Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":

Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 2 Muslims Differ

This page in: -- Arabic? -- Cebuano -- Chinese -- English -- French -- Georgian -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Kirundi -- Russian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Uzbek -- Yoruba

Previous booklet -- Next booklet

01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI

2 - Gaskantawa da Tunani Yakan Sha Bambam a Tsakanin Musulmai



2.01 -- Gaskantawa da Tunani Yakan Sha Bambam a Tsakanin Musulmai

2.02 -- Historical developments and practical realities

Duk wanda yake so ya gane tunanin Musulmai yakamata ya san abubuwan da suka faru a Tarihin Yahudawa da Krista zaunannu a kasashen larabawa a zamanin da. Addinin Islama bai bayyana haka ba kawai amma yana da tushe daga mu’amala tsakanin matsafa Larabawa, Yahudawa da Krista.

2.03 -- Yahudawa Da Krista Kafin Haihuwar Muhammadu

Sojojin Roma sun warwatsar da Yahudawa a wurare dabam-dabam, wadansu an sayar da su bayi bayan an kawo karshen tawayen su (70AD; 132 AD a 135 A.D.). An kafa gararuwan zaman Yahudawa a Asiya, Iraki, kasashen Larabawa na gaban teku, Misrah da Roma da kanta.

A ci gaba da yake-yake tsakanin kasashen da ke a mediteraniya da mayakan da suke fitowa daga kasar Asiya, Yahudawan da suke barin gabashin hamadan Siriya sun hada hannu da Sassanidawa suka yaki Romawa. Da taimakon abokansu suka kafa mulkinsu ta Yahudawa a kudu da Yemen, inda ake noman murruh da kayan kanshi wannan ya zama musu garu da ya tsaresu daga mamayar krista na kasashen Banzantayin.

Bayan da Romawa suka kawo karshen tawayen Yahudawa tsakanin Urushalima da Dimaska, Ikklesiyu na Krista sun tattaru a Alegzandariya, Antakiya, Afisu, Roma, Edassa da Konstantinoful. Sun kai bishara a Mesafotamiya, Habasha, Arewacin Afirka da Asiya ta Tsakiya. Krista na darikar Koftik Sun kai bishara a Arewacin Yemen, suka kafa mulki na addinin krista na shekaru da dama tare da Krista da suke a Nadjran. Yaki ya barke a tsakanin kasar Yahudawa a kadancin Yemen da kasar Krista a Arewacin Yemen. An sayar da bayi krista daga Siriya a Hedjaz. Akwai Ikklelsiya a Makkkah da ke taruwa a gidan Waraka bin Nawfal. A wannan lokacin ne Bishof na birnin Sohat, wanda yau yana a kasar Oman, ya zama daya daga cikin ‘yan majalisa na taron Nisiya.

2.04 -- Muhammadu da “Mutanen Littafi”

Muhammadu (575 – 632AD) ya ji sha’awar Yahudawa da Krista don suna da littafi wandake bayyana musu asirai na abubuwan da suka faru a baya har zuwa lokacin halitta, yana koya masu hanyar rayuwa tawurin dokoki, sa’annan yana nuna musu abubuwan da zasu faru a nan gaba har da ranar sharia. Muhammadu ya darajanta Yahudawa da Krista har ya kira su “MUTANEN LITTAFI”. Yayi sha’awar samun littafi irin wannan a harshen larabci. Yayi kokarin tattara labarun da zai iya samu akan Littafi Mai Tsarki da begen kafa nasa addini.

Muhammadu yayi sha’awar Ibrahim, makiyayi wanda ya yarda ya bada dansa hadaya ga Allah (Sura al-Saffat 37:99-113). Don wannan Kur’ani ya kira Ibrahim Musulmi na farko (Sura Al’mran 3:67). Musa, shugaban jama’a da kuma matsakanci tsakanin Allah da mutanensa na alkawari, an kira sunansa sau 136 a Kur’ani. Musa ya zama wa Muhammadu da Mabiyansa Misali da jagora don ya hada addini da mulki a rayuwarsa.

Labarun Ubanni na bangaskiya dana Sulemanu da dokoki da yawa na Musa sun cika ayoyi ninki goma na yawan ayoyin da suka yi magana akan dan Maryama, mai mu'ujjizan warkarwa da mabiyansa. Duk wanda ya karanta Kur’ani zai yi tunanin cewa musulunci daya ne daga cikin darikun addinin Yahudanci, musulmai suna musun wannan.

2.05 -- Tasirin Ikklesiyar Otodoks A Lokaci Kafa Addinin Islama

Ikklesiyar Otodoks na da tasiri mai karfi akan addinin musulunci fiye da Ikklesiyar Katolika ta Roma. Ko da shike Krista na Otodoks basu yi wa Muhammadu cikakken koyaswa akan Kirsti ba. Yayin da ‘yan darikar Koftik sun fi mai da hankali akan koyaswa game da Allahntakar Yesu kamar yadda ake koyarwa a makarantarsu ta Alegzandariya, Krista wadanda suka bi koyarwa ta makarantar Antakiya sun fi mai da hankali akan mutuntakan Kristi.

Salon sujadar musulunci ya sami tushe ne daga sujada ta Krista na Otodoks , da sukan durkusa da yi wa Triniti Mai Tsarki ban girma a makon da kan gabaci bikin Ista. Kalmar “qir’an” a tsakanin Ikklesiyar Otodoks da suke amfani da harshen larabci na nufin: a karanta bishara da ka a lokacin sujada. Wannan kalma da ma’anarta watakila ita ce tunshen kalma “kur’ani”. A littafi Mai Tsarki na Asuriyawa, kalma ceto shine” furqan”, wanda aka yi amfani dashi sosai a kur’ani.

2.06 -- Muhammadu Da Bambance – Bambance Da Ke Tsakanin Yahudawa Da Krista

Muhammadu na sane kwarai da jayayyar da ke tsakanin Yahudawa da Krista (Sura al-Baqara 2:113 d/s). Ana ta fada tsakanin Yahudawa da Krista na Arewaci da Kudanci Yemen na darurrukan shekaru, duk wadanda suka ci nasara a yaki, sukan azabta wa wadanda aka fi karfinsu. Muhammadu ya dauki wannan rarrabuwa a kaddarar Allah ce wanda ya dame hankalinsu ya sa su gaba da juna a Hedjaz, saboda a iya yada musulunci cikin nasara a tsakanin abokan gaban da yaki ya rage karfinsu. Muhammadu ya bayyana kaman dankallo amma daga karshe ya yi nasara akansu.

