14 da cikansa zai iya bamu karfafawa.

Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dare, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, har ya sauka kansa. Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, ‘wannan shine Dana Kaunataccena, wanda nake farin ciki da shi kwarai”. (Matiyu 3:16-17).

Ga Musulmi, labarin baftisman Kristi (Matiyu 3:16-17; Markus 1:9-1; Luka 3:21 – 22; Yahaya 1:31-34; 5:37-38) gaskiya ne mai ban mamaki: an ji murya daga sama! Musulmai sun gane cewa wannan wahayi ne daga sama. Babu wanda zai iya hana Madaukaki yin magana. Wanene zai iya hana shi fadin: “wannan shine dana kaunataccena, wanda nake farinciki da shi kwarai”? Ruhu Mai Tsarki ya sauko bisansa a mai karfafashi don hidimarsa ko da shike haihuwarsa tawurin Ruhu Mai Tsaki ne. Yesu ya sa an yi masa baftisma a kogin Urdun ko da shike Yahaya mai Baftisma bai so haka ba. Yesu bashi da zunubi kuma bashi da bukatan ayi masa baftisma. Amma ba da sanin mu ba ya dauki zumubanmu a kansa tun sa’anda ya fara hidima.

 • Shiya sa mai baftisma Da babban murya yace: “Kun ga, ga Dan rago na Allah, mai dauke zunubin duniya!” (Yahaya 1:29).
 • Shiyasa Ruhu Mai tsarki ya sauko bisansa kamar kurciya ya kuma kasance a bisansa.
 • Shiyasa Uba yayi shaida: “Wannan shine Dana kaunataccena, wanda nake farinciki da shi kwarai!

Baftismar Kristi muhimmin nassi ne ga Ikklesiya na fahimtar dayantakar Triniti Mai Tsarki, Uba, Da da Ruhu Mai Tsarki suna aiki tare don ceton mutane daga farkon hidiman Yesu.

Matiyu 12:18 Na magana akan bawan Ubangiji wanda ya zaba, wanda yake kauna kuma yana jin dadin sa. Zai sa Ruhunsa a cikinsa saboda ya iya yin shelar adalci ga al’ummai. Wannan cikar (Ishaya 11:1-5) ya nuna cewa Ubangiji, Bawansa da Ruhunsa dayane kuma suna dayance a cikin kasancewan Yesu. Duka rayuwansa ba shi kadai ne ba amma dayane cikin Triniti (Luka 4:18-19): “Ruhun ubangiji na tare da ni, Domin ya shafeni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni inyi shelar saki ga daurarru, in kuma bude wa makafi ido, in kuma ‘yanta wadanda ke adanne, in yi shelar zamanin samun karbuwa ga Ubangiji”.

A Luka 4:18, Yesu Kristi ya gabatar da kansa a Nazarat da cewa “Ruhun Ubangiji na tare da ni! …” Dan wannan batu na nuni ga Triniti Mai Tsarki domin Allah, Ruhu da Yesu sun bayana a dayance. Kristi ya bayyana wannan gaskiya yace: “domin ya shafeni” kalma Kristi na nufi: masihu, shafaffe. Don menene aka shafe Yesu? “Ya yi wa matalauta bishara da kuma shelar saki ga daurarru” (Duk wanda ya karbi shafewa na Sabon Alkawali (II Korintiyuwa 1:21; I Yahaya 2:20,27) zai iya maimaita wannan shaida na Yesu, Krista kan cika Krista ne idan Ruhun Ubangiji na bisansa kuma yana iza shi don ya cika, nufinsa (Ishaya 61:1-2; Romanwa 8:10-16).

An mallaka mini dukan iko a sama da kasa. Don haka sai ku je ku almajitar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Da, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abinda na umurce ku. Gashi, ni kuma kullum ina tare da ku har matukar zamani” (Matiyu 28:18-20).

A cikin babbar umurni mun karanta cewa duk wanda ya yi kudurin bin Kristi sai a yi masa baftisma cikin sunan Uba, da na Da na Ruhu Mai Tsarki. Me ya sa wannan umurni ba a ce “cikin sunayen” ba? Domin ukun daya ne! Ainihin sunan Allahn mu shine “Uba da Da da Ruhu Mai tsarki”.

Yahaya 10:30, A bishara daga hannun Yahaya mun karanta shaida mai daukan hankali na makiyayi mai kyau: “Ni da Ubana Daya ne” an ce “biyu”?! A’a amma “daya”! Me yasa mukan yi wa’azi game da biyu, in Yesu yace daya? Wannan ganewa na sama – sama na bukatan masu bishara su tuba wa musulmai da Yahudawa. Uban da Dan dayane ba biyu ba! Dole mu canza ra’ayinmu kuma mu koyi yin tunani ba akan ka’idodi da abubuwan da za’a iya gani ba amma har ma a hanyar gaskiya ta ruhaniya, kuma mu shirya kanmu don masu neman gaskiya na kasashen Gabas.

