Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 3 Bible not Corrupted
Previous booklet -- Next booklet
01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI
3 - Yadda za a Bayyana Cewa ba a Gubatar da Baibul ba
3.01 -- Yadda za a Bayyana Cewa ba a Gubatar da Baibul ba
3.02 -- Gabatarwa
Musulmai da yawa na da shakka akan Baibul kuma sunce an canza shi kuma akwai kuskurori a ciki. Wadansu sun yarda cewa Krista sun iya hada kansu da yin aiki tukuru, kuma suna da dokoki masu adalci. Amma suna daukan Krista wadanda ke tsoron Allah kamar wadanda basu san abinda suke yi ba domin sun yarda da Attaura, Zabura da Linjila a amintattun Litattafai. Sukance, wadannan Litattafai masu aminci ne a da amma yanzu an lalatar dasu. A garesu, duka Krista na cikin babbar yaudara, suna gaskanta tatsuniyoyi.
Daga ina ne musulmai suka fara yin shakka a kan Litattafai 66 na Baibul? Wace muhaware ce sukan kawo don tuhumar Littafi Mai Tsarki akan gurbata?
3.03 -- Sukar Da Kur’ani Ya Yiwa Attaura
Amsar wadannan tambayoyi za’a iya samu a ayoyi goma na Kur’ani. Sune tushen shakkan Musulmai akan Baibul. An yi wa wani Dattijo ba Yahude a Madina suka na cewa yayi zina. Yudawa basu so su bayyana wa Musulmai ayoyin Attaura akan horon daya kamata a yi wa mazinaci ba don suna so su ceci dattijon daga kisa ta jifa da duwatsu. Akan wannan, Muhammadu a cikin nassoshi da yawa a Kur’ani ya sa Allah ya kalubalanci Yahudawan da basu bayyana asirin dokokin da suke a Attaura ga Musulmai ba. “Kuma kada ku sayi yan kudi kadan ayoyi na” (Sura al-Baqara 2:41).
“Kuma kada ku lullube gaskiya da karya, kuma ku boye gaskiya, alhali kuwa kuna sane.” (Sura al-Baqara 2:42).
“Wata kungiya daga garesu sun kasance suna jin Maganar allah, Sa’annan kuma su karkatar da ita daga bayan sun gane ta, alhali su suna sane?” (Sura al-Baqara 2:75).
“Kaiton wadanda suke rubuta littafi da hannunsu sa’annan kuma suce wannan daga wurin Allah yake, domin su sayi kudi kadan dashi” (Sura al-Baqara 2:79).
“Hakika, Suna boyewa gaskiya alhali kuwa su suna sane” (Sura al-Baqara 2:146).
“Yaku mutanen Littafi! Don me kuke lullube gaskiya da karya, kuma kuke boye gaskiya, alhali kuwa kuna sane?” (Sura al-Imran 3:71).
“Kuma lalle ne, daga garesu akwai wata kungiya suna karkatar da harsunansu da Littafi, domin ku yi zatonsa daga Littafin, alhali kuwa ba daga Littafin” (Sura al-Imran 3:78).
“Daga wadanda suka tuba (Yahudu), akwai wasu suna karkatar da Magana daga wurarenta.” (Sura al-Nisa 4:46).
“To, saboda warwarewarsu ga alkawarai su muka la’anesu, kuma muka sanya zukatansu kekasassu, suna karkatar da magana daga wurarenta, kuma suka manta da wani yanki daga abinda aka tunatar da su da shi.” (Sura al-Ma’ida 5:13)
“Kuma daga wadanda suka ce: ‘Lalle ne mu Nasara ne’, Mun riki alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abinda aka tunatar dasu dashi.” (Sura al-Ma’ida 5:14).
Idan mun duba wadannan ayoyi goma na Kur’ani filla-filla a cikin harshen Larabci za mu iya samun zahirin gaskiya na tarihi guda takwas.
- Ba “duka” Yahudawa ne ba suka yi kokarin yaudaran Muhammadu amma kalila ne (Sura al-Baqara 2:75, 146; al-Imran 3:78).
- Su mutane ne da aka yi wa jagora daidai (Sura al-Nisa’ 4:46), amma suka boye wani bangaren shari’arsu da maganganun wofi saboda su boye gaskiya (Suira al-Baqara 2:42; al-Imran 3:71).
- Basu fassara duka Littafi Mai Tsarki ga Muhammadu ba kuma basu fada masa kome a cikin Littafin su ba, sai in ya fara sayen kaya daga wurinsu (Sura al-Baqara 2:41 - 79).
- Sun boye masa wadansu dokokin ne musamman wadanda zasu yi musu barna a lokacin da suka sami sabani tsakaninsu da Muhammadu da mabiyan sa (Sura al-Baqara 2:42 - 146; al-Imran 3:71).
- Sun canza wasula ko lafazi na wadannan kalmomi, ta haka sun canza ma’anar kalmomin (Sura al-Baqara 2:75; al-Nisa’ 4:46; al-Ma’ida 5:13).
- Sukan karkatar da harsunansu lokacin da suka karanta wadansu nassoshi daga Attaura yadda babu wanda zai fahimci ainihin abinda suke fadi (Sura al-Imran 3:78).
- Su suka rubuta Litattafansu masu Tsarki amma sun yi karyan cewa sauko su akayi daga wurin Allah (Sura al-Baqara 2:79).
- Sun mance wadansu ayoyi daga Litattafansu, wanda wahayi ne da yakamata su hadace (Sura al-Ma’ida 5:13). Muhammadu ya kuma tuhumi Krista na yin wannan rashin aminci ga Allah da wahayinsa (Sura al-Ma’ida 5:13).
Daga wannan Tuhuma na Kur’ani za a iya gani cewa Yahudawa ‘yan kalila ne a Madina suka sami Matsala da Muhammadu. Kur’ani bai yi tuhumar sauran dokacin Yahudawa ba. Basu gurbata ko sun boye Littafinsu Mai Tsarki ba. Yahudawa a ko’ina suna rike da Attaura na ainihi a yau.
A Kur’ani ba a ce an canza duka Littafin Attaura daga farko zuwa karshe ba. Muhammadu ya ce wadansu kalmomine aka boye, karkata lafazinsu ko an canza wasulansu. Kur’ani bai soki martabar Attaura ba.
Yahudawa da Krista kuwa basu iya haddace nassoshi masu yawa a Baibul ba, amma sukan fadi ra’ayinsu, dandanawansu ko fassara na nassoshin Littafi Mai Tsarki. Ga Musulmi, haddace wahayin Allah shine nuna kaunar mai bada gaskiya gareshi da wahayinsa. Sun ga babu wannan irin kauna a tsakanin Yahudawa da Krista. Muhammadu ya so ya ji an haddace masa ainihin wahayin ne bai so ya ji ra’ayin wani game da wahayin ba.
Wannan ‘yar gajeruwar yayyana ayoyin Kur’ani da aka rubuta a baya ta nuna cewa tuhumar gurbata da musulmai ke yi wa Attaura bashi da makamashi. Bugu da kari, babu inda Kur’ani ya fada cewa an gurbatarda ko an canza Linjila, domin Muhammadu ya darajata Krista kuma ya san su masu aminci ne da kaunar gaskiya.
3.04 -- Binciken Sunan Muhammadu da Musulmai keyi a Cikin Baibul
Bayan Yahudawa da Krista Larabawa da yawa suka Musulunta, sai suka fara kawo tunanin cewa, shi Muhammadu wanda ya kira kansa annabi na karshe, kamata a ce anyi annabcinsa a kalmomin Littafi Mai Tsarki. Muhammadu ya sa Isa ya ce, akwai wakili wanda zai zo bayansa wanda za a kirashi Ahmad (Sura al-Saff 6`:6).
Tun daga nan, Musulmai sun tuhumci Yahudawa da Krista da laifin goge sunan Muhammadu ko sunan da ke da ma’ana daya, wato Ahmad daga Litattafansu masu tsarki.
A wannan lokacin ne aka shiga binciken anabcen-anabcen zuwan Muhammadu. Akwai zace-zace da rubuce-rubuce da yawa da suke Magana akan gaskantawa da Musulmai suka yi na cewa an ambaci Muhammadu a Baibul. Yawanci lokaci sukan fadi Maimaitawar Shari’a 18:15 – 18. A nan Musa yace: “Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama’arku, sai ku saurare shi”. Musulmai sun yi dokin cewa: “Wannan annabin da aka yi alkawarinsa lallai Muhammadu ne”. Amma basu yi la’akari da cewa wannan annabin zai fito daga zuriyar bani Israila ba ne. Duk wanda ya tambaye su ko suna so su furta cewa Muhammadu bani Israila ne ko ba Yahude ne nan da nan zasu ce a’a cikin fushi.