Yahudawa sun ki Muhammadu a matsayin annabi, sun gane kurakurensa a Kur’ani kuma sun yi masa ba’a a fili. Saboda haka ya la’antasu sau goma (Sura al-Baqara 2:65-66; al-Maida 5:60; al-Araf 7:163-166 d/s). Ya kirasu abokan gaba mafiya hatsari ga musulunci (Sura al-Ma’ida 5:82). Ya tilasta wa Yahudawa masu arziki su yi hijira, yana mai da wadansu bayi wadansu kuwa ya kashesu da takobi.

2.07 - Ikklesiyar Otodoks Sun Dade Suna Shan Wahala

Da farko, Krista da suke a kasar larabawan da suke a gabar Teku an dauke su abokai ne a tsakanin abokan gaban musulmai (Sura al-Ma’ida 5:82). Amma da suka cigaba da shaida cewa Yesu Dan Allahne, an la’antasu Kaman Yahudawa (Sura al-Tawba 9:30). Bayan shekaru kima, kalifa Omar Ibn al-Kattab ya kore su.

A nasarar Yaki na (632-732 A.D.) Mayaka Musulmai sun kame muhimman cibiyoyi na addinin Krista na farko: Urushalima, Alegzandariya da Antakiya. Daga nan aka kame Konstantinoful da Afisu a zango na biyu na yada Islama. Yawancin Krista a kasashen yamma sun manta, sun yi watsi da ko na’am da wannan babbar masifa a tarihin Ikklesiya.

An sha gwada wa Ikklesiyoyin Otodoks wahala. An muzguna masu, an tsananta su an wulakantasu na tsawon shekaru 1.370. a lokacin Muhammadu yawancin mazauna kudu maso gabar da Arewa maso gabar na meditarraniya Krista ne na Otodoks, amma haka aka musuluntar da su tawurin haraji, danniya da kaskanci. Kashi goma bisa dari ne suka rike bangaskiyar su cikin Kristi har da yadda aka maidasu kaman bare a kasarsu. Musulumai masu mulki sukan yi wa wadannan ‘yan kasa masu biyaya kwace. Krista basu zama musu abin fargaba ba. Tawurin halayen su, musulmai sun dauki Krista masu tawaliu ne da kaskantar da kai da kowane lokaci za a iya danne su.

Kakkarfar sujada ta Triniti a Ikklesiyar Otodoks da irin shugabancin ta wannan ya taimaka har yanzu tana a raye. A kasashen da ba na musulmai ba, sukan yi biyaya ga masu mulki amma wannan kaskantar da kai yakan sa a maida su Addinin kasar (bazantiya, Rasha, Gris, Sabiya d/s). a kasashen musulmai akan tilasta Bishof- Bishof da Dattawa su karbi haraji daga wurin Krista a kai wa masu mulki. Ladansu shine akan dan kara musu iko a cikin Ikklesiyansu. Sauran Ikkesiyun Otodoks da membobinsu a yau sun kai Miliyan 250, kuma sune kashi 14 bisa dari na yawan Krista a duniya.

2.08 -- Musulunci Da Ikklesiyar Katolika

Ikkelesiya ta Katolika, koda shike akwai rarrabuwa a cikinta, musulmai suna daukanta a matsayin ikklesiya mai fada. Suna mata ganin kungiyar addinice da ta siyasa mafi karfi a duniya, har bayan shudewan mulkin Roma da kuma hargitsin neman gyare-gyare a Turai.

Sojojin Charles Martell wanda shi Katolika ne sune suka fara tare mayakan musulmai a Twas kusa da Faris, a Faransa (A.E. 732). Jihadi na katolika da suka yi ya raunana Ikklesiyar Otodoks da nasarar da aka yi akansu a Konstatinoful (A.D. 1204) wanda ya kai ga karyewar kakkarfan wuri na addnin Krista a gabas. Wannan wuri ya fada a hannun musulmai a shekara ta 1453. ba da dadewa ba a shekara ta 1529, Turkawa suka fara toshe kofofin Vienna. Lokacin da suka kewaye Vienna na biyu a 1683, sojojin Katolika ne na Foland suka tsayar da kutsawar da musulmai suke yi na neman mamaye dukan Turai.

A wannan lokaci Romawa masu tsananta wa mutane sun kori dubban Yahudawa da musulmai daga Sfen da Turai. Ikklesiyar Katolika da Jihadinsu sun sa Krista sun yi bakin jini a gun musulmai. Ikklesiyar Katolika ta zama kishiya ga musulunci a batun tunanin gina kasar da ke mulki ta addini. Wannan magabtaka ya kawo karshen yaduwar addinin musulunci.

Tun da musulmni suna zaton kawane aiki ko kokarin da Krista suke yi suna so su kafa mulki ne irin ta Krista. Basu amince da kokarin da ikklesiyar Katolika wanda suka zatar a majalisar su ta Vatican na su bude kofofin su karbi duka abubuwa masu kyau daga dukan addinai na duniya. Rokon da Fafa Roma John Paul II yayi na neman samun hadin kai tsakanin Krista da Musulunci bai sami karbuwa ba domin musulmai sun gaskanta cewa Ikklesiyar Katolika na kokarin kafa mulkin Kristi ne a duniya da wayo. Ikon da ke ofishin Fof ya iya hada kan Ikklesiyar Katolika a kalkashi tsaikonta: “Mulkin ka shi kasance a duniya kamar yadda yake a sama”, Mabiya darikar Katolika sune kusan rabin yawan Krista a duniya. Membobinsu sun kai miliyan 950 a duk duniya.