A bayyananniyar shaidar Yesu game da kansa (Yahaya 14:9-11) mun karanta: “Wanda ya gan ni ya ga uban!” Da wannan furci Yesu ya shaida dayantakansa da ubansa tawurin bayyanuwarsa wanda ya zama cikar Farawar 1:27. Bayan haka Yesu yace Kalmomin da yake furtawa ba nasa bane, amma na uban ne, wanda ke zaune a cikin sa, ba yana magana ne a cikinsa ba kadai amma yana aikata abubuwan da yake fadi. Yesu ya kasance a cikin Uba, Uban kuwa a cikinsa. Wannan ya jaddada dayantaka cikin rayuwa da Ruhu.

Cikin Yahaya 14:23 Yesu ya ce: “Kowa ke kaunata, zai kiyaye maganata, ubana kuwa zai kaunace shi, zamu zo wurin sa mu zauna tare da shi”.

Yesu ya bayyana kasancewar Ruhu Mai Tsarki a cikin mabiyansa. A wannan aya Ruhu ya bayyana ba kawai a cikin dayantakan Uba da Da ba, amma ya wakilcesu a matsayin ruhunsu ma.

A alkawarai uku game da mai shawara wanda zai zo (Yahaya 14:26; 15:26; 13-15) Mun karanta halaye 10 na dayantaka da hada hannu na Uba da Da da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu baya daukaka kansa ko wadanda ya basu baye-baye amma yana daukaka Yesu. Yesu kuma bai yi fahariya da kansa ba amma yakan girmama ubansa. Allahn mu mai hankali ne da tawaliu (Matiyu 11:28-30)! A cikin Triniti Mai Tsarki babu hatsarin yin hargitsi. Babu wanda ke maida kansa babba amma kowa na kokarin girmama dayan ne. Wannan dalili ne ya sa Uba ya mallaka wa Dan sa duka iko a sama da duniya; Yesu kuma ya ba Ruhu Mai tsarki ikon gina Ikklesiya. Tawali’u irin na Allantaka shine asirin dayantaka na Triniti Mai Tsarki zamu iya gane Allahnmu muddin mun barshi ya canza rayuwa ya sa mu zama da tawali’u kamar yadda yake. Wannan yayi sabani da fahariyar Allah da mabiyansa a Islama. (sura al-Hashir 5:23).

Yahaya 17:21-23: Yesu a cikin adu’arsa ta babban firist yayi adu’a domin mabiyansa: “Domin su zama daya, kamar yadda mu daya ne; ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama daya sosai” …

A wannan zance cikin Triniti Mai Tsarki Yesu ya takaita wannan asiri: “Mu daya ne” wannan gaskiya na ruhaniya shine dalilin da ya raba mu da Yahudawa da Musulmai. Dayantuwa ta ruhaniya wanda ke cikin Uba da Da da Ruhu Mai Tsarki shi ne harsashen bangaskiyarmu. Wannan dayantaka kuwa bai bayyana kamar abubuwa uku da za’a iya kirgawa ba amma za’a iya kwatatashi da Babban karfe mai iya jawo wadansu karafuna (magnet), Kaunar Allah iko ne da ke jawo mutane zuwa wurinsa.

Yesu ya roki Ubansa ya sa mu zama daya, kamar yadda shi da Ubansa daya suke, shi a cikinmu, Uba kuma a cikinsa. Triniti Mai Tsarki ba kage bane amma gaskiya na ruhaniya wanda ya kawo mu cikin rayuwa ta Allahntaka ta wurin Alheri. Ana kiran mu “jikin Kristi” (Romawa 12:4-5; I Korintiyawa 12:27; afisawa 4:4, 25) da kuma “Haikali” na Ruhu Mai Tsarki (I Korintiyawa 3:16) kuma mun sami dama na shiga da kasancewa cikin Triniti Mai Tsarki, a cikin Kristi (II Korintiyawa 5:17; Yahaya 15:4) Kuma da cikin Allah da kansa (I Yahaya 4:16).

Sabon Alkawali na cike da alamomi na asirin Triniti. Wadanda suna neman sani tawurin bincike, karatu da bayani zasu iya yin tunani a kan wadannan ayoyi: Yahaya 17:1-3; 20, 21-23; Ayukan Manzanni 1:4-5; 2:32-36; I Korintiyawa 2:10; II Korintiyawa 5:19; Galatiyawa 4:4-6; Kolosiyaw 2:9-10; Ibraniyawa 9:14; Wahayin Yahaya 7:10; 21:22023; 22:3-4 d/s. Mu karanta wadannan nassoshi akan dayantakan Uba da Da da Ruhu Mai Tsarki ba ta tunanin mutuntaka ba amma cikin adu’a godiya da sujada. Ruhu Mai Tsarki ne kadai zai iya nuna mana asirin Triniti Mai Tsarki. Sa’annan ba za mu sake daukan kamar Tsohuwar dabara ba amma abinda za’a furta a matsayin uwar duka gaskiya da aka dandana.

