Previous Chapter -- Next Chapter
1. Kalmar Allah a Bakin Annabi
Kiristoci ba su yarda cewa Kur'ani Maganar Allah ba ce, amma don hujja kawai, za mu ci gaba kamar da gaske Allah ya sa kalmominsa a bakin Muhammadu don gano ko wannan zai iya tabbatar da cewa Muhammadu Annabi ne da ake magana akai cikin Kubawar Shari’a 18:18. A ganinmu furucin nan “Zan sa maganata cikin bakinsa” ba ta taimaka wajen gane annabin da ake magana akai ba. Gaskiya ne ga kowane annabi cewa Allah ya sanya maganarsa a bakinsa. Domin Allah ya ce wa Irmiya:
Bugu da kari kuma mun karanta a Kubawar Shari’a 18:18 cewa annabin da zai bi Musa “zai fada musu dukan abin da na umarce shi”. Yanzu mun karanta cewa Yesu ya taba gaya wa almajiransa:
Irin wannan nassin da ya kwatanta wannan yana cikin babbar addu’a da Yesu ya yi a daren ƙarshe da ya kasance tare da almajiransa. Yace:
Saboda haka, ba yadda za a yi a tabbatar da ainihin annabin da ke cikin Kubawar Shari’a 18:18 daga gaskiyar cewa Allah zai sa kalmominsa a bakinsa. Ga kowane annabin da yake gaskiya haka lamarin yake kuma annabin nan mai girma da ake magana a kai a cikin nassi, wanda zai zama na musamman kamar Musa ta hanyar da babu wani daga cikin sauran annabawa, dole ne a gano shi daga wasu tushe.