2.09 -- Addinin Musulunci Da Ikklesiyun Furotesta

Ikklesiyoyin Furotesta tun asalinsu masu “sukan ra’ayine” wadanda suka yi kokarin kawo canje-canje a ikklesiyar Katolika. Sun zabi Littafi Mai Tsarki kadai, sun ki bin ala’dun Katolika, sun yi imani akan ceto tawurin alheri ne kadai, ba tawurin ayuka ba kuma sun dogara ga Kristi wanda shine matsakanci ba uwarsa Maryamu ba.

Yawancin Ikklesiyu na Furotesta a Turai a karni na fari bayan samun canji, Ikklesiya ce ta sarakunan yankunan da suke. Falkawa mai karfi yayin fadace – fadace da yamutsi, ya haifar da amsa kira mai karfi na zuwa aikin bishara a Amerika, Turai da Koriya. Tauhidi na masu zurfin tunani wanda babu cibiyar Ikklesiya da ke da ikon kayyade tauhidin su ba, ya sa yawancin Furotesta masu halin ko in kula sun fada cikin ‘yanci wanda bai gamshi Allah ba. Ikklesiyun su na cin gashinkai wadanda ke da membobi miliyan 600, sun dauki kashi daya bisa uku na duka Krista na duniya.

Ikklesiyu na Furotesta, wadanda suka bayyana kimanin shekara 450 da suka wuce, sun fara kai bishara duniya a karni ta 18 da 19. sun tura injin buga litattafai na farko zuwa kasashen gabas kuma sun buga tarjarmmar Littafi Mai Tsarki a cikin yarurrukan musulmai, sun sa ya zama a bu mai yiwuwa a buga Littafi Mai Tsarki, Kur’ani, da kananan litattafai. Makarantun Furotesta da na masu kawo agaji sun kara karfin aikin bishara wanda yake da tushen buga Littafi Mai Tsarki.

Wata miskila da aka samu ita ce, ayukan furotesta sun shafi Krista ‘yan Otodoks wanda ya sa wasu fastocinsu sun zama abokan gaban furotesta.

Musulmai suna tuhumar Ikklesiyun Furotesta domin yadda suka dauki mutanen Israila a matsayin Zababbun mutanen Allah. Akan dauki Mishanarai na furotesta a matsayin ‘yan leken asiri da mataimakan Tsohon Alkawali.

Musulmai masu sassaucin ra’ayi sun sha bambam a tunaninsu akan Krista Furotesta. Wani babban malamin musulunci ya yi tambaya, “me ya sa Furotesta ne suka fara zuwa duniyar wata?”shi da kansa ya bada amsar tambayarsa ya ce, “mu musulmai akwai abinda ya toshe tunaninmu shi ya sa bamu iya gina fasaha ta zamani ba. Kullum Katolika dole ne su furta zunubansu kuma su zama da tawali'u. Furotesta ne kawai sun iya gina ruhun yanci wanda ke karfafa su su gwada yin abubuwan da ana gani basu yiwuwa”. Duk kokarin a wofinta abinda malamin ya fada ya zama banza. Har ma da kokarin nuna hatsarin da samun cigaba cikin fasaha ke kawowa wannan bai canza tunaninsa ba.

Yana da nasa ra’ayi game da muradi da manufa a cikin addinai na wannan zamani.

2.10 -- Darikun Krista Dana Musulunci

Wadannan manyan sassa na Ikklesiya guda uku wadanda suka rarrabu cikin kananan Ikklesiyu.masu cin gashin kai, majalisu ko kungiyoyi da koyarwarsu ko kuma gudanarwarsu wanda suka wuce guda 22,000, wanda wannan rarrabuwa ya sa dole mutuba in mun tuna da adu’ar Yesu Kristi.: “Bari su dayanta, kamar yadda mu daya muke” (Yahaya 17:21-22).

Abu guda da har yanzu yake hada kan wadannan Ikklesiyu shine abubuwa uku da suka zama shika-shikai na katikizim (catechism). Wadannan sune: Adu’ar Ubangiji, Shaidar Bangaskiyar Krista da dokoki goma da bayaninsu bisa ga koyaswar sabon alkawali. An dauki Furcin shaida bangaskiyar mu ga Allah Uba, da Da da Ruhu Mai Tsarki ya zama bin alloli da yawa kuma shirka ne wanda a musulunce, zunubi ne da ba’a gafartawa. Ba su yarda da Triniti ba (Allah, uku cikin daya) amma Allah daya kawai. Sun kuma musanci giciyen Kristi, wanda shine tushen bangaskiyarmu (Sura al-Nisa’ 4:157). Musulunci ya hakikanta cewa shine babbar iko a duk duniya da ya fi gaba da addinin Krista (1 Yahaya 2:22-24; 4:1-5). Irin wannan tunani na da zurfi a cikin duka musulmai, kuma basu nuna wa a fili ba. Duka al’adun musulmai sun cika da halayen gaba da Krista.

Duk wanda ya gane rarrabe-rarrabe na Ikklesiyu a kasashen Gabas da kuma duka duniya ba zai yi mamaki ya ji cewa musulunci ma ta rarrabu kashi-kashi. Kamar yadda Ikklesiyu sun rarrabu sau dubu, addinin musulunci ma kazalika. Addinin musulunci na da manyan dariku kashi biyu.

2.11 -- Darikar Sunni – Mafi Girma a musulunci

Mabiya darikar sunni suna ganin kansu amintattu masu rike da addinin musulunci na ainihi domin ba kawai don suna bin kur’ani ba amma suna bin kwaikwayon rayuwan annabi Muhammadu (Sunna). Bayan an kifar da kokarin kawo zurfin Ilimi a musulunci (Mutaziyya) sai aka juya zuwa bin dokokin addini da aka samu daga shari’ar musulunci. Daga cikin kur’ani, Hadisai, yardan malamai da zurfin tunani aka kirkiro shariar musulunci. Sun gina dokokin da suka shafi kowane bangare na rayuwa fiye da ka’idodin bangaskiyar addinin musuluncin. Mabiya darikar sunni yawansu ya kai 84 bisa dari na duka yawan musulmai, sun kusa biliyan daya. Yawansu kusan daidai ne da na mabiya darikar Ikklesiyar Katolika.