6.08 -- Misalai na Yiwuwar Kasan Cewar Triniti Daga Halitta da Rayuwar Dan Adam

Daga Abubuwan Da Suka Kasance

Tunani akan Triniti Mai Tsarki ya fi gaban tunanin mu na mutuntaka. Wannan asiri na Allahntaka za’a iya ganeshi ne a ruhaniya. Musulmai dayawa basa matsayin da zasu iya tunani a ruhaniyance domin babu ainihin Ruhu Mai Tsarki a Islama. Yesu yayi amfani da misalai don sadarwa da wadanda basu riga sun karbi bishara ba. Saboda haka duk wanda yana so ya bayyana wa musulmai da basu yarda da Baibul ba akan dayantakan Triniti Mai Tsarki, zai iya amfani da misalai dayawa daga rayuwa ta yau da kullum. Dalibai na sakandare da na jami’a suna shirye don su ji su.

RANA: kamar kwallo ne mai kuna wanda fadin madauwwarinta ya kai kilomita miliyan daya da rabi wanda tsarkiyoyin ta kadanne suke isowa duniya kuma takan bada haske, zafi da rayuwa. Duka bayyanuwan nan nata na kwallon rana, tsirkiyoyi da zafi ba a iya raba su, daya ne.

LANTARKI: na da inji wanda ke kawo haske, zafi yayin da yake aiki. Duka uku wato injin, wutar da gudun injin duka daya ne!

RUWA: zai iya samuwa kashi uku: da ruwa-ruwa, kankara da tururi. Ko tayaya ya bayyana duka ruwa ne.

DAKi: na da bisa, fadi da tsawo. In babu daya a cikinsu bai zama daki ba.

MUTUM: yana da jiki, kurwa da ruhu. Idan daya daga cikinsu ba lafiya sauransu sukan sha wahala. In babu daya daga cikinsu, sauransu baza su rayu yadda yakamata ba.

IYALI: ya kunshi uba da uwa da ‘ya’ya. Ukunsu a dayance suke rabuwarsu na kawo ciwo.

IDO: na da gababuwa dayawa: zamu iya gani a kwayar ido, fari, da kala-kala da kuma baki. Dukansu ne ido. In babu daya daga cikin wannan ukun mutum zai makance.

KWAI :abin al’ajibi ne. Da bawo, da majina-majina da gwaiduwa daga ukun nan akan sami mai rai.

FARAR TSIRKIYAR HASKE: za a iya rarraba ta har kala uku a cikin tubalin farin gilas. Domin kaloli da yawa ne kan bada fari.

ALWATIKA MAI KUSURWA UKU: Duka kasurwa uku da tsawon gefe uku daidaine. In da wani canji to ba shi bane.

LISSAFI: na goyon bayan dayantakan Triniti Daya a tara da daya a tara da daya zai zama uku, amma daya sau daya sau daya zai zama daya. Dangane da Uba, da Da da Ruhu Mai Tsarki, kowannensu ba za ya kasance shi kadai ba; amma suna raye a dayance in da kowannensu yana cikin dayan. A zahiri sun bayyana a yadda basa rabuwa.

KULLUN YIN BURODI: na da Garin Fulawa, ruwa da sikari ko gishiri. Wadannan basa zama burodi sai an cuda garin sa’annan a gasa shi. Haka a cikin Triniti Mai Tsarki, babu wanda ke raye shi kadai, amma kowanne na raye cikin dayan ne kuma dukansu daya ne.

A Afirka, wani mai bishara ya ziyarci wani kauye wanda ke da dakunan ciyawa. Wata mace tana dafa wa iyalinta abinci a tunkunyar da ba marufi. Sai mai bisharan ya ce mata ta dauke daya daga cikin duwatsu uku na murhun ta. Matan ta ki, ta ce” in na cire dutse daya, tukunyar zata fadi, abincin kuma zai zube”. Mai bisharan ya ce” Ba zaki iya dafa ba tare da Triniti ba. In kika cire daya daga ukun rayuwarki zai rushe kuma zaki kone cikin wuta”. Ya bayyana dayantakan Triniti a hanya mafi sauki cikin yanayin da take ciki. Duk wadannan misalai daga dandanawar rayuwar yau da kullum baza su iya bayyana dayantakan Triniti ba, ba a iya gwada bangaskiya. In zamu iya gwada bangaskiya bata zama bangaskiya ba kuma. Misalai sukan taimaka ne da nuna alama ga wadanda suke bukatar gane gaskiya ta ruhaniya da neman jagora zuwa sanin asirin bangaskiyar.