Daga Linjila sun yi ta maimaita wannan Sanannen alkawarin da Yesu yayi: “Mai Taimako, wato Ruhu Mai tsarki, wanda Uban zaya aiko a cikin sunana, zaya koya muku abu duka”. (Yahaya 14:16 – 17 & 26). Musulmai masu bincike suna tunanin Muhammadu shine wannan Mai Taimakon! Sukan duba kalma “parakletos” (Mai Taimako) a harshen Helenanci sai su sauya Parakeltos da Perikletos, wanda yake nufi “Wanda aka yaba” (Mahammadu). Yayinda suka tuhumi Krista akan sun canza sunan Muhammadu zuwa Parakletos, zamu iya nuna musu cewa sune suka canza wasulan! Bayan wannan, idan ka tambayi wadannan ‘ya neman cikan alkawari ko sun yarda cewa Kristi ne ya aiki Muhammadu a matsayin bawansa, zasu yi masun haka (Yahaya 17:7 an rubuta cewa Yesu ne ya aiki Mai Taimako. Wannan tambaya kadai zai kakkarya wannan jayayya.
3.05 -- Yanke Shawarar Gaba Da Baibul
Yayin da malamai na Islama da masu sharhi a kan Kur’ani suka gwada Baibul da Kur’ani shekaru dama bayan mutuwar Muhammadu, sai suka ga cewa babu ko jumla daya a cikin Baibul da ta tayi daya da ta Kur’ani a kome. Wannan rashin cikar burinsu ya kai su ga yanke shawara irin ta zamanin jahiliyya, da yanke hukumci ta wayo. Suka yi kuduri cewa duk bambance- bambance a Baibul da Kur’ani suna nuna cewa an gurbatarda Baibul. Ta wannan hanya aka maida Kur’ani ya zama magwaji da mai Shar’anta Baibul. Daga asali, musulmai sun gaskanta cewa duka Littafi biyu na da tushe daga Littafi na ainihi a sama kuma an sauko da sune tawurin Magana ta baki a wahayi. Bambance- bambance da baza a iya gyarawa ba tsakanin wadannan Litattafai uku a ra’ayinsu na nuna cewa Attaura da Linjila jebu ne. Ya kamata mu gane wannan cewa a bias ga wannan yanke shawara Islama ta nuna kanta cewa ita ruhun da ke gaba da Baibul ce kuma ta daddaure yawancin Musulmai a madauri daya.
3.06 -- Harbin Malam Deedat Mai Dafi
Harin Islama karo na hudu gaba da Baibul ya zone daga Malam Deedat da kungiyarsa. Shi Deedat mutumin Indiya ne, musulmi, zaunannen Afirka ta kudu. Ya tattara Muhawara da yawa wadanda ba na Kur’ani ba daga Turawan da basu yarda da Allah ba, masu addinin kwammisanci, marasa addini da masu Ilimin Tauhidan son ‘yanci wadanda sun yi kokarin su nuna cewa akwai kurakurai a Baibul. Kiyayyansa akan Baibul ya saba wa fadin Kur’ani. Ko dashike ya gina Muhawararsa akan harsashe mara karfi, gwamnatocin kasashen musulmai masu arzikin mai sun cigaba da goyon bayansa domin ya iya girgiza dogaro da dimbin Krista da musulmai suke dashi akan Baibul a duka duniya.
A cikin tuhumar da Malam Deedat yayi shine na cewa Kristi bai fadi gaskiya ba lokacin da yayi annabcin: “Kamar yadda Yanusa yayi yini uku da dare uku a cikin cikin kifi, haka ma Dan Mutum zai yi yini uku da dare uku cikin kabari”. (Matiyu 12:40; Markus 8:11 – 12; Laka 11:29 – 32) cikin keta Malam Deedat ya nuna zahirin cewa Kristi ya kasance a cikin kabari daga ranar juma’a kafin faduwar rana, Zuwa ranar Lahadi da asuba. Yana yayata cewa Yesu yayi yini daya da rabi ne da dare biyu a cikin kabari, amma ba yini uku da dare uku ba! Daga wannan zahiri ne ya yanke Magana cewa ba annabin gaskiya bane!
Krista da yawa basu san yadda zasu maida martani akan wannan irin muhawara na Malam Deedat ba sai su tafi gida da kunya. Amma a wannan hali zamu iya amsa cewa, bisa ga al’adar Yahudawa, duk abinda ya faru a cikin rana ya shafi dukan wannan ranar. Tunda an bizne Yesu a ranar Juma’a, duka Juma’a ta zama ranar mutuwarsa. Hakanan kuma ainihin ranar tashinsa ya faru a rana tafari a mako.
Ta irin wannan dabara Malam Deedat yayi kokarin tuhunar giciye da tashin Yesu daga Matattu da bisharansa. Ya tattara rubuce-rubuce na kawo suka akan Littafi Mai Tsarki wanda Masu Tauhidin son ‘yanci suka rubuta yana cewa harma Krista masana basu yarda da cewa Baibul bashi da kuskure ba. Wannan harbi mai dafi daga magabcin Almasihu ana wallafawa kuma ana rabawa miliyoyin mutane a nahiyoyin Afirka da Asiya da sauran nahiyoyi. Almajiransa sun yi aiki tukuru cikin karni biyu cikin harsuna da yawa kuma akwai Tasiri a aikin nasa.
3.07 -- Girgizawa Na Dogaro A Cikin Gaskiyar Baibul
Kada muyi mamaki cewa ba Krista kadai ba, amma har ma musulmai an girgiza dogaron su a cikin Baibul. Duk wanda ke kokarin bayyana ceton Kristi ga ma biya Muhammadu dole ne ya fara neman hanyar kafawa a cikin musulmin, dogaro ga Littafi Mai Tsarki kokuwa duka kokari zai zama a banza. Wannan waka daga Nikolaus Ludwig, Earl daga Zinzendorf (1700 - 1760) yana da gaskiya a cikin aikin mishan zuwa ga musulmai:
Ubangiji, ka tsare kalmarka
Kyauta Mai daraja, zinariya gareni;
Ni fi son shi fiye da kowace Mallaka
Fiye da arziki mai yawa.
Menene zai zama harsashen bangaskiya?
Bana so in yi wa duniyoyi dubu aiki amma in so in yi aiki a
wannan duniya
(Waka ta Furotesta a Jamus lamba 436).
I dan kana kokarin bayyana wa musulmi gaskiyar Littafi mai Tsarki, Zaka sami tushen Mahawara guda biyar da zasu taimake ka a aikin ka.
- Shaida ta Tsohon Alkawali ga gaskiyar maganar da Allah ya saukar.
- Shaida ta Yesu Kristi game da gaskiyar Tsohon da Sabon Alkawali.
- Rubuce-rubuce wadanda ba na addini ba wadanda suka tabbatar da gaskiyar Baibul.
- Ayoyi a Kur’ani wadanda ke Magana akan rashin gurbatar Attaura da Linjila.
- Dandanawar mu na samun iko daga cikin maganar Allah.
3.07.1 -- Shaidar Tsohon Alkawari Game da Amincin Attaura da Annabawa
Duk wanda yake so ya bayyana wa Musulmi cewa Allah na Lura da maganar sa sai ya tuna da wadannan ayoyi ya kuma karanta su tare da abokinsa Musulmi:
● Irmiya 1:11 – 12: “Kuma maganar Ubangiji ta zo wurina, cewa, Irmiya, me kagani? Na ce Ina ganin sandar itacen almond. Sai Ubangiji yace mani, Daidai ne kagani: gama ina kiyaye magananta domin in cika ta”.
An yi wa annabin alkawari, an bashi tabbacin amfani da amincin maganar Allah, domin Ubangiji da kansa yana kiyaye maganarsa. Shi madawwami baya barci ko gyangyadi, amma yana hura da mutanensa kuma yana hana mutane su murda maganarsa. Manufar maganar Allah ba Kalmar ne kawai ba , amma harda aikin da yake yi cikin mutane. Ubangiji yana kiyaye maganarsa don ya tabbatar an kiyaye-Babu wanda ya isa ya hana Buwayi-Ubangiji aikata abinda ya fadi.
● A Maimaitawar Shari’a 4;2, Mun karanta kalma daga Wurin Musa: “Bazaku dada akan Magana wanda na dokace ku da ita ba, ba kuwa zaku rage kome daga cikinta ba, domin ku kiyaye dokokin Ubangiji Allahn ku wanda na Umurce ku”.