2.12 -- ‘Yan Shi’a – Darika ta farko cikin musulunci

Lokacin da addinin musulunci ke girma, mabiyan Ali – dan da Muhammadu ya rene shi, Muhammadu kuwa, kawunsa ne, shi Ali kuma surukin Muhamamdu ne shine ya balle daga darikar Sunni tare da ‘ya’yansa – Hassan da Hussaini. Dalilin rabuwarsu ba don jayayya akan bangaskiya ba amma akan shugabanci na al’umman musulmi. ‘Yan shi’a sun nema a ce Ali ne da ‘ya’yansa sun dauki shugabancin musulunci bayan mutuwan Muhammadu. Wannan ya nuna addinin musulunci gwamnati ne ba addini bane kadai. ‘Yan Shi’a sun ci gaba da daukaka Ali da ‘ya’yansa biyu, suna kusan girmama su Kaman alloli kuma suka kirkiro rukunan limamai a rukuni daya akwai limamai bakwai, daya kuma akwai sha–biyu wadanda suke yi musu biyaya babu tambaya. Limamansu (ayatollah) sun ce suna karbar budi daga limami na karshe. ‘Yan Shi’a sun kai kimanin miliyan 200 wato kashi 14-16 bisa dari na dukan yawan musulmai a duniya.

Banda ‘Yan Shi’a, akwai dariku dayawa na addinin musulunci, hanyoyi, yadda ake sallah, jama’a, alkawura da hada kai, basu kuma da shiri su dayantu,amma suna kokarin cin gashi kai.

2.13 -- Yada Addinin Musulunci Yunkuri na Uku

Bayan yunkurin yada musulunci kashi na biyu zuwa Turai ya kasa cin nasara (AD 732 da 1683) domin sojojin Katolika, a yunkuri na uku wanda ya fara 1973 bayan karuwan farashin mai. Kasashen musulumai masu arzikin mai sun sami wadata. Tunda suna biyan wani kashi daga ribar da suke samu don yada addinin musulunci, tunani da shirye- shiryen musulmai masu tsatstsauran ra’ayi ya sami goyon baya. Ana basu kudi don aikata abinda suke so. Hassan al-Bana, Wanda ya fara kafa darikar “Muslim brotherhood,” a wa’azinsa ya ce “Musulmi wanda yana Sallah, Azumi yana bada Zakka ba musulmin kwarai ba ne. Sai dai in ana amfani da shari’ar Musulunci a kasar, sa’annan Musulunci ya cika.” Darikarsa ta rarrabu fiye da kashi hamsin a yawanci kasashen Musulmai.sun yi kokarin canza addinin musulunci da kuma kokarin kawo kasashen musulmai a kalkashin shari’ar musulunci.

A lokaci guda musulmai masu tsatstsauran ra’ayi sun fara kyakkyawan shiri don yada musulunci a nahiyoyin nan biyar na duniya. A na ta kafa ‘yan kananan masallatai. Krista masu yawan sake ta hanyar marabtar musulmai a kasashensu wadanda ke da al’adu daban- daban. Basa so su amince cewa fiye da kowane zamani musulmai sun sami gindin zama a kasashen Krista ‘yan Furotesta. Muna zaune a cikin jihadinsu bamu gane ba!.

2.14 -- Wadanne irin Musulmai Muke Mu’amala da su?

Ba duka musulmai suke rayuwa ko suna yin tunani iri daya ba. Kowanne a dauke shi a mai cin gashin kansa. Ba zai yiwu a kasa su kashi-kashi ba. Iyawa iri-iri, al’adu daban-daban, Ilimi da abubuwan da suka yarda dasu duk sun taru akan mutun daya. Wanda yake so ya gane musulmi yana bukartar lokaci. Mu tambayi kowannen su inda ya fito, menene tunaninsa, abinda yake ji kuma menene damuwarsa. Duka amososhin da an bayar cikin zato ba zasu zama da amfani ba, idan muna son yin abokantaka da musulmai,muna bukatar matukan hakuri don mu gane su. Wannan ma gaskiya ne. duk ra’ayin da aka kaga dole ne a sake ta in an gane gaskiya. Musulmi yakan yi saurin ji ko gane muna darajanta shi ne ba muna kokarin amfani da shi bane, amma muna karban shi kamar yadda yake, bishara zai iya yin aiki a ikon Allah bayan an gina gadar amincewa da yarda. Nacewa cikin adu’a shine asirin dawwamammen albarka.

Ko da shike kowane musulmi yana da ra’ayin kansa. Zamu iya rarrabasu jinsi-jinsi yayin da muke magana akan kungiyoyin musulmai dabam-dabam.

2.14.1 -- Masu Ra’ayin Mazanjiya Da Asalin Wadanda Suke Tsoron Allah

A karkara da Jami’oi, a masallatai da cikin kowane irin sana’a, zaka iya samun musulmai wadanda suke so su yi rayuwa a bisa koyarwar Kur’ani da Hadisi. Yawancin su sun hadace kur’ani cikin larabci tun suna kanana. Sun sa “tabarrau na kur’ani “ta haka suke gane duniyarsu. Ban da al’adar Kur’ani da dokokin shari’ar musulmi, babu wani irin rayuwa da ke karbabbiya a garesu. Yan kungiyoyin asiri, sauran duka addinai da duka matsafa an dauke su kazantattu ne kuma Allah ya la’ance su. Abinci haramtacce da wanda ke halal ya raba duniya kashi biyu masu cin alade da mutane tsarkaka. Sayen nama a kasuwa wanda ba a furta masa “Bisimillah” ba lokacin yanka zai gurbata musulmi inji masu ra’yin mazan jiya, har da haka in ya zama musu tilas, ba laifi bane.

Ma biya addininsu ba a yarda musu da su yi tunani ko su soki ra’ayin Kur’ani ba, in zaka soki aya guda daya, duka tunaninsu da ganewarsu zasu rushe. Don haka, dole ne su kare addininsu duk lokacin da aka sami sabanin ra’ayi, Kur’ani ne rayuwarsu. Zaka iya bayyana gaskiyar bishara da taimakon kalmomin Kur’ani, wadanda zaka cika su da ma’anar bishara.