Abu daya da ya hada misalan da aka kawo mana a baya shine nuna cewa abubuwa masu cingashin kansu sukan dayanta a kalkashin babbar lema wadda ta rufe su. Yarurruka da al’adun da basu gama bunkasuwa ba ba sa iya tunani akan yadda abu biyu zasu iya hadewa ba. Ruhu Mai Tsarki ya koya mana abinda a tunanin mutuntaka bashi da makama kuma kamar an yi Karin gishiri amma gaskiya ne. Mun gaskata Yesu yana zaune tare da Ubansa a sama sa’annan kuma yana zaune a zukatansu. Wannan ba abu mai yiwuwa ne ga musulmi ba. Sai dai ko ya kasance a sama ko ya zauna a zukatanmu amma ba biyun a lokaci guda ba.

Kukan yi shaida cewa mu masu zunubi ne da muka sami barata tawurin bangaskiya. Musulmi zai iya mai da martani ya ce: ko kai mai zunubi ne ko kuwa baratacce ne amma ba zaka iya zama mai zunubin da aka baratadda shi ba.

Ruhu Mai Tsarki na koya wa mabiyan Yesu hanyan tunani ta ruhaniya wanda musulmi ba zai iya fahimta da wuri ba. Tunaninsu na mutuntaka dabanne da na ruhaniya shiya sa dole ne mu zama da hakuri yayin da muke zance da su. Da ma zahirin gaskiya na ruhaniya ya kan dauki tsawon lokaci kafin mu gama amincewa da shi. Yin adu’a don Allah ya ba musulmai fahimta da budi na da muhimmanci kaman yin magana da su.

Sai mu tuna yayin da muke magana da musulmai cewa kalma “Triniti” baya Littafi Mai Tsarki. Saboda haka kada muyi jayayya akan suna Trinity amma muyi kokarin jawo hankalinsu ga gane dayantakan Allah! Ainihin gaskiya akan Allah Uba, Da da Ruhu Mai Tsarki a fili yake a duka litattafai na Baibul domin Yesu ya jaddada madawwamiyar dayantakansa da Ubansa da Ruhu Mai Tsarki.

Wannan ra’ayi akan Triniti kuskure ne a bangaren ilimin harsuna a Turanci da Larabci. Babu wannan kalma Triniti a Baibul! Kristi da manzanninsu sun bayyana murhunniyar Allah, basu taba yin magana akan alloli uku ba. Yakamata mu sake yin tunani akan tushen bangaskiyarmu mu koma ga gaskiyar da aka bayyana mana a Littafi Mai Tsarki.

6.09 -- Alamun Dayantakan Triniti a Kur’ani

Musulmai da yawa basa shirye don su saurari abinda Littafi Mai Tsarki ke fadi domin suna tuhumar gurbatar da shi. Amsoshi daga dabaru da kimiyya, zasu taimaki dalibai a manyan makarantu da jami’oi. Musulmai da yawa zasu yarda da amsoshi daga Kur’ani da Hadisi. Sai mu binciki boyayyun sassan magana game da Trinity Mai Tsarki a Kur’ani domin masu ra’ayin rikau.

A farkon zance da musulmai, za a iya amfani da ayoyin Kur’ani domin kashi 60 bisa dari na maganganu da tunani a Kur’ani daga Tsohon Alkawali ne, wadanda aka gaya wa Muhammadu a yadda aka rubuta su a littattafai na sharhi na Yahudawa wato “Mishna” da Talmud” Kimanin takwas bisa dari na Kur’ani labaru ne da aka gaya wa Muhammadu daga Linjila kokuwa tatsuniyoyi daga darikun Krista. Mu kuwa muna da dama mu karbi shaidar da aka dauko daga wajen Yahudawa da Krista da aka rubuta a ayoyin Kur’ani cikin Larabci tunda tushensu daga Baibul ne. Ko ta yaya dole ne a cika su da ma’anarsu na ruhaniya. A cigaba akwai maganganu dayawa a cikin Kur’ani a harshen Larabci wadanda suke da ma’ana daban-daban kuma ana juya su a hanyoyi dabam dabam saboda haka za a iya cika ma’ana na Littafi Mai Tsarki na ainihi a cikin nassoshin Kur’ani.

Dangane da Triniti Mai Tsarki akwai ayoyi kashi biyar a Kur’ani da suka goyi bayan murhunniyar Allah:

Haihuwar Kristi ta Wurin Maryama

Surrin al-Anbiya 21:91 da al-Tahrim 66:12 sun bada ruya daga Allah:

Mun hura a cikinta daga ruhun mu

A wannan, da an halicci Kristi ne a cikin Maryama Allah na magana cikin jam’i wanda za a iya daukan sa a alama ta kasancewarsa a jam’i. Ya ce: Mun hura a cikinta daga ruhun mu! Tabbas Allah bai hura mala’ika jibra’ilu cikin Maryama ba, a sabanin haka, Allah ya hura daga ruhunsa zuwa cikin Maryama. Daya daga cikin ayoyin biyu ta ce Allah ya hura ruhunsa cikin Maryama dayan kuwa ta ce Allah ya hura ruhunsa cikan farjinta.