Wanene ya isa ko da saninsa ko da kuskure ya canza dokokin Allah da alkawuran sa, sa’annan ya kara nasa ko ya ciccire abubuwanda ya haramta? Ubangiji da kansa yayi umurni tawurin Musa cewa zai kiyaye maganarsa daidai, a haddace ta sa’annan a yi biyaya kullum. Littafi Mai Tsarki na kare gaskiyarsa da kansa. A Islama, maganar annabi kalmomin Allah ne. Babu bambanci tsakanin su, wakilin Allah yana da babban iko. Musulmai sun fahimci Attaura a Matsayin dukan Tsohon Alkawali ne.
● A Karin Magana 30:5–6 mun karanta: “kowace maganar Allah tsarkakakkiya ce; Garkuwa ne shi ga wadanda ke dogara gareshi. Kada ka kara ma zantattakansa, Domin kada ya tsauta maka, a tarar da kai makaryaci”.
Yadda akan tsarkake zinariya da wuta hakane an tsarkake maganar Allah tawurin ikon tsarkinsa. Don wannan babu aibi, tsarkakakke ne kuma dauwamamme. Allah ya bamu “cikakken kayan yakinsa” (Afisawa 6:10 - 20) tawurin maganarsa. Wanda bai kahu a cikin Maganar Allah ba bashi da iko na ruhaniya. Duk wanda ya kawo iliminsa irin ta duniya, kimiyya da abubuwan daya tsin-tsinto daga wadansu addinai da al’adu a matsayin wahayi, Allah zai tona asirinsa a makaryaci kuma za a horeshi. “Wautar maganar Allah” ya fi hikimar duniya harfi (1 Korintyawa 1:18 – 29).
● Zabura 33:4 “Gama maganar Ubangiji mai gaskiya ce; Dukan aikinsa cikin aminci yake kuma”.
Nassoshin Littafi Mai Tsarki na kunshe da ainihin gaskiya, ko da Musulmai da Krista masu son ‘yanci sun musanci wannan gaskiyar. Alamar gaskiyar maganar Allah za a same shi ne a cikin aikin da Allah yake yi. Maganarsa ba gaskiya ne kadai ba amma zai aikata abinda ya fadi. Alkawura 333 a cikin Tsohon Alkawali wadanda aka cika a Sabon Alkawali, na tabbatar da gaskiyar Tsohon Alkawali a hanya ta Musamman. A duka duniya babu Littafin da ke kunshe da abinda ke kare gaskiyarta a cikinta kamar Baibul. Ubangiji yana aikata abinda ya fadi! Kur’ani na koyar da cewa kome kaddarar Allah ne. Cikar alkawuran Allah na Tsohon Alkawali a cikin Sabon Alkawali abinda ya kamata ya bude idon musulmai ne akan fahimtarsu ta kaddara.
● Zabura 119:89 “Har abada, ya Ubangiji, Maganarka ta kafu a sama”. (Ishaya 40:8; 1 Bitrus 1:25).
Rashin iyakan wannan kalma “dawwamamme” na bayyana mana girman wannan alkawali. Rayuwar mu na gajeren lokaci ne. Amma maganar Allah bashi kawuwa har abada kuma baya girgizuwa, ya ma fi babban dutsen da ke cikin mafadar ruwan Rhine kusa da Shafhawsin a kasar Switzerland, wanda ruwan ke bugunsa yau da kullum. Tawurin maganar Ubangiji muna dandana madawwamiyar rayuwa. Wannan alkawali na maganar Ubangiji ya shafi duniyarmu da sauran duniyoyi. Dokokin sa, Alkawaran sa, shaidarsa da dandanawar masu imani na tabbatar mana da amincinsa. Wadansu Yahudawa da Musulmai suna tsammani cewa, Littafin Allah na ainihi da duka wahayinsa yana a sama. Babu wanda zai iya karkace ko ya canza maganar Allah na ainihi.
● Zabura 19:7 – 9, na kunshe da Shaidar Dauda, yadda ya dandana gaskiyar maganar Allah wanda ba a canzawa a rayuwarsa:
Shar’ia Ubangiji cikakkiya ce
Tana mayas da rai:
Shaidar Ubangiji tabbatacciya ce tana
Sa mara sani ya zama mai hikima.
Dokokin Ubangiji madaidaita ne,
Masu-faranta zuciya:
Umurnin Ubangiji tsatstsarka ne
Yana haskaka idanu.
Duk wanda yayi tunani akan wadannan batutuwa guda hudu: cikakkiya, tabbatacciya, daidaitacciya da kuma mai haskakawa, zai sami iya yarda da amincin Littafi Mai Tsarki kuma zai iya koyawa Musulmai.
● Ishaya 55:10 – 11 na karfafa duka ma’aikatan Ubangiji wadanda suke kai wa Yahudawa, ‘yan addinin Hindu, Budha, Musulmai, masu neman ‘yanci da masu tsatstsaurar ra’ayi bishara: Gama kamar yadda ruwa yakan sauko, da snow kuma daga sama, ba yakan koma can kuma, amma yakan yi ma duniya ban ruwa, yakan sa ta bada ‘ya’ya, ta yi tofo, yana bada iri ga mai shuka, abinci ku ma ga mai ci; hakanan kuma maganata, wadda take fitowa daga cikin bakina za ta zama: bazata koma wurina wofi ba, amma zata cika abinda na nufa, zata yi albarka kuma a cikin sakona”.
Wahayin Ubangiji a Baibul ba kawai amintattu ne kawai da gaskiya ba, amma masu girma ne da iko zasu aikata abinda Allah ya kadurta. Musulmai basu yi tunanin Maganar Allah na da irin wannan iko ba. Daga cikin maganar Allah ana samun warkaswa, gafartawa, ta’aziya da sabonta karfi Yahudawa da yawa sun dandana wannan gaskiya kuma suna girmama Littafin Attaura da dukan bangirma, An kashe yawancinsu don bangaskiyarsu akan aminci da iko na Litattafan Tsohon Alkawali.
3.07.2 -- Ayoyin da Suke Tabbatar da Amincin Wahayin Sabon Alkawali
● Matiyu 5:17–18 ya bamu shaida ta Yesu wanda ya zama tabbaci da jagora wanda kuma ya nuna matsayinsa akan wahayin Tsohon Alkawali: “Kada ku zaci na zo domin in warware attaura da annabawa: ban zo domin in warware ba, amma domin in ciccika. Gaskiya fa nike fada maku, Har sama da duniya su shude, ko wasali daya ko digo daya, ba za ya shude daga Attaura ba, sai duka abu ya cika”.
Ta wurin wannan kakkarfan Magana Dan Allah ya tabbatar da amincin Tsohon Alkawali. Yesu ya musanci furci na cewa ya zo ne don yakau da tsofaffin wahayi na da ya kawo sabobin da suka fi kyau kamar Kur’ani wanda cikinsa akwai ayoyi 240 wadanda an riga an kawar, basu da amfani kuma.
Yesu kuwa yayi Magana akan cikan Attaura da Annabawa tawurin koyaswarsa, rayuwarsa, mu’ujjizansa, mutuwarsa, tashinsa daga matattu, zubowan Ruhu Mai Tsarki da dawowansa. Ubangiji Yesu da kansa ya darajanta, ya zurfafa kuma ya nuna Tsohon Alkawali a rayuwarsa wadda shine Baibul da yayi amfani dashi.
Yesu ya tabbatar da amincin duka Litattafan Tsohon Alkawali har zuwa karshen duniya yadda ko musulmi zai iya samun tabbaci cewa ko digo daya bai bata ba, amma an cika shi daidai. Wannan furci mai iko daga wurin Yesu Kristi ya soke duk tuhumar Muhammadu da mabiyansa.
● Matiyu 24:35 ya bamu wani Kalmar Yesu Kristi wanda ya tabbatar da dawwamar Bisharansa da duka Litattafan Sabon Alkawali: “Sama da kasa zasu shude, amma zantattukana ba zasu shude ba”. Yesu ba mai neman sa’a bane ko mai karyayyen zuciya amma mai sanin dahir ne. Ya tabbatar mana cewa duk shirye-shiryen mutane na neman inganta duniya da tsareta zasu zama aikin banza, domin sama da kasa zasu shude. Amma tun da Ubangijinmu na da rai, maganarsa na cike da ruhu da iko, Bisharansa ba za ta shude ba har ma in duka abubuwan duniya kuma sun lalace. Ya karfafa mu da mu gaskanta kuma mu sazuciya yayin daya ce: “kuyi murna saboda an rubuta sunayenku cikin sama! (Luka 10:20). Duk wadanda suka sami haihuwa na biyu tawurin maganarsa kuma sun karbi Ruhu Mai Tsarki zasu gaji rai madawwami.