Abin mamaki, akwai dalibai da yawa masu ra’ayin mazanjiya. In sun shigo birni daga karkara kuma sun ga ‘yanci, rayuwar zunubi, sukan ji kunyar mutanensu, sai su koma a tushen al’adunsu su zama musulmai masu tsatstsauran ra’ayi fiye da yadda suke a da. Sukan yi kokarin tabbatar da abinda ya gina rawarsu kuma su kare gaskiya da mutuncin Kur’ani ko ta yaya.

Lokacin da masu tsatstsauran ra’ayi suka yi ilimi, sukan yi kokarin kawo canji ga mutanensu ta hanyar salama ko da karfi. Yawancin wadannan musulmai suna shirye su kashe musulmai masu yanci ko su kirkiro kungiyoyin da zasu tilasta bin ka'idodin musulunci a kasarsu.

Yawan masu tsatstsauran ra’ayi ya bambamta daga kasa-zuwa kasa. Sukan kai tsakanin 15-35 bisa dari. In an jefa kuri’a a kasashen su sukan dauki kashi 10 zuwa 20 bisa dari. Mafi yawan musulmai ba masu son kawo canji da karfi bane. Amma Kur’ani ya umurcesu da su kafa shari'ar musulunci a kasashen su koda halin kaka.

2.14.2 -- Musulmai Masu Sassaucin Ra’ayi

Kamar a kasashen Krista, yawanci musulmai a kasashen musulunci masu sassaucin ra’ayi ne da kaunar salama. Sukan yi aiki da hannunsu don samun abinda zasu ciyar da iyalansa. Basa neman abin duniya da yawa. Suna sa zuciyar su sami firiji, babbar talabijin, in ya yiwu su sai mota ko babur. Ga yawancin su addini ba shine kan gaba ba. Ana amfani da shi don samun hanyar cin abinci ne.

A kullum, musulmai masu sassaucin ra’ayi sukan nuna suna bin addini don wanda baya rayuwa bisa ga al’adar Kur’ani ba ba zai dade cikin sana’arsa ba. Yawanci sukan yi amfani da kalmomin musulmunci a bainin Jama’a kuma su goyi bayan sarakunan su. In mutum daya a cikin iyali ya zama Krista yakan kawo hargisti. Don darajar danginsu za’a ki jininsa, a nema a kashe shi ko a koreshi. Ba za a taba yarda wani rashin biyaya ga addinin musulunci ya bata sunan dangin su ba. Yawanci wadanda suke a irin wannan dangi basa yin sallah wani lokaci sukan zo ne don ganin ido. Da wuya sukan karanta Kur’ani. Musulmai da yawa sun nuna halin ko in kula a sha’anin addini. Irin wandannan yawansu ya kai 50-70 bisa dari na dukan al’uman musulmai. Wannan ya danganta ga yanki ko kasar da suke zaune.

Wani lokaci kishin kasa da na addinin musulunci kan hadu yadda daya na goyon bayan dayan. Amma dai bayan kasar ta zama ta musulmai, son abin duniya kan sami rinjaye. Aiki,abinci da iyali kan fi addini muhimmanci.

Musulmai masu karimci sun fi jaddada ayoyin kur’ani da na hadisi wadanda suna inganta rayuwar ‘yan adam. Hana cin wani irin nama, Jihadi, matsayin mata a Kur’ani da horo na rashin tausayi sun yi wasi da su akan cewa irin wadanan dokoki sun yi daidai ne da mutanen zamanin Muhammadu. Yau, a zamanin da aka cigaba, wadannan dokoki basu shafe mu ba. Musulmai masu sassaucin ra’ayi suna rayuwa da gurguwar addinin musulunci.

Yawancin gwamnatocin islama haka suke. Sukan danka wa limamai nawayar gudanar da shari’ar musulunci. Duka ka’idodin Jihadi ko horo suna hannun gwamnati. Sukan yi kokarin daidaitawa tsakanin shari’ar musulunci da ‘yancin ’yan Adam a duka duniya, kuma su yi gaba da musulmai masu tsatstsauran ra’ayi a kasarsu. Hare-haren yan ta’adda a Misrah ko Aljeriya ba wani abu bane illa yaki ne na nenam aiwatar da dukan shari’ar musulunci. Wannan shine musulmai masu sassaucin ra’ayi suna so su hana a gwamnatinsu Ko ta halin kaka.

2.14.3 -- Mata Musulmai

Rabin dokacin al’uman musulmai matane! Kada muyi tunanin maza kadai in muna magana akan musulmai. Mata suna taka muhimmiyar rawa a addinin musulunci. Suna da tasiri a bisa ‘ya ‘ya a iyalinsu fiye da mazajensu.

Ko ta yaya, an rubuta wannan a Kur’ani cewa namiji ba zai zama kamar mace ba (sra Al’imran 3:36)

Wannan gaskiyar a islama na da kakkarfan tushe. An rubuta a kur’ani cewa: maza masu tsayuwa ne a kan mata, saboda abinda Allah ya fifita sashensu da shi akan sashe, kuma saboda abinda suka ciyar daga dukiyoyinsu” (Sura al-Nisa 4:34.)

A kotu, shaidar mata biyu ne ke daidai da na namiji daya (sura al- Bagara 2:282). A rabon gado, mace tana samun rabin abinda namiji kan samu ko rabin na danta, yar’uwa na samun rabin na dan uwanta,yarinya na samun rabin na yaro (sura al-Nisa 4:11, 176). A shar’ance, mace tana da rabin darajar namiji ne.An yardam ma na miji ya auri mata hudu (Suraal-Nisa 4:3) in zai iya kaunar dukansu daidai. Da shike yawanci maza basu da arzikin daza su rike mata hudu da yaransu ba, shiya sa suna auren mata daya-daya. Amma dai matan da aka tara a kalkashin mutum daya sukan sha wahala wajen kishi, bakinciki da talauci fiye da yadda muke zato.

A iyalin musulmai, namiji na da daman ya ilimantar da matarsa, in tana tawaye yayi mata huduba, in ta cigaba sai ya ki shiga dakinta, in bata daddara ba, yana da daman yayi mata duka har sai tayi biyaya (Sura al- Nisa 4:34), amma ba a yarda ya karya mata kasusuwa ba.