Da wannan furci na Kur’ani, an cire tunanin da musulmai suke da shi na cewa Krista suna nufin Allah yayi jima’i ne da Maryama aka haifi Kristi. Wadannan ayoyi sun bayyana haihuwar Kristi tawurin Ruhun Allah. Duka uku: Allah, Ruhunsa da Kristi sun bayyana a Kur’ani a dayantakan da bashi rabuwa.

“Malaman musulunci sun gane raunin wadannan ayoyi kuma sun yi kokarin karkatar da ma’anan tawurin bada sabon fassara:” Amma ba ainihin abinda wadannan ayoyi ke nufi ba ne. An kawo wannan karkatacciyar fassara ne don cire Allahntakan Kristi daga tushen sa.

Allah Ya Goyi Bayan Kristi Da Ruhunsa

A cikin kur’ani zaka iya samun ayoyi uku wadanda ke fadi cewa “Allah ya karfafa Kristi da ruhu na Mai Tsarki”, saboda ya iya kammala manyan mu’ujjizansa. A cewan wadannan ayoyi Kristi ya bude idanun makafi, ya warkar da kutare da kalmarsa, ya kuma tada matattu daga kaburburansu (Sura al-Ma’ida 5:110). Kur’ani ya fada mana kimanin mu’ujjizai goma da Kristi yayi wadanda a cewar Islama bai iya yinsu shi kadai ba amma da taimakon Ruhu da Allah ya aiko masa. Wannan na nufin Allah, Ruhunsa da Kristi na hada hannu cikin dayantaka.

Malamai na Musulunci sun nuna cewa: Kristi bai iya aikata wani mu’ujjiza shi kadai ba, shi yasa Allah ya aiko Jibra’ilu don ya karfafa shi a wannan aiki. Basu iya gane tawali’un Kristi wanda ya ce: Dan bashi iya yin komai don kansa ba, sai abinda ya ga Uban yanayi” (Yahaya 5:19-23). Amma idan ka tambayi Muslumi “Wanene zai iya tada matacce ya rayu”? “Allah ne kadai” amsar da zaka samu. Amma in yi tambaya” ka yarda Kristi Allah ne? zai musanci wannan. Gaskiyar shine Allah, Ruhunsa da Kristi sun dayanta a aikinsu, har a Kur’ani.

Kristi – Ayatolah Na Gaske

Shelar haihuwan Kristi a Kur’ani ya bada sako mai ban sha’awa daga Allah, wanda ya fada game da Kristi cewa“Zamu maida shi alama ga duka mutane da kuma jinkai daga gare mu” (Sura Maryam 19:21).

Kalmar Larabci “ne aka juya an sami alama”, in an karanta shi gaba daya da sunan Allah shine zai bamu Ayatollah, wanda ke nufin “Mu ujjiza na musamman daga Allah”, Kristi shine kadai Ayatollah namiji wanda Allah da kansa ya nada ya zama alama ga duka mutane. A cikinsa ne aka cika ayoyin Farawa 1: 27 da Yahaya 14:9.

Allah ya cigaba da bayyana cewa Kristi jinkai ne daga gare “mu,” yana magana a jam’i. Wannan zance ya jagoranci malaman Kur’ani a Afirka ga yin tunani. Sun gane cewa duka surori sun fara da! “Cikin suna Allah mai Rahama mai jinkai!” saidai sura guda daya da bai fara da shi ba. Wadannan masu neman gaskiya sun yanke shawara cewa mai Rahama (al- Rahman) Allah Uba ne, mai jinkai (al-Rahin) shine Ruhu Mai Tsarki sa’annan jinkansa (al-Rahmat) shine Isa, dan maryama. Duka uku- dayane.

Allah cikin ikonsa ya sa Muhammadu ya rubuta wannan fassara ta wahayi cewa “Bamu aike ka ba a sai matsayin jinkai ga duka duniya” (s al-Anbiya’21:107).

Menene jinkan Allah a rayuwan Muhammadu? Ya kawo sabuwar doka, sharia, wanda shine tushen gwammnati na addini, wannan doka ta Allah bata ceton musulmi, amma zata shar’anta kowane mutum wanda ya tsaya a adaci tawurin nagartansa. Yesu ya nuna alamar jinkan Allah cikin mu’ujjizansa: ya warkar da duk wandanda suka zo gareshi, ya tada matattu ya kuma kawo Ruhun salama cikin duniya. A nan mun gani a fili ko wanene ya kawo jinkai cikin duniya, wanene kuma ke cike da rahama.