● Luka 1:1– 4 ya nuna mana yadda marubuta Litattafan Bishara sun yi matukan kula a rubuta kalmomi da rayuwan Yesu Kristi. Luka, Likita ba Hellene ya gaya mana yadda ya rubuta nasa Littafin Bishara: “Dashike mutane da yawa sun dauka su rubuta labarin wadannan al’amura da ke tabbatattu a wurin mu, kamar yadda suka bada su garemu, mu da muke shaidu na ido tun daga farko, masu hidiman maganar kuma, ni kuma naga yayi kyau, dashike tun da fari na bibbiya abu duka daidai, in rubuta maka; bisa jeranta, ya TIYOFILUS mafificcin nagarta, domin ka sansance inganci zantattukan da aka sanasheka”.
Ba’a jeho Litattafan Linjila daga sama ba a Litattafan da aka kamala rubutawa ba kamar yadda wadansu musulmai suke tunani an saukar da Kur’ani. Luka, Likita wanda ba Hellene ne wanda yana cikin Kristi ya tattambayi wadansu mutane-ganau wadanda mazannin Yesu suka nadasu don su tattaro, kuma su rubuta kalmomin Yesu. An kira su masu hidiman kalma.
Luka, Likita, ya so ya sani yadda budurwa Maryamu ta iya samun da ba tare da sanin namiji ba saboda haka ya nemi sani daga gareta. Wata kila Maryamu ce ta gaya masa yadda mala’ika Jibra’ilu ya bayyana ga Zakariya kuma yayi shelar haihuwar Yahaya mai baftisma 9Luka 1:5 – 24). Ta gaya masa game da bayyanuwar wannan babban Mala’ika gareta a Nazarat (Luka 1:25 – 56) an gaya masa kuma filla-filla Labarin Kristimati (Luka 2:1 – 21). Ta kuma sanar da shi game da mika Yesu da aka yi a haikali (Luka 2:22 – 40) kuma game da ziyarar Yesu a haikali lokacin da yana dan shekara goma-sha-biyu (Luka 2:41 – 52).
Wannan Likita ba Hellene ya tattara Misalai da sauran basu ambata ba: Batacciyar Tunkiya (Luka 15:1 – 7), Bataccen da (Luka 15:11 – 32), Nagarin Ba Samariye (Luka 10:25 – 37), Mai arziki da Li’azaru (Luka 16:19 – 31) da kuma rahoton kutare goman da Yesu ya Warkar (Luka 17:11 – 19). Luka ya saurari misali na ba Farise da Mai karban haraji (Luka 18:9 – 14), ya lura da ziyarar Yesu wurin Zaka (Luka 19:1 – 10) da kuma hawayen da Yesu ya zubar domin Urushalima (Luka 19:41 – 44). Luka ya hada da labarin Maryamu da Marta (Luka 10:38 – 42), ya rubuta sunayen almajirai mata da suka bi Yesu (Luka 8:1 – 3), watakila a wajensu ya koyi kalmomi uku na musamman wadanda Yesu ya furta a kan giciye (Luka 23:34 – 43 & 46).
Luka ya nemi cikakken bayani game da haduwan Yesu da almajirai biyu a hanyar zuwa Imwasu bayan tashin matattu (Luka 24:13 – 35) da sauran bayanai akan koyarwar da Yesu yayi masu a cikin Tsohon Alkawali wanda ya basu mamaki (Luka 24:44 – 49). Shine kadai ya bada rahoton yadda Yesu ya koma sama (Luka 24:50 – 52; Ayukan Manzanni 1:1 - 14).
In ba don Likita Luka ba, da bamu san yawancin muhimman nassoshi a Linjila ba. Ya rubuta Litattafansa guda biyu zuwa ga mutum daya, wato Tiyafilus, Gwamnan Roma wanda ya zama Krista Antakiya. Ubangiji wanda ya tashi daga matattu, tawurin Ruhunsa Mai Tsarki, ya jagoranci Luka wanda “bako” ne ya tattara zahiri na tarihi ya rubutasu jeri-jeri da aminci. Litattafansa ya rubuta su da goyon baya da kuma hatimin Ruhu Mai Tsarki. Yesu da kansa bai rubuta Littafi ba ko dashike ya iya rubutu da karanta Ibrananci. Amma shaidun da suka ga abinda yayi sun bada kakkarfan shaida mai aminci game da abinda suka gani suka kuma ji.
● Yahaya 1:14 ya bamu muhimmiyar taimako yayin da muke zance da musulmai: “Kalman ya zama jiki, ya zamna a wurin mu. Muka duba daukakarsa, kamar ta hafaffe daga wurin uba, cike da alheri da gaskiya kuma”.
Yahaya ya gane cewa Yesu ba yayi wa’azin Kalmar Allah ne kadai ba, amma shi da kansa ne Kalmar! Babu bambanci tsakaninsa da kalmominsa ko Ayukansa. Saboda haka ya kasance babu zunubi. Kalmar Allah kan yi halitta, warkaswa, gafara, ta’aziya, kuma ya sabonta mai bada gaskiya. A cikin Yesu ne nufin Allah da ikonsa sun bayyana a fili. Bayyanuwar Kalmar Ubangiji cikin jiki da muka gani a cikin Yesu ya takaita mana duka kalmomin Allah cikin rayuwansa. Duka alkawuran Allah, cikakku ne cikin Kristi. Bama bada gaskiya cikin addini, amma ga Kristi da kansa! Bamu dogara ga kalmomin Ubangiji da aka buga a Littafi ba kadai, amma mun fara dogara ga Yesu ne ba ya canzawa. Za a iya gurbata Littafi a halakar dashi. Amma Yesu yana raye har abada. Shine Kalmar Allah Kur’ani ya shaida wannan gaskiya sau biyar. Ya kamata mu gane wannan budaddiyar kofar, mu shiga, tawurin shigarta mu yi wa Musulmai bisharar Yesu a matsayin Kalmar Allah wanda ya bayyana cikin jiki.
● Yahaya 16:13 ya kunshi jumla mai ban sha’awa: “Amma sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya taho, za ya bishe ku cikin dukan gaskiya”.
Sa’anda wani Musulmin daya zama Krista a Kashimir ya karanta wannan nassi, yayi tambaya cikin farin ciki, “Kana da Ruhu na gaskiya”? Ya cigaba da cewa, “In ka karbi Ruhun gaskiya, bazaka iya yin karya ba. In kuma kayi karya cikin kuskure, Ruhun gaskiya zai tilasta ka ka furta wannan zunubi. Wannan Ruhu baya yarda da ha’inci. Wannan Mutumin Kashmir bai jira a bashi amsa ba, ya cigada da cewa”, In Ruhun gaskiya yana cikin Krista baza su iya gurbata Baibul ba! Wannan Ruhun gaskiya ba zai bar wannan ya faru ba”.
Wannan shine ainihin matsalar! Musulmai suna tuhumar Yahudawa da Krista da laifin gurbata Baibul, domin babu Ruhun gaskiya a Islama. A Islama, an yarda a yi karya bisa yanayi kashi hudu: A Jihadi, a yin sulhu tsakanin Musulmai biyu, sa’anda maigida na Magana da matayensa, da kuma lokacin da mace take Magana da mijinta. Za a iya karya rantsuwa da aka yi cikin hanzari (Sura al-Tahrin 66:1 – 2). A Islama Allah ya kira kansa mafi iya yaudara (Surorin al-Imran 3:54; al-Nisa’ 4:132; al-Anfal 8:30). Wanene zai yi mamakin ganin musulmai suna tuhumar wadansu a matsayin mayaudara Kaman ruhun da ke cikin Kur’ani? In kana kokarin bayyana wa Musulmi amincin Baibul sai ka fara yin adu’a da Ruhun gaskiya zai lullube su tare da kai ma. In ba haka ba, gaskiya da aminci zasu kasance bakin kalmomi.
● Yahaya 17:17 ya bayyana mana asirin adu’a ta babban Firist wanda Yesu yayi. A nan ne ya furta a bayyane – gaskiya da amincin Baibul a takaice: “Maganarka it ace Gaskiya”! Wannan jumla ta fi gaban koyaswa, huduba, ko shaida. Maimakon haka, Yesu ya fada mana zahiri da gaskiyar maganar Allah a cikin Zancen sa a adu’a da Ubansa na sama. Duk abinda masu neman ‘yanci, Musulmai masu gaba da Kristi ko kuwa masu bin addinin kwamnisanci zasu kawo gaba da Baibul za a ragargaza shi a gaban bayyananniyar gaskiya ta Allah. Duk abinda zasu iya kawowa a matsayin shaida, gurbata ko abinda ke da dangantaka da wannan, Shaida ta Dan Allah Zuwa ga Ubansa: “Maganarka it ace gaskiya” zai rushesu.