A cewar kur’ani (ba a cikin dokokin Turkiyya, Misrah ko Tunisiya da wadansu kasashen musulmai ba). Namiji yana da dama ya saki matarsa a kan kowane dalili. Bayan iddarta na wata uku ko hudu,zai iya auren ta kuma, ya sake ta ya kuma sake aurenta. Bayan ya sake ta na uku, dole ne sai ta auri wani, bayan ya sake ta kana wanda ya fara aurenta ya sake dawowa da ita.(sura al- Bagara 2:229-230). Cigaba da shan wahalan mata a wadansu kasashen musulunci na da zurfi fiye da yadda muke tunani. Wanene Allah ya kirashi ya kai wa matan musulmai bisharar ’yanci akan cikakken gafartawa da baiwar Ruhu Mai Tsaki?.

Krista maza kada suyi magana da matan musulmai su kadai sai in mazansu na wurin. Saboda haka, yakamata matan Krista su dauki nawayan kai wa mata da ‘yan matan musulmai bishara suna shaida dandanawarsu cikin Almasihu. Matan musulmai ne ke tarbiyyar da yaransu. Don haka bishara a cikin matan musulmai na taka muhimmiyar rawa a bishara tsakanin musulmai a kowane lokaci. Shiri na talabijin don mata da litattafai don mata wanda uwaye cikin Kristi suka rubuta babbar bukata ce. A shekarun baya mata da ‘yan matan musulmai, kasa da 25 bisadari na yawan sune ke zuwa makaranta. Yau sun karu har sun kai tsakanin 40 zuwa 70 bisa dari. Wanene ya gane cewa wannan dama ce don bishara a tsakaninsu?.

Matan musulmai a wani lokaci sun fi mazansu rike addini da tsoron Allah. An ce Muhammadu ya taba ganin gidan wutan lahira, ya kuma ga 90 bisa darin wandanda suke ciki matane saboda suna kin biyaya da mazajensu. Mohammadu kuma yace yaga aljana amma 10 bisa dari ne mata don maza kalila ne suka yi shaidar cewa matansu suna yi musu biyaya. Irin wannan bambanci yakan iza matan musulumai su rike addinin musulunci fiye da mazansu saboda su sami daman shiga aljanna.

Wanene zai nuna wa matan musulumai jinkai, kuma cikin aminci ya nemi hanyar cetonsu daga wahala ta duniya da ta lahira cikin sunan Yesu.

2.14.4 -- Matasa Masulmai

Rabin dukan musulumai matasa ne wadanda shekarunsu basu kai 18 ba. A wadansu kasashen musulumai, rabi basu kai 16 ba. Wanda yana da dandanawa a bishara tsakanin matasa ya san wannan. Matasa na bukatar shiri daban da na manya. Wannan ganewa na bukatar sake tunani da gyara dabarun aikin bishara da adu’a.

Matasa a duka duniya na kaunan kwallon kafa da wasar gudu a mota. Duk wanda yayi tafiya zuwa kasashen musulumai, zai iya tambaya game da Beckenbaver,Rummenigge da Schumacher. Becker da Graf sanannun sunaye ne a tsakanin matasa musulmai.

Matasan musulmai suna koyon karatu da rubutu a yau. Suna neman litattafai da ke da sha’awan karatu. Sun kosa su sami sani . suna so su koyi kome. Sun yarda da kimiyya kuma suna tunanin zasu iya mamaye duniya in sun hazaka.zamu iya basu takarda , kasidu, mujillar da matasa zasu ji dadin karantawa, makarantar Litafi Mai Tsarki ta hanyar wasika zai iya sa matasa da yawa su yi bincikein Littafi Mai Tsarki.

Matasa da yawa basa neman gafaran zunubansu. Basa tunani game da tuba ko imani. Suna so su bincike kome. Yesu, Bulus da Yahaya suna basu sha’awa kamar Marx, Lenin da Mao. Wannan neman sani budaddiyar kofa ce ta kai bishara ba tare da matsala ba. Yawancin wadannan masu neman sani zasu tabu kuma su sami canji tawurin kaunar Yesu Kristi, tawali’unsa, kaskanta da kai da salama.

Matasa da suke manyan makarantu da jami’oi masu anfani da inji mai amfani da kwakwalwa suna kara yawa. Suna iya amfani da yanar gizo-gizo a wuraren shan iska da kuma gidajensu. Yawan kazanta,sabani tsakanin kungiyoyin musulmai da muzika na lalata ana samunsu ta wannan hanya. Amma wanda yana aiwatar da shirye-shirye na ruhaniya masu taimako don matasa zai sami masu karantawa har ma a kasashen musulmai. Babbar abin bukata shine kyakkyawar gwaji ko kwatantawa tsakanin bishara da islama da amsoshin tambayoyi masu wuya.

Kirkiro wakokin Krista masu kyau cikin maryar yarensu na cikin wannan aiki. Irin tsofaffin wakokin mutanen Jamus da Amerika basu da sha’awa ga matasa musulmai. In an gabatar da bishara cikin wakoki da muzika cikin al’adarsu, zaka ga sun fara kokarin yin wakar tun basu kama ba. Tsoron Allah mahalicci da mai shar’anta duniya bai rabu da tunanin musulmai ba duk da canji zamani.

Ba a taba samun dama ba na kai wa musulmai bishara kamar wanda aka samu a yau, domin matasa musulmai suna koyon karatu, rubutu da tunani kuma yawancin su suna da farincikin duban wadanda sun hazaka a filin wasanni da fasaha. An taba tambayar yar balarabiya daga Karkarar Hadramout, wanda yake a hamadar Rub al-Khali, wane irin waka kika fi jin dadin sauraro? Sai ta amsa “wakokin ABBA daga Sweden’’

2.14.5 -- Musulmai Masu Jin Takaici

Tunda Musulman Zamanin nan suna kokarin yin tunanin, yanzu sun fara yin tambayoyi akan al’ada da addininsu. Kumamancin addinin musulunci yanzu ba boyayyen abu bane gare su.