Kristi Kalmar Allah da Ruhu Daga Gareshi

Sau da yawa Muhammadu yayi amfami da furcin manzo Yahaya, cewa Yesu kalmar Allahne cikin jiki, (surorin Al’imran 3:39,45,64, al-Nisa’ 4:171, Maryam 19:34). Tawurin wannan lakabi ya yarda da ikon Kristi a matsayin cikakken ikon kalmar Allah. A cewar Kur’ani, a cikin Kristi, halitta, warkaswa, gafartawa, ta’aziya da ikon sabontuwa na kalmar Allah duka sun kasance kuma suna aiki. Kristi bai fadi maganar Allah kadai ba amma shi da kansa kalmar Allah ne. A cewar Kur’ani, Kristi bai yi zunubi ba, domin babu bambanci tsakanin kalmominsa da rayuwansa. A ciknsa nufin Allah da ruhun Allah sun zama a bayyane, kamar yadda wahayin Allah daga Allah ne, haka ma Kristi kalmar Allah, Allah ne.

Sau da yawa Kur’ani ya shaida cewa, hailuwar Kristi ba tawurin nufin namji ba ne amma ruhun Allah ne ya Zama jiki. Musulmi sun bayana mutuwarsa ya koma wurin Allah inda ya fito (surorin Al’imran 3:49,55; al-Nisa 4:158, 171, al-Anbiya 21:91, al-Tarin 66:12). Da wandannan maganganu Islama ta matso kusa da fahimtar Krista a kan Triniti Mai Tsarki. Masu fasara sun yi kokarin su karkatar da wannan ra’ayi sai suka kira Yesu “ halittaccen” kalma da kuma halittccen Ruhun Allah.

Amma wannan bai bayyana a Kur’ani ba, an cusa wannan ra’ayi ne don keta.

Tattaunawa Akan Trinitin Kur’ani

A cikin litttafin musulmai mutum ya iya samun alamun da ke nuna cewa Kristi musamman ne. Allah ya dauke Dan Maryama bayan mutuwarsa zuwa gareshi cikin daukaka (surorin Al’imran 3:55 da al-Nisa’ 4:158). A cewar Islama, Kristi na raye tare da Allah a yau.

A cikin zance (sura al- Ma’ida 5:116-117). Allah ya tambayi Kristi, ko ya koya wa mutane su karbe shi da uwarsa a matsayin alloli? Wata karkatacciyar darikar Krista a kasar Larabawa ta kago irin wannan Triniti wanda duka Krista sun ki amincewa da shi. Kila Muhammadu ya saurari wandannan fandararrun da karkatacciyyar fahimtarsu a kan Triniti. Tun daga nan musulmai suna tsammani Allah yayi jima’i da Maryama kuma ya zama Ubansa. Suna da gaskiya da suka ki amincewa da irin wannan sabo! Mu ma mun tabbatar da gaskiya Muhammadu na kin yarda da wannnan sabo. Babu irin wannan Triniti! Da irin wannan yarda irin wannan kiyayya zai wartsake. Mu bayyana musu cewa mun gaskanta da Triniti na ruhaniya cikin dayantaka wanda ya kunshi Allah, Ruhunsa da Kalmarsa (Yahaya 1:1-14).

Lokacin wannan zance tsakani Allah da Kristi a Kur’ani, in an cire gurbata na masu gaba da Kristi. Za a sami wandansu kalmomi wandanda ke cewa, bayan Kristi ya koma sama, Allah ya yi shaida kuma ya lura da almajiransa marayu kamar yadda shi Kristi shaida ne da kuma makiyayin almajiransa. A Nan Allah da Kristi suna da lakabi da suna guda daya Wanda na nuna Allahntakan Kristi a Kur’ani!

Ba shakka ba zamu iya yi wa Musulmai bishara da Kur’ani ba. A cikin Littafin Musulmai babu zancen ceto! Bamu yarda cewa Allah ne ya saukar da Kur’ani ba. Amma zamu iya samun gutsutsuren shaida na Krista a Littafin Musulmai. Saboda haka a dauke su a tsarkakake su sa’annan a dauke su a sa su inda suka cancanta a cikin bishara. Musulmai masu tsatstsauran ra’ayi basa sauraren wani harshe illa na Kur’ani. Saboda haka muna kai musu bishara cikin salon maganarsu. Har da haka kada mu fadi kalmomin Kur’ani in bamu san ma’anoninsu ba.

6.10 -- Shaidar Dayantakan Trinity Mai Tsarki a Bakunan Krista

Manzannin Kristi sun yi shaidar kasancewar Triniti Mai Tsarki.

Bitrus yace: “Albarka ga Allah Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya maya haihuwarmu bisa ga jinkansa mai girma zuwa bege mai rai tawurin tashin Yesu Kristi daga matattu…” (1 Bitrus 1:3 – 10; 5:10).

Yahaya ya rubuta: “Hakannan mun sani muna zaune cikin sa, shi kuma cikin mu, daya bamu daga cikin Ruhunsa. Mun duba kuma muna bada shaida uban ya aiki dan shi zama mai ceton duniya. Dukan wanda ya shaida Yesu dan Allah ne, Allah yana zaune a cikinsa, shi kuma a cikin Allah”. (1 Yahaya 4:13 – 16; 5:12 – 20).