A cikin harsunan Yahudawa da Larabawa gaskiya ma na nufin “ doka da yin abu daidai”! saboda haka wannan jumla na nufi: Maganar Allah na kunshe da duka dokokinsa, ka’idodinsa da Shari’unsa da kuma duka alheransa, kafara da Mutuwarsa domin mu. Duk wanda rayuwansa ya saba wa dokokin Littafi Mai Tsarki, dan tawaye ne. Amma duk wanda ya bada gaskiya kuma yana kiyaye Kalmar Yesu zai barata kuma za’a sabonta shi. Kalmarsa ne rayuwanmu, karfinmu da begen mu. Ko wane mai yi wa Ubangiji hidima yana da tushen moriya wanda zurfin Ilimi, Shirye-shiryen kungiyar siyasa ko mafarkai da suka fi karfin fahimta basu sani ba. Kakkarfan gaskiyar maganar Ubangiji wanda baya canzawa; Kristi ne gaskiyar kuma Kalmar Ubansa wanda ya zama mutum.
● Wahayin Yahaya 2:18 – 19 yayi mana kashedi wanda yayi daidai da tunanin Musulmi: “Ina shaida ma kowane mutum wanda yake jin zantattukan annabcin wannan Littafi, Idan kowane mutum ya kara bisa, Allah za ya kara masa alobai wadanda aka rubuta cikin wannan Littafi: Kuma idan kowane mutum ya dauki wadansu daga cikin zantattukan Littafin wannan annabci, Allah zaya kawasda rabonsa daga cikin itace na rai, daga cikin birni mai tsarki kuma, watau daga cikin abinda aka rubuta cikin wannan Littafi”.
Musulmai zasu iya gane ma’anan wannan kashedi: In ka kara wani abu akan maganar Allah, Allah zai kara maka alobai akan azaban da zaka sha har abada. In ka cire wani abu ko ka boye wata ma’ana daga cikin maganar Allah, Allah zai rage maka albarkar da aka shirya maka a cikin sama. Sakamakon wannan kashedi daga Allah na a bayyane: Wanene zai yi wautar gurbata maganar Allah in ya san hukuncinsa azaba ne wuta na har abada? Ba wanda zai iya yin tunanin cewa Ba Yahude mai tsoron Allah zai gurbata Attaura ko kuwa Krista na gaskiya zai gurbata Linjila. In bai yi imani ba kokuwa yana rayuwa ta zunubi, shi ba ba Yahude na ainihi bane ko kuwa amintaccen Krista, amma da na uban duka karerayi (Yahaya 8:37 - 45).
A cikin Tsoho da Sabon Alkawali zaka sami ayoyi da dama wadanda suka bada shaidar gaskiya da amincin Baibul kada mu karanta Littafi Mai Tsarki namu da ganewarmu ta Krista ba kadai amma mu koyi yadda zamu gane ayoyin da ke Magana da Musulmai. Littafi Mai Tsarki na kare kansa. Mu koyi sauraron Muryarsa, saboda mu iya fada wa musulmai gaskiya cikin kauna.
3.07.3 -- Muhawara Daga Tunanin Mutuntaka da Litattafan Kumran Akan Amincin Baibul
Musulmai dayawa a yau sun gaskanta da ilimin kimiyya, suna barin tunaninsu ta zamamin Muhammadu. Mai yiwuwa ne ka yi Magana dasu ka kuma karfafasu su yi tunani mai zurfi. Wadannan tambayoyi zasu iya taimakawa:
Wanene ya gurbata Baibul? Yahudawa ko Krista? Yawancinsu sukan amsa, Yahudawa ne. Zamu iya tambayansu: Kuna tsammani Krista zasu yi shiru in Yahudawa sun canza wani abu a cikin Attaura da Annabawa? Zahirin cewa kasancewan addinai guda biyu da kishiyoyi ne ya sa duk kokarin canza wani abu a cikin Tsohon Alkawali ko a bainin jama’a ko a asirce ba zai yiwu ba. In kuma sun ce ai Krista ne suka canza Attaura, za ka iya gaya musu cewa ai da Yahudawa sun fara jihadi akan wadanda suka saba wa Litattafansu. Yahudawa masu ibada zasu ma iya yakan ‘yan’ uwansu Yahudawa marasa bin addininsu cikin gaskiya saboda su kare maganar Ubangijinsu.
Yaushe ne aka gurbata Attaura? In amsarsu “Kafin” haihuwar Muhammadu ne, zaka iya tambayarsu Me ya sa Muhammadu ya kira sunan Musa sau 136 a cikin Kur’ani, Ibrahim sau 69, shaidan sau 68, Israi’la sau 47, Suleimanu sau 17 da Dauda sau 16. Kur’ani kai tsaye da kuma a hannunka mai sanda ya tabbatar da cewa Allah ne ya Saukar da Attaura Shekaru goma sha biyar na farkon aikin Muhammadu na addini, ba tantama ya yarda da cewa Attaura gaskiyar Allah ne. Ko dashike bai iya karanta Ibrananci ba amma ya dogara ne ga masu juya masa nassoshin zuwa Larabci. Wadannan masu juya masa basu gaya masa gaskiyan da ke cikin Baibul ba, amma sun gaya masa Labarai ne da ke cikin Litattafan sharhi na Yahudawa wato Mishna da Talmud.
In musulmi ya tsaya akan an gurbata Attaura ne a shekarun Muhammadu na karshe ne a Madina zaka iya bashi amsa cewa a wannan lokaci an riga an juya Baibul cikin harsuna da dama kamar su Helenanci, Latin, Armenanci, Siriyanci, Kaldiyanci, Koftanci, Habashanci da sauran wadansu yarurruka.
A cikin wadannan yarurruka akwai Litattafai da dama da aka riga aka rubuta. Wanene zai iya tatattara wadannan juyi na Baibul da aka yi har ya canza wansu kalmomi a wadansu shaffuka? Yadda Baibul ya riga ya bazu a zamanin Muhammadu, ba zai iya yiwuwa a gurbata shi ba.
Menene da kuma Wadanne surori ne aka gurbata a Baibul. Babu Musulmin da yake da cikakken amsar wannan tambaya! Yawancinsu basu san abinda aka aka rubuta a Attaura ba. Saboda haka muna da Baibul na ainihi amma idan suna da wani, muna shirye mu karba mu bincika. Daganan ne fa muke da daman mu dage cewa Baibul namu na ainihi ne. Ba mune da ake tuhuma ne zamu hakikanta gaskiya da amincin Baibul ba, nuna mana wanda suka ce shine gaskiyar – wannan ba za su iya yi ba sai idan sun kawo mana Baibul na ainihi, mu zamu ci gaba da basu Baibul na ainihi wanda aka tsare daga gurbata.
Malam Deedat yayi kokarin wofinta Baibul da taimakon hamayyar da Turawa arna suka yi suna sukar Baibul a karni na goma sha tara. Yawancin Muhawararsa kimiyya ta riga ta amsa su. Ko da haka, Mishanarai masu aiki cikin Musulmai yakamata su karanta Litattafan Deedat da amsoshin da abokin hamayyarsa, Malam Gilchrist, lauya daga Afirka ta kudu ya bayar. Wadannan amsoshi zasu taimaka.
Wadansu Musulmai masana sukan nuna sharhin da akan rubuta a karkashin Sabon Alkawali na Hellenanci, Wanda yakan nuna ‘yan bambance-bambance a kofi dabam-dabam na ainihin Littafin don su nuna muhimmancin zargin da suke yi. Amma wadannan abubuwan da suke zargi akai na nuna gaskiya, aminci da kwazo na masu bincike, masana tauhidi da masu ilimin harsuna wadanda basu kago nasu Baibul da kowa zai bi ba, amma don nuna gaskiya sun cigaba da tsare Baibul har ma da wadannan bambance-bambance. Babu wani Littafi a duniya wanda aka hakikanta gaba daya kamar Sabon Alkawali wanda yake da kofi sama da 1500 wadanda sunanan. Da Kur’ani, abin ya sha bambam! Lokacin da Muhammadu ya mutu, akwai kofi na Kur’ani kimanin goma sha biyu wanda bambance-bambance da ke ciki ya kawo hargitsi da hamayya a tsakanin sojojin kalifofi. Kalifa Usman ya umurci Zaid b. Thabit daya shirya Kur’ani daya da za a yi amfani dashi sa’annan ya sa aka kone sauran. Musulmai nayau basu da ainihin Kur’anin Muhammadu, wanda suke dashi shine wanda kalifa Usman ne da aka shirya. “Yan shi’a har wa yau sana cewa an gurbata Kur’anin khalifa Usman.