Wadansu musulmai da suka damu sukan yi tambaya, ‘Me Yasa Sojojin larabawa wandanda yawansu ya kai miliyan 250 ba su iya cin nasara da sojojin Israila a shakara 50 da suka wuce wadanda yawansu bai fi miliyan biyar ba?

Wadansu sun ce “Kalma Islama na da ma’anoni mai kyau. Daya daga cikinsu shine: Kawo Salama! Me yasa rabin yake-yake a duniya na da alaka da kasashen musulmai? Me yasa abubawan da muke aikawa a kasashen waje sune ta’addanci, yakin basasa, zubadda jinni amma ba salama da kawo ginuwa ba?

Wadansu sun furta cewa, ‘kasashen musulunci masu arzikin mai suna cikin kasashen mafi arziki a duniya! Amma sama da kasashe goma na musulunci suna cikin kasashen mafi talauci a duniya. Me yasa masu arzikin basa taimakawa wadanda suna cikin talauci? in ma anyi taimako, me yasa manyan da ke gwamnati ne kadai sukan cin moriyarsa, talakawa basa samun kome?

Direban wani attajirin sarki a saudiyya mutummin Indiya an tambaye shi ko ya zama cikakken musulmi a shekaru goma sha daya wanda yayi yana tuka daya daga cikin manyan masu tsaron wurare ma fi tsarki? Direban ya zabura ya ce “yi shiru! Bana so in ji wani abu game da addinin musulunci! Ba na sake son wani abu ya hada ni da shi. In ka san abinda suke furtawa, suna sha da abinda suke yi sa’anda suke su kadai bazaka gaskanta ni ba” lokocin da aka tambaye shi cewa menene wannan ganewa akan Islama ya jawo masa? Ya amsa, “zan yi bincike akan kwaminisanci da addinin Krista, in gwada su in ga wanda ya fi mini amfani a rayuwata . shi ne zan bi

Wani wanda ya gama digiri a fanni Islama a Jamiar AL-Azhar a Alkahira yaso ya gogu a lafazin larabci a tsakanin larabawan Saudiyya. Ya koyar da darasin litattafan musulumci a Jami’ar Riyad. Yawanci daliban sun soke shi don yana kawo tunani irin na zamani a koyarwarsa, kuma a maimakon sa farin jallabiyya, yana sa tufa irin ta turawa. Lokacin da gabar tayi yawa har dalibai sun jejjefeshi da duwatsu lokocin koyarwa, ya fusata, ya gudu daga dakin karatun, ya gudu zuwa gida ya dauki Kur’ani yana karatu da karfi don ya huce. Nan da nan ya tsaya, ya yi shaida daga bisani “a wannan lokaci na gane cewa wannan littafi ne yayi aiki a kwakwalwan musulmai ya hana su yin tunani da rayuwa mai kyau”. Ya dauki Kur’anin ya yayyage shi cikin fushi, ya tafi bayan gida yayi kokarin kona shi.

Wadansu malamai wadanda suka ji rufe kofar da karatunsa da karfi, sun zo su bashi hakuri. Amma dukansu sun zo sun tsaya shiru, sun gigiye suna, kallon Kur’ranin da yake cin wuta. Kowa ya sani cewa wanda ya aika wannan laifi, shi ma kona shi za a yi. Ba wanda ya ce uffan. Malami ya dawo cikin hankalinsa, ya gudu ya shiga dakinsa, ya gudu zuwa filin jirgin sama kafin tarkon nan na mutuwa ya kamashi.

Mutanen nan basu da wata alaka da Krista. Sun gane kumamancin Islama da koma bayan kasashensu kuma suna kokarin samun ’yanci a ruhunsu. Dalibai masu koyon aikin likita, ’ya’yan sarakuna, malamai da sauran musulmai sun gane sabanin da ke cikin Kur’ani suna kuma neman amsoshi da tunanin da zai fi inganta rayuwansu. Mu yi adu’a don mu hadu da musulmai masu jin takaici kafin su fada hannun kungiyoyin da zasu baudar dasu. Watakila kimanin kashi biyar bisa dari na duka musulmai addininsu baya iya biyan bukatarsu ta ruhaniya, suna neman wani ya basu haske.

2.14.6 -- Wadanda Basu Yarda da Allah ba a Chikin Musulmai

An taba tambayan wani tauraro a sha’anin finafinai na musulunci cewa, wane addinin yake bi. Ya amsa, ‘ addini mafi kyau a duniya wato musulunci! (sura Al’Imran 3:19, 110; al-Fath 48:28; al-Saff 61:9; da sauransu).

An cigaba da tambayarsa ko yayi imani da kasancewar Allah, ya ce, “A a! Irin wannan bangaskiya na tsofaffi mutane ne kafin su mutu da kuma kananan yara, amma mu muna cikin zamanin da muke yin wasa”. Dan jarida ya yi mamaki ya kuma yi tambaya yace, idan an kai wa musulmai hari, me zai yi? Ya amsa nan danan “zan zama na farko da zan dauki makami in kare addinin musulunci”. Har yanzu ya dauki kansa a matsayi musulmi ko da shike bai yi imani akwai Allah ba, baya kuma sallah! Islama ba addinin ne kawai ba, amma al’ada ce, gwamnatice, al’umma ce.

Lokacin wata lacca akan dangantakan musulunci da addinin Krista, wani matashi daga Turkiyya ya tashi yana hamayya da mai magana: musulunci ya fi kyau, ya fi kula da hakkin mutane, za a fi danganta shi da rayuwan zamani fiye da yadda ya ji a laccan. Sa’anda aka kira wannan matashi don ya bayyana ra’ayinsa a gaban masu sauraro, da ya fara magana sai malamin ya gano tushensa ya kuma katse masa hanzari da tambaya, “a cikin rayuwarka ka taba bude Kur’ani ka karanta? Yace “ A a”. lokocin da aka tambaye shi ko sau nawa yake zuwa masallaci yayi sallah sai ya ce bai taba yin sallah ba! Amma ya kare addininsa da duk karfinsa. Islama ba Kur’ani da sallah bane. Yana daya daga musulmai na zamani wadanda sun baude daga imani amma suna kare musulunci da su ma basu gane shi ba.