Bulus ya rubuta: “Shi wanda ya nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya. Gama akwai Allah daya, matsakanci daya kuma tsakanin Allah da mutane, shi kuwa mutum ne, Kristi Yesu, wanda ya bada kansa fansar mutane…” (1 Timoti 2:4 – 6; 1 Korintiyawa 3:17 – 18).

Shaida ta mazanni abin sha’awa ne sun yi shaidar gaskiyar dayantakar Trinity Mai Tsarki a rayuwarmu.

Wani dattijo a wani Ikklesiya a Lebanon ya ziyarci dansa wanda injiniya ne a Qatar, a Tekun Fasha Lokacin da yayi adu’a gaban jama’a kafin cin abinci, wani bako, Musulmi,ya kusance shi ya fada masa cewa yaga cewa shi mai Ibada ne, saboda haka yana bashi shawara ya musulunta ya karbi cikakken jinkai na Allah.

Dattijon ya amsa cikin hikima: “Zan yi tunani akan shawararka. In zaka iya bani fiye da abinda na riga na samu, zan duba da kyau”!

Cikin mamaki, Musulmin yayi tambaya: “Me kake dashi da mu bamu dashi”?

Dattijon ya amsa: “Allah uba na ne, ya sanni ya na kula da ni kuma yana kaunata. Kristi shine dan rago na Allah wanda ya dauke dukan Zunubai na kuma ya sulhunta ni da Allah. Ba za a kashe ni kuma bazan je gidan wuta ba domin ya maishe ni adali a gaban Allah. Ruhun Allah yana zanue a cikina, ya tsarkake zuciya ta mai zunubi. Nakan iya yin Magana da ubana a sama cikin adu’a kuma in gode masa don rai madawwami wanda ya bani. Bazan mutu ba, amma zan rayu har abada kuma in tashi daga matattu kamar yadda Ubangiji naya tashi daga matattu”. (Yahaya 11:25 – 26).

Musulmin nan ya tafi gida cikin zurfin tunani domin wannan dattijo yayi masa bishara cikin kalmomi masu sauki akan gaskiyar dayantakan Triniti Mai Tsraki a rayuwarsa.

A wannan yanayi muna gaida duk wadanda Allah ya kirasu ga yin aiki a tsakanin Musulmai kuma muna adu’a dominsu da Allah ya jagoran ce su zuwa ga yin zance na rahaniya ga Musulmai a wuraren da suke.

ALHERIN UBANGIJIN MU YESU
ALMASIHU DA KAUNAR ALLAH DA ZUMUNTAR
RUHU MAI TSARKI SU KASANCE TARE DA KU

(II KORINTIYAWA 13:13).

6.11 -- Tambayoyi

In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan

Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.

Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.