Littafin Ishaya Kofin Kumran
Wani yaro makiyayi ne ya sami kofin Litattafan Kumran kusa da Tekun gishiri. Wadannan suna da muhimmanci a nuna gaskiyar Baibul na ainihi ne. A cikin wadannan kofi, abinda ya bada mamaki shine Kofin Littafin Ishaya wanda babu gurbata a cikinsa. Masana kimiyya sun gwada da na’ura sun ga cewa an rubuta wannan kofi wajen shekaru 150 zuwa 100 kafin haihuwar Kristi. Kafin a sami wadannan, kofin Attaura wanda ya fi tsufa an same shi ne daga shekara ta 875 A.D.
Bayan an gano Littafin Ishaya a Kumran, nan da nan ya zama abu mai yiwuwa a gwada Littafin ko akwai kuskurori a cikin Shekaru 1000 na kwashe shi da aka yi ta yi, ko kuwa an gurbata shi da gangar. Wannan lokaci da aka diba ya hada da lokacin rayuwar Muhammadu da farkon addinin Islama saboda a iya kamala bada amsan tuhumar gurbata da aka yi.
Mai kwashewa yayi wadansu kuskurori a rubuta bakake lokacin aikinsa Kowane kukure an gyara shi tawurin rubuta ainihin wannan bakin a bisan sa. Ba a goge ko baki daya ba, an yi kome a fili. A karshen wannan gyara an kirga duka bakaken da ke cikin Littafin sau da dama an ga sun yi daidai da wanda ake da shi. Littafin Ishaya wanda aka samu a kogon Kumran zai iya sa Musulmi mai kaunar gaskiya ya rude.
A cikin duka zance game da amincin Baibul, yana da kyau kada a manta cewa babu inda Kur’ani yace an gurbata Linjila. Muhammadu ya darajanta Krista kuma ya sani baza su yi masa karya ba ko kuwa su yi masa wata dabara. Ko ta yaya, wannan Muhawara za a iya kawo shin a ta hanyar tambaya saboda kada a kunyatar da Musulman.
3.07.4 -- Ta Yaya Kur’ani Ya Shaida Amincin Baibul?
A farko, Muhammadu ya darajanta Yahudawa da Krista domin suna da Litattafai masu Tsarki ya yarda da shaida tasu ta baki wanda aka juya masa cikin harshen larabci, an kuma hada su cikin Kur’ani. Wanda ya kafa addinin Islama bai sami daman karanta Attaura da Linjila cikin harshensa ba, domin a wannan lokaci ba a riga an juya su zuwa harshen Larabci ba. Bayan Muhammadu ya kafa gwamnatin Islam a Madina kuma ya sa rai ga amincewa, yarda da mika wuya daga Yahudawa da Krista kuma bai samu ba, sai ya fara sukan su domin sun ki hadewa dashi. Tunda sun ki yarda cewa shi annabi ne, ya yake su, ya kore su ya kuma kashe Yahudawa. An sassauta wa Krista da fari domin Krista na Abisiniya sun ba Musulman da aka tsanantasu mafaka.
Daga lokacin da Muhammadu ya so ya ja ra’ayin Yahudawa da Krista zuwa ga Islama, akwai ayoyi da yawa a Kur’ani, wadanda za a iya amfani dasu don nuna wa musulmai cewa Muhammadu ya tabbatar da rashin Kuskuren Baibul.
● Za a iya samun ayoyi a sura al-Ma’ida. Yahudawan Madina sun gwada Muhammadu, mai gari da alkalin garin yayi sharia akan laifin zina wanda aka aikata a garin. Amma Muhammadu wanda bai iya karanta Attaura ba yayi zaton an dana masa tarko ne don a kunyatar da shine kuma a tona asirin sa don yin ramakon a wani dangi.(Sura al-Ma’ida 5:42). Saboda haka ya maida hukumci a hannun shugabannin Yahudawa da wadannan hujjoji (Sura al-Ma’ida 5:43 – 45).
“43 kuma yaya suke gabatar da kai ga hukunci, alhali a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa’annan suna karkacewa a bayan wannan? Wadannan ba mumimai ba ne”!
“44 Lalle ne Mu, Mun Saukar da Attaura, a cikinta akwai shirya da haske, annabawa wadanda suke sun Sallama, suna yin hukunci ita ga wadanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya, da manyan malamai ga abinda aka neme su dasu tsara daga Littafin Allah, kuma sun kasance, a kansa, masu bada shaida To, kada kuji tsoron mutane, kuma kuji tsoron na, kuma kada ku sayi ‘yan kudi kadan da ayoyin na. Wanda bai yi hukunci bada abinda Allah ya saukar, to, wadannan su ne kafirai”.
“45 kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (ana kashe) rai saboda rai, kuma (ana debe), ido saboda ido, kuma (ana Katse) hanci saboda hanci, kuma kunne saboda kunne, kuma hakori saboda hakori, kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda yayi sadaka dashi, to, shi kaffara ce a gareshi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abinda Allah ya saukar, to, wadannan sune azzalumai”.
Wadannan Muhimman ayoyi sune dalilin da baza a tilasta Yahudawa dasu Musulunta ba a kasar Musulunci! An yarda musu dasu yi shari’a bisa ga dokar da Allah ya basu. Wani Muhimmin dalili na wannan ka’ida ta shari’a an same shi ne a furcin Muhammadu wanda ya amince a wannan nassi na Kur’ani cewa a wannan lokacin, doka ta Tsohon Alkawali a cikin Attaura ta kansance. Ya kuma tabbatar cewa akwai jagora da haske a cikin Attaura da kuma hukunci wanda ya kunshi shari’a da hikima, jagora da jinkai. Wadannan ayoyi na Kur’ani na nufin Allah na jagorantar Yahudawa a hanyar da ta dace kuma baya badda su. Sun sami dama na zaben da Allah ya zabe su, tunda suna da Littafin da Allah ya saukar. Me yasa Musulmai zasu ce an gurbatar da Attaura?
● Haka ma Krista ba a tilasta su bin sharia Musulunci ba:
“46 kuma muka biyar akan gurabunsu da Isa dan Maryama, yana mai gaskatawa ga abin da yake a gaba gareshi daga Attaura, kuma muka bashi Injila, a cikinsa akwai shiriya da haske, yana mai gaskatawa ga abinda yake a gaba gareshi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa’azi ga masu takawa”.
“47 kuma sai mutanen Injila su yi hukunci da abinda Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abinda Allah ya saukar, to, wadannan su ne fasikai (Sura al-Ma’ida 5:46 – 47).
Krista wadanda ke zaune a kasashen Musulunci su haddace ayoyin nan guda biyu, domin suna kunshe da daman da Krista ke dashi na kasancewa Krista a wannan kasa. Babu wanda a shari’ance an tilasta masa ya zama musulmi.
Asalin wannan daman a Musamman shine: Allah ya aiko Isa ya tabbatar da amincin Attaura a matsayin babbar Muhimmiyar aikinsa (Matiyu 5:17 – 18). Wannan aya ya kuma na bayyana cewa a Kur’ani an amince cewa an saukar da Linjila tawurin furci wanda ya Kunshi jagora da haske. Bugu da kari, mun karanta cewa Linjila wanda Kristi ya koyar ya tabbatar da Attaura da kansa. Wannan tabbatarwa nunki biyu na nuna amincin attaura ta hanyar Yesu da Linjilarsa an hakikance dasu tun zamanin Muhammadu har zuwa yau. Saboda haka wannan furci na Allah a cikin Kur’ani zai rufe bakin Musulmai wadanda ke tuhumar Krista da gurbata Linjila.
Muhammadu ya bar Allah ya nuna jagora ta musamman da wa’azi wanda Krista ya yi wa mabiyansa. Wata kila yana Magana game da wa’azi akan dutse ne (Matiyu 5:7), wanda Muhammadu bai iya karantawa ba, domin dole sai an juya shi zuwa Larabi. Kari akan wannan, Muhammadu bai iya karantu ba a farkon aikinsa na addini (Sura al-Airaf 7:158 – 159).
Daga wadannan zahiri, kuma daga wa’azin da an ce daga Allah ne Muhammadu ya zartar da hukunci ya kuma bar Allah ya Umurta cewa duk wanda yake da Linjila yayi rayuwa bisa ga koyarwarta. Duk Krista wanda bai yi rayuwa bisa ga koyarwar Linjila bashi mai laifi ne.
Krista a cikin wannan aya ta musamman an Kirasu Mutanen Linjila domin sukan yi Magana da Muhammadu da Musulmai daga Linjila kuma suna aikatawa.
Wannan lakabi na girmamawa ya bayyana a wannan sura ne kadai saboda haka ya bayyana Krista a matsayin bishara da ke Bayyane tawurin rayuwar Krista.