Likita Nasri daga Bengali ta yi kira da ayi gyare-gyare a Kur’ani dangane da matsayin mata da zaluncin da ake yi wa kananan mata a gidan aure. Tilas ta gudu zuwa Sweden domin maza musulmai suna kishin matsayinsu- kuma don tayi wa Kur’ani tuhuma! Wannan likita har yanzu tana daukan kanta a musulma ko da shike tana shakkar gaskiyar Kur’ani tawurin dandanawar ta.

‘Yan siyasa musulmai da wadanda suka gama jami’a kuma sun yi rayuwa a kasashen ketare wani lokaci sukan fi sukan addinin musulnci. Suna da bukata a rayuwansu kuma suna da shakka akan imaninsu ga Allah. Don iyalinsu ne sukan yi Sallah in sun dawo gida. A fili sukan yi azumin watan Ramadan su bada zaka. A cikin zuciya sun yi nesa da shariar musulunci sun shiga neman sabon dandanawa a zamanin duniyar wata. An tabbatar da cigaban magabtaka da musulunci na ra’ayin mazanjiya tawurin saduwa da masu ilimin kimiyya, fasaha da manyan mutane daga kasashen gabas da yamma, tunda sun gane cewa yawanci wadannan mutane ba musulmai bane amma suna rayuwa mai daraja.

Musulmai wadanda basu yarda da sallah ba kalilan ne, kimanin daya bisa dari, za’a iya samun yawancinsu a kasashen da suke da gwamnatin kwaminisanci. Za a iya gane su Kaman ‘yan soshalis a Turkiyyaa, tawurin kawo suka ga Muhammadu da islama a mujallu da litattafai.

2.14.7 -- ’Yan Sufi A Islama

Sakamakon rashin biyan bukata ta Ruhaniya a addinin musulunci ya haifar da musulmai masu tsatstsauran ra’ayi da wadanda a boye basu yarda da Allah ba. Wannan na kawo rashin biyan bukata, takaici da neman sabobin hanyoyi masu ma’ana. Daya daga cikin wannan al’amari za’a iya gani a sufi na islama. Sun juya wa shari’u da dokokin islama baya. Wadannan manema gaskiya a dandanawar addini sun ware kansu daga aikatawa a masallaci abuwan da suka gada daga kakanni, yin tsarki, maimaita addu’oi. Sun bar kafaffen addinin islama, sun hada kansu a kungiya- kungiya don su iya kirkiro wa kansu hanya da son addini daga Kur’ani da wadansu littattafai wandanda ba na musulunci ba.

Zaka iya samun mabiya sufi da darikunsu a Moroko, Sudan, Turkiyya da Fakistan. Harma a Sin da Indonesiya musulunci ya rabu zuwa ‘yan sufi da masu son shari'a. A Moroko mutun zai iya ganin fararen karburbura na waliyai akan tuddai ko bakin hanya. Mata wadanda basa haihuwa kan goga cikinsu a bisa kabarin waliyyi saboda su iya daukan ciki. A Sudan masu zikiri sukan yi tsalle, suyi birgima a kasa don nuna yadda suke kaunar Allah da ruhaniya.

A Misrah, ‘yan sufi wani lokaci sukan zauna ko su tsaya a da’ira suna maimaita sunan Allah ko lakabinsa, kamar; “Huwa, Huwa, Huwa… “(wanda a larabci na nufi,” shi, shi, shi..”) Sau da yawa har sai in waninsu ya shiga cikin wahayi ko ya fara furta bakin harsuna. A Turkiyya, dalibi na irin wadannan kungiyoyi ya ce, “Ana koya mana yadda zamu kira ruhohi da yadda zamu sallamesu in sun gama yi mana hidima.” Wata yarinya ta yi shaida cewa shaidan yakan ziyarce ta kowace Juma’a. abokai sun ce mata mafalki take yi amma ta yi bayani cewa lokacin da take karamar yarinya, ubanta ya taba daukanta a rashin lafiya zuwa ga shehun sufi wanda ya warkar da ita da wani iko na ruhaniya. Tun daga nan kowane mako shaidan na damunta da ziyara.

A Fakistan, kungiya kan taru suna zulumi tare,bayan dayansu ya zama Krista, uban mutumin da ya tuba ya kawo wani malami don ya dawo da dansa da yayi ridda. Amma malami ya cusa ra’ayin yin jima’i a cikin dan nasa, uban ya kori malamin don irin wannan abin kyama ne.

A Indonesiya, mabiya addinin Hindu da yawanci ruhohinsu, suna hade da na sufi na islama. Lokacin biki a karkara, kabilu sukan sake rahohi wadanda sukan yi fada da juna a iska a fili, sukan hadiye karafuna, kusoshi, fitilar lantarki kuma su narkadda su. A kan ji muryoyin maza a cikin mata, na mata kuma a cikin maza.

’Yan sufi sukan yi kokari su sa Allah ya shiga ya zauna a cikinsu, ya cikasu da bayyanuwarsa. Wadansu da kansu sukan yi kokarin shiga cikin Allah tawurin tunaninsu. Kashi na uku suna kokarin shiga duniya ta Mala’iku da Aljannu na Allah. Suna daddaure cikin kangin kungiyoyin asirai a matakai daban-daban.

Tun da shike Allah a cikin islama yana nesa da halittunsa, babu wanda zai yi tunanin musulunci na kirki da zai yi kokarin gina wannan gada tawurin ayukan addini. A rashin sa a, ruhohin da ke gaba da addinin Krista kan shiga wannan wuri. Yawan ’yan sufi na karuwa ne. a wadansu kasashe sun kai kashi 10 zuwa 20 bisa darin na yawan musulmai a wannan kasa.

Wadansu masu Tauhidin Ikklesiyar Katolika sun ce ’yan sufi ne zasu iya zama gada mafi kyau tsakani addinin Krista da islama. Ko ta ya ya sun manta cewa ’yan sufi sun gaskanta adalci na kansu kuma basa tunanin suna da bukatar tuba. Dan Allah giciyayye har yanzu ya zama sanadin tuntube garesu. Aikin kirkin da suke yi ya rabasu da ceton Yesu wanda a ka kamala domin mu da su.