 1. In an raba Kalmar shahada sau biyu, menene kashi na farkon ke nufi.
 2. A tawace hanya Muhammadu ya ki Trinity Mai Tsarki.
 3. Sau nawa ne zamu iya karantawa a Kur’ani cewa Allah bashi da da? Ina baicin wannan musu a cewar 1 Yahaya 2:18 – 25?
 4. Me yasa Isa Dan Maryama a Islama ba Dan Allah bane?
 5. Ta yaya Kur’ani ya dage cewa Kristi bawan Allah ne kuma talikin sa ne?
 6. Me yasa babu Ruhu Mai Tsarki a Islama? Menene wannan ke nufi a rayuwar Musulmai na ruhaniya?
 7. Me yasa baza iya gane Allah a matsayin Uba ba a Kur’ani?
 8. Menene babu a cikin tunanin Musulmai na ko wanene Allah?
 9. Menene ayoyi uku na farkao a Baibul ke bayyana mana game da dayantakan Triniti? Wane amfani ne wadannan ayoyi zasu iya yi mana cikin hidimar mu a tsakanui Musulmai?
 10. Me yasa Allah wani lokaci a Tsohon Alkawali yakan yi Magana da kansa a matsayin jam’i (mu)? Menene ainihin ma’anar Kalmar Ibrananci “Elohim”.
 11. Ta yaya zai yiwu a fassara Albarkar Haruna (Kidaya 6:24 – 27) da sujadar Mala’iku (Sarafim) a Ishaya 6:3 a Shaidar Murhunniyar Allah?
 12. Menene Zabura 2:1 – 7 ke koya mana a fuskar Triniti?
 13. Me yasa Ishaya 9:6 ya kasance aya ta musamman akan dayantakan Triniti?
 14. Ta yaya Marubucin Ibraniyawa 1:9 ya fassara Zabura 45:6 – 7? Menene wannan zai iya nunawa a zance mu da Musulmai?
 15. Me yasa zabura 110:1 ya kasance kalubale ga Yahudawa da Musulmai?
 16. Ta yaya Bayahude da Musulmi zai iya daukan Alkawuran Tsohon Alkawali?
 17. Menene ma’anar suna “Immanuwel” da aka ba Yesu? A ina ne aka rubuta wannan alkawali a cikin Litattafan annabawa?
 18. Me yasa bayyanuwar Triniti Mai Tsarki na musamman ya biyo bayan baftismar Yesu a kogin Urdun? Menene dan gajeruwar furci na Allah bayan baftismar Yesu zai iya zama ga Musulmi? Wanene zai iya hana Allah madaukaki samun da idan yana son haka?
 19. Ta yaya Yesu ya bayyana lakabinsa na “Kristi” a Majami’an Nazaret? A ina manufar wannan bud’i a fahimtar Dayantakan Triniti Mai Tsarki?
 20. A ina ne a babbar Umurnin Yesu an ambaci dayantakan Triniti Mai Tsarki?
 21. Me yasa Yesu bai ce: “Ni da Ubana biyu ba ne”? Me yasa mukan yi maganar Alloli biyu da Musulmai?
 22. Menene zamu amince dashi daga cikin Yahaya 14:9 – 11 akan zuzzurfan asirin Triniti Mai Tsarki?
 23. Me yasa Ruhu Mai Tsarki yakan daukaka Dan yadda Dan yakan daukaka Uban?
 24. Menene Yesu ya alkawarta a Yahaya 14:23 game da dayantakan Triniti?
 25. Wace irin muhimmiyar ganewa ce akan Murhunniyyar Allah wanda Yesu ya bayyana a Yahaya 17:21 – 23.
 26. Me yasa kalma “Triniti” kuskure ne na ilimin Harsuna a Turance sa’anda ana Magana akan Allah na Littafi Mai Tsarki? Me yasa kalmomin “Murhunniyar Allah” sun fi bayyana gaskiyar Uba, Da da Ruhu Mai Tsarki? Menene zamu jaddad a zancen mu ga Musulmai da Yahudawa game da wannan zance?
 27. Me ya sa rana, tsirkiyoyin rana da zafin rana suna nuna Murhunniyar Allah?
 28. Tayaya Inji (Janareto), karfin wutar lantarki da aikin wutar( hita, fanka, konfuta) na kamanta dayantakan Triniti?
 29. Menena Zamu koya daga ruwa, daki da kuma kasancewan mutum akan dayantakan Triniti?
 30. Ta yaya Ido, kwai ko alwatika mai kusurwa uku ke nuna dayantakan Triniti?
 31. Menene bambancin 1 + 1+ 1 da 1 x 1 x 1? Ta yaya kullun burodi daga fulawa, ruwa da yisti kan zama burodi?
 32. Me yasa wadannan batutuwa daga dandanawar rayuwar yau da kullum baza su iya bada cikakken bayyani akan Triniti Mai Tsarki ba? Me ya sa Krista sun iya tunani akan dayantuwan abu biyu kuma me musulmi ke bukata ya gane wannan gaskiya ta ruhaniya wanda a fahimtar mutuntaka akwai sabani?
 33. Yaya Muhammadu yayi tunani akan haihuwar Yesu daga cikin Maryama? Ta yaya irin wannan tunani zai taimaka mana a zancen mu da musulmai?
 34. Me yasa karfafawan Kristi tawurin ruhu daga Allah na nuna “dayantaka cikin aiki” na Allah, Ruhunsa da Kristi?
 35. Ta yaya Kur’ani ya bayyana cewa Kristi shine kadai Ayatollah namiji da Allah ya nada? Ta yaya ne wannan ayar Kur’ani ya taimaki wadansu malaman Kur’ani a Afirka matsowa kusa da gaskiyar Triniti Mai Tsarki?
 36. Ta yaya wannan furci daga Kur’ani wanda yake cewa Kristi “Kalma ne daga wurin Allah” kokuwa “Kalmarsa” wanda ya zama jiki zai taimaka mana a zancen mu da musulmai?
 37. Ta yaya bayanin Kur’ani akan cewa shi “ruhu daga wurin allah” ne zai iya taimakonmu mu bayyana wa musulmai dawwama da Allahntakar Dan Maryama?
 38. Menene zance Allah da Kristi a Kur’ani bayan tafiyarsa sama ke nufi? Me yasa zamu yarda da Musulmai cewa Triniti ta Kur’ani wanda Muhammadu ya ki, muma dolene mu ki shi? Ta yaya wannan yarda zai kawo yanayi mai kyau da zamu nuna wa musulmai Triniti na Ruhaniya?
 39. Me da me ake bukata don bayyana wa musulmi dayantaka ta Ruhaniya a Triniti Mai tsarki?
 40. Wace Shaida ce ta Manzannin Kristi a fahimtarka na bayyana dayantakan Triniti Mai Tsarki da kyau?
 41. Za ka iya nuna mana inda za a iya samun Kalma Triniti a Baibul?

Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.

Naku cikin Hidimarsa

Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.

Ku aika da amsoshin ku zuwa:

The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.

Ko

GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY

Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on June 03, 2013, at 08:44 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)