Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":
Home -- Hausa -- 14-Christ and Muhammad -- 010 (The Young Creator)
This page in: -- Cebuano -- English -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Yoruba

Previous Chapter -- Next Chapter

14. ALMASIHU DA MUHAMMADU
Gano a cikin Alkur'ani game da Almasihi da Muhammadu
6. Alamomin Muhammadu da na Kristi

c) Matashin Mahalicci


Mun karanta a cikin Alqurani - ba a cikin Injila ba - cewa Yesu, tun yana yaro, ya siffanta kwatankwacin tsuntsu daga laka, ya hura a ciki; sai ya zama tsuntsu mai rai, mai tashi sama:

"Lalle ne ni, na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, a cikin ta, zan halitta muku daga laka, misalin tsuntsu; to zan hura a ciki, sai ya zama tsuntsu da izinin Allah. Zan kuma warkar da makaho da kuturu, kuma in rayar da matattu da izinin Allah.” (Suratu Al Imrana 3:49)

أَنِّي قَد جِئْتُكُم بِآيَة مِن رَبِّكُم أَنِّي أَخْلُق لَكُم مِن الطِّين كَهَيْئَة الطَّيْر فَأَنْفُخ فِيه فَيَكُون طَيْرا بِإِذْن اللَّه وَأُبْرِئ الأَكْمَه وَالأَبْرَص وَأُحْيِي الْمَوْتَى بِإِذْن اللَّه (سُورَة آل عِمْرَان ٣ : ٤٩)

A cikin wannan ayar, mun sami keɓaɓɓiyar jumla, “Zan ƙirƙira muku”, wanda ke nuna cewa Kristi shine Mahalicci mai iko. Mutum ba zai iya ƙirƙirar wani abu daga wofi ba, ko ya hura rai cikin abin da ba shi da rai.

Kur'ani ya ba da shaidar ikon Kristi na rayarwa ta wurin saurin numfashinsa. Ya hura a tsuntsu na yumɓu kuma ya zama tsuntsu mai rai, daidai yadda Allah ya busa cikin Adamu a baya. Wannan yana nufin cewa Kristi yana da Ruhu mai ba da rai a cikin kansa; Yana da ikon numfasa rai cikin laka mara rai.

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on November 07, 2023, at 02:50 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)