● A cikin wannan sura (5:48) Muhammadu ya bar Allah ya bayyana aya ta musamman gareshi:
“48 kuma Mun saukar da Littafi zuwa gareka da gaskiya, yana mai gaskatawa ga abinda yake a gaba gareshi daga Littafi (Taurata da Linjila), kuma mai halartawa a kanshi”.
Musulmai sun gaskata cewa akwai Littafi na asali a sama, Uwar duka Litattafan da aka saukar daga inda kowane annabi ya karbi wadansu shafuffuka. Da wannan aya Muhammadu ya bar Allah ya fadi cewa Kur’ani na tabbatar da Attaura da Linjila a zamanin Muhammadu, kuma cewa Allah da kansa yana lura da maganarsa yadda babu wanda zai iya gurbata shi. Allah yayi barci ne lokacin da Yahudawa da Krista suka gurbata Baibul yadda wadansu musulmai suka ce? Allah ya karyata duk mai zaton haka.
● A cikin wannan surar (5:68) Muhamma ya kusa zama “mai bishara”. Yayi fushi sa’anda ya ga Yahudawa da Krista suka ki gaskata shi kuma wadansun su basa rayuwa bisa ga umurnin Litattafansu.
“68 ka ce: Ya ku mutanen Littafi! Ba ku zama a kan kome ba, sai kuntsayar da Attaura da Injila da abinda aka saukar zuwa gareku daga Ubangijin ku”.
A wannan aya Muhammadu ya kalubalanci Yahudawa da Krista dasu karanci Attaura da Linjila kuma su yi rayuwa bisa ga koyaswarsu kuma su shirya su kuma yi sharia bisa ga koyarwarsu. Muhammadu a wannan lokaci ya gaskanta da cewa duka Litattafan da aka saukar suna da asali daya kuma suna goyon bayan juna. Shi bai yi tunanin an gurbata Attaura da Linjila ba bacin haka ya umurci mutanen Littafi da suyi amfani dasu a rayuwa ta yau da kullum.
Wani ba larabe mai bishara a Jordan yayi amfani da wannan aya, ya daga Baibul a hannun damansa yana Magana da karfi yana kai da kawowa a tsakanin jiragen kasa guda biyu da ke dauke da masu zuwa aikin hajji zuwa Makkah yana cewa.
“Baku zama akan kome ba sai kun tsayar da attaura da Linjila”! Mai bisharan ya cire abinda aka fada da farko da na karshe sa’annan ya kira musulmai da su zo su sayi Baibul daga wurinsa. Babu wanda ya kawo masa hari don ya na maimaita ayar da aka saukar ne daga Kur’ani.
● A cikin Kur’ani akwai ayoyi masu taimakawa, amma kada ayi amfani dasu kowane lokaci. A sura Yunis 10:94, Allah ya Umurci Muhammadu:
“90 To, idan ka kasance a cikin shakka daga abinda Muka saukar zuwa gareka, sai ka tambayi wadanda suke karantun Littafi daga gabanka”.
Muhammadu ya nemi sanin gaskiya daga wurin Yahudawa da Krista, wadannan abubuwan da aka fada masa ya ajiye a zuciyarsa. A lokacin da farfadiya ta bugashi sai ya rika fadin abubuwan daya koya a matsayin wahayi cikin harshen Larabci. Wani lokaci yakan yi kokorin maimaita abinda aka fada masa amma baya iya tuna su. Hanya mafi sauki a gareshi shine ya bar Allah ya umurce shi ya sake tambayar wadanda suka koya masa wadannan ayoyi don sanin ma’anarsu. Ta yaya musulmai zasu ce an gurbata Baibul, in a Kur’ani Allah ya umurci Muhammadu da ya koma gun Yahudawa da Krista saboda su bayyana masa abinda yake a Kur’ani domin sun karanta Littafin kafin shi? Kada mu bayyana abinda ayannan ta kunsa ga Musulmai da kanmu, amma mu tambaye su ma’anarta har sai sun gane su kuma furta abinda suka gane a cikinta.
● A cikin sura al-Nahl 16:43 an bada irin wannan jumla ga duka Musulmai. An ce Allah ya fada wa Muhammadu:
“43 kuma bamu aika daga gabaninka ba, face wadansu mazaje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutanen Ambato idan kun kasance baku sani ba”.
Muhammadu ya karfafa Musulami da su je wajen Yahudawa da Krista lokacin da suna da shakka akan bayanin wadansu nassoshin Kur’ani, don su nemi sani akan Allah da dokokinsa. Amma Muhammadu bai aike su zuwa ga kowane Krista ko ba Yahude ba, amma ga wadanda zasu iya haddace wahayin da ke cikin Attaura da Linjila.
Duk wanda yake so yayi aiki a tsakanin musulami a matsayin mai hidiman Ubangiji ya haddace ayoyin Baibul har in da za a same su. Muhammadu ya aiki musulmai ga wadanda zasu iya haddace maganar Allah ba tare da rike wani Littafi a hannunsu ba.
● Akwai sauran ayoyi da yawa a Kur’ani da sun hakikanta abinda Baibul ya kunsa. Zamu sake bada guda daya wanda Allah ya saukar a Kur’ani:
“27 sa’annan Muka biyar a bayansu da Manzanninmu; kuma muka biyar da Isa dan Maryama, kuma Muka bashi Linjila, kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan wadanda suka bishi (Sura al-Hadid 57:27).
Sau da yawa Muhammadu yayi shaida cewa cikin abokan gaban Musulmai, Krista ne suka fi yin abokantaka, domin suna da tausayi da jinkai. Wannan dandanawa ta Muhammadu tun lokacin da aka tsananta masa a Makkah. Ya iza Musulmai 83 su gudu zuwa Habasha don samun Mafaka. Da suka je ba a maida su bayi ba amma an karbesu, an taimakesu an kuma basu ‘yanci. Muhammadu yayi tunanin yadda wannan zai iya yiwuwa. Ya gane cewa Allah ya saukarwa Isa Linjila ya kuma ya sa jinkai, kauna da tausayi daga wannan Linjila cikin zukatan mabuya Kristi cikin aminci.
Muhammadu ya gane wani abin mamaki daga wurin Krista, amma bai iya gane abinda ya iya canza su suka zama mutane masu kauna da taimako har ga makiyansu. An rubuta amsar wannan a Romawa 5:5b inda Bulus yace: “Allah ya kwarara kauna tasa a zukatan mu ta Ruhu Mai Tsarki da aka bamu”. Muhammadu bashi da kyakkyawan sani game da Ruhu Mai Tsarki ba, amma ya ga albarkarsa a cikin rayuwan mabiya Yesu Krista.
Wannan aya na nuna hanya mafi kyau da za a iya bayyana wa musulmai cewa ba a gurbatar da Baibul ba. Hanya mafi kyau shine na nuna kauna da jinkai zuwa ga magabtan giciye. Da rayuwanmu, adu’oi, shaida da ayukanmu zasu taimaki musulmi ya gane cewa Baibul na asali ne, akwai aminci da iko. Kowannen mu na da nawaya akanmu.
3.07.5 -- Shaida Daga Dandanawa ta Krista
● Bitrus ya shaida: “Ya Ubangiji, gun wa zamu je? Kai ke da maganar rai madawwami. Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah”. (Yahaya 6:68 – 69; Matiyu 16:16). Daga bisani, Bitrus ya goyi bayan wannan shaida a wasikarsa ta farko da cewa: “Gama sake haifarku da aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, saidai marar lalacewa, wato ta maganar Allah rayayiya, dawwamammiya” (1 Bitrus 1:23; Yahaya 1:13; 3:5).
● Yakubu, dan’uwan Yesu, ya tabbatar da wannan dandanawa a rubuce: “Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa” (Yakubu 1:18).
● Yahaya, mafi kankanta a cikin almajiran Yesu shima ya yi Shaida: “shi da ke tun fil azal kenan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taba, game da Kalmar Rai-wannan rai kuma an bayyana shi mu kuwa mun gani, muna bada shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun da ke tare da Uba, aka kuwa bayyana shi garemu-to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shine dai muke sanar da ku, domin kuma ku yi tara da mu. Hakika kuwa tarayyan nan tamu da Uba ne, da kuma Dansa Yesu Almasihu”. (1 Yahaya 1:1 – 3).
● Bulus ya cire kowace shakka yana cewa: “Gama bana jin kunyar bishara, domin it ace ikon Allah mai kai kowane mai bada gaskiya ga samun ceto” (Romawa 1:16).
● Marubucin wasika zuwa ga Ibraniyawa ya fada mana: “Domin maganar Allah rayayyiya ce, mai karfin aiki, tafi kowane takobi ]kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gabobi, har ya zuwa cikin bargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufa tata” (1 Ibraniyawa 4:12).
Cikin Shekaru 2000 na tarihin Ikklesiya mun karanta shaida iri-iri na maza da mata wadanda sun hakikance cewa kalmomin Yesu ruhu ne da rai, cike da iko, gaskiya da hikima. Fasto Wilhelm Busch daga Essen a Jamus ya karfafa masu bada gaskiya a Ikklesiyarsa a daren da akayi ruwan bama-bamai cikin Yakin Duniya ta Biyu: “Lokacin da aka busa jiniya kuka gudu zuwa mafaka, abu mafi muhimmanci da zaku dauka ba kudi bane ko takardar ajiyarkudi a banki ba amma Baibul”, domin “Bada gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace maganar da ke fitowa daga wurin Allah”. (Matiyu 4:4; Luka 4:4).
Dukiyar da ke cikin wakokin bishara da falkawa mutane ne masu bada gaskiya na amsawa lokacin da Allah na magana da su. Sun yabe shi don shi Ubansu ne, sun furta zunubansu zuwa gareshi, shi kuma ya gafarta musu, kuma suka karbi ikon Ruhu Mai Tsraki, wanda ya haifar da jinkai da kauna a rayuwarsu. Sun kuma ji kira na kai rayayyiyar Kalmar Allah zuwa ga duka al’ummai, don sai anyi bishara ga duka mutane sa’annan Yesu zai dawa.
Martin Luther ya rera wannan waka:
Ubangiji, ka karfafa mu cikin maganar ka
Ja Linzamin masu amfani da wayo ko takobi
Masu so su kwace mulki daga wurin Dan ka
Don su wofinta aikin da yayi
(Littafin waka ta Lutheran, Australia, 197,1).
Ikklesiya ta Leipzig ta rera wannan waka a 1579:
Kalmar ka gaskiya ce kuma zata dore
Alkawuranka tsayayyu ne har abada
A raye, ko a gadon ajalina
Kai, Ubangiji, nawa ne:
Ka tsare ni, ni naka ne
Ka bani duk karfin da nake bukata.
(Littafin wakokin Lutteran, Australai, 535,3).
3.08 -- Tambayoyi
In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan
Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.
Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.
- Menene ke kawo halin dari-dari cikin yawancin Musulmai game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki? Me ya sa irin wannan tunani ke hana yawancin su yarda da Attaura da Linjila?
- Wace matsala ce ta Shari’a da ta faru wadda ta sa Yahudawan Madina sun yi kokarin boye wa alkalin garin, wato Muhammadu wadansu dokokin Attaura?
- Wannene cikin tuhuma goma da aka yi wa Attaura ya fi hatsari gare ka?
- A ina ne Kur’ani ya fada cewa Yahudawa na duka duniya sun hada baki sun yarda su canza wadansu nassoshi a Attaura?
- A ina ne aka rubuta cewa an gurbata dukan Littafi Attura?
- Menene Kur’ani ya fadi gurbatar Linjila?
- Ta yaya zaka wayar wa musulmi kai cewa alkawalin da aka rubuta Maimaitawar Sharia 18:15-18 na “annabi Kaman Musa” ba Muhammdu ba ne?
- Ta yaya alkawalin Yesu game da zuwan Mai Taimako (Parakletos) ba zai taba yiwuwa a ce ya cika a zuwan Muhammadu ba?
- Menene Malaman Musulunci sun gane lokacin da suka gwada Kur’ani da Baibul? Ta yaya suka yi kokarin warware matsalar sabanin da suka samu a tsakanin Litattafan biyu?
- Wadanne ne kibiyoyi masu guba na Malam Deedat kuma me ya sa wannan ya iya girgiza bangaskiya wadansu Krista a nahiyar Asiya da Afirka? Bayyana matsalar da za a iya a samu aka tashin Yesu daga matattu bayan an bizne shi na yini uku da dare uku?
- Wadanne ne wurare guda biyu da za a iya samun bayani da za a yi wa musulmi na cewa ba a canza ko digo a Baibul ba?
- Ta yaya Ubangiji da kansa ya ba Irmiya tabbaci game da gaskiyar maganarsa da ba ta canzawa?
- Menene zamu iya koya daga Maimaitawar Shari’a 4:2 da Karin Magana 30:5 – 6 yayin da muka kare gaskiya da rashin kuskure na Baibul?
- Wadanne ayoyi ne a Tsohon Alkawali suke nuna cewa wannan Littafi Mai Tsarki da kansa yana kare gaskiyar da bata canza wa wanda aka saukar a cikinsa?
- Ta yaya alkawarin Ubangiji a cikin Ishaya 55:10 – 11 zai karfafa kowane mai hidiman Almasihu a tsakanin Musulmai?
- Me zai sa kowane Krista wanda yana mu’amala da Musulmai ya koyi wannan Magana ta musamman da Yesu yayi a Matiyu 5:17 – 18 kuma ya haddace?
- Ta yaya Yesu ya bada tabbaci akan dawwamar Maganarsa?
- Menene zamu iya koya game da gaskiyar Linjila daga gabatarwar Luka, Likita ba Hellene a bisharansa?
- Wace ganewa ce Musulmi zai samu na cewa an kira Yesu “Kalmar Allah cikin jiki a Littafin Yahaya da kuma a Kur’ani?
- Me yasa bukatar Ruhun Gaskiya ya zama mana da na musulmai dole? Me yasa wannan irin Ruhun gaskiya baya cikin Islama? Menene wannan zahiri zai iya haifarwa a hidimarka a cikin Musulmai?
- Me yasa Yesu a cikin adu’arsa ya iya furtawa ga Ubansa “Magarka gaskiya ce”? Menene wannan furci ke nufi?
- Me yasa Wahayin Yahaya 22:18 – 19 ke ba kowane Musulmi mai budden zaciya haske?
- Ta yaya wannan tambaya, “Wanene ya canza Attaura”? Zai taimakeka don nuna wa musulmai cewa babu wanda zai iya gurbata Baibul.
- Ta yaya tambaya, “Yaushe kake tsammani an canza Attaura” zai taimakeka ka jagoranci musulmi ya amince da rashin kuskuren Attaura?
- Me yasa kofi-kofi na rubutun hannu na sassan Baibul ba a tarasu sun zama daya ba ko kuwa a konasu? Me yasa an kona ainihin kofi-kofi na rubutun hannu na Kur’ani?
- Wace bayani zaka iya samu na amincin Baibul daga Littafin Ishaya da aka gane a kogon Kumran?
- Wadanne dama na musamman Krista ke da shi wanda yake zama a kasar musulunci a cewar sura al-Ma’ida 5:43 – 45? Ta yaya Muhammadu ya tabbatar a wadannan ayoyi cewa Attaura an saukar ne daga Allah kuma babu kuskure?
- Yaya ayoyi na musamman cikin sura al-ma’ida 5:46 – 47 na tabbatar wa Krista damansu na kasancewa Krista in suna zaune a kasar musulunci? Don menene duk Krista da ke zaune a tsakanin Musulmai yakamata ya haddace wadannan ayoyi? Ka bayyana abinda ayoyinnan guda biyu na Kur’ani suka kunsa!
- Ta yaya Muhammadu ya ce Kur’aninsa na tabbatar da Tsoho da Sabon Alkawali? Tayaya Allah a cikin Islama ya kamata ya kare wahayinsa? (duba sura al-Ma’ida 5:48).
- Me yasa Muhammadu ya kusa zama mai bishara yana bukatar Yahudawa da Krista su yi rayuwa bisa ga koyarwar Litattafansu? Menene wannan kira ke nufi a bangaren tabbatar da rashin aibin Baibul (duba sura al-Ma’ida 5:68).
- Wanene Muhammadu yakamata ya tambaye shi ma’anar abinda bai gane ba akan Wahayin da aka saukar masa? (duba sura Yunus 10:94).
- Ga wanene aka tura musulmai idan suna neman taimako don su gane Kur’ani? (duba sura al-nahl 16:43).
- Wacce ce kyakkyawar shaida ta nuna rashin kuskure da ikon da ke cikin Baibul?
- Wace aya ce a cikin shaidar Manzannin Yesu wanda ke nunawa a fili cewa Baibul Maganar Allah ne marar canzuwa.
- Me yasa manzo Bulus ya fadi cewa Bisharar Kristi na da cikakken ikon Allah? (duba Romawa 1:16).
- Ko Ubangiji mai rai ya yi maka Magana tawurin maganarsa a cikin Baibul? In mai yiwuwa ne, ka rubuta mana a gajarce abinda yace maka.
Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.
Naku cikin Hidimarsa
Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.
Ku aika da amsoshin ku zuwa:
The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.
Ko
GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY
Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net