Previous Chapter -- Next Chapter
1) Isa (عيسى)
Wannan suna ya zo sau 25 a cikin Alkur'ani. Wasu malaman suna da’awar cewa ya fito ne daga lafazin kalmar Aramaic na Yesu, wanda asalinsa yana nufin: “Ubangiji yana ceto” (Matiyu 1:21); Yakan cece shi daga masifu, da cututtuka, da wahala, da fushi mai zuwa, da zunubai, har ma da mutuwa.
A rayuwarsa, Isa ya cika ma’anar sunansa na asali. Ya buɗe idanun makafi ba tare da tiyata ba, ya warkar da kutare ta wurin kalmarsa mai aiki, ya rayar da matattu ta wurin kiransa, ya kuma fitar da aljanu daga masu mallake. Wanda ya gane sunansa na asali, Yesu, zai iya samun iko na har abada daga gare shi.
Maganar Kur'ani ga Isa: Surar al-Baqara 2:87, 136, 253; -- Al 'Imran 3:45, 52, 55, 59, 84; -- al-Nisa' 4:157, 163, 171; -- al-Ma'ida 5:46, 78, 110-116; -- al-An'am 6:85; -- Maryam 19:34; -- al-Ahzab 33:7; -- al-Shura 42:14; -- al-Zukhruf 43:63; -- al-Hadid 57:27; -- al-Saff 61:6, 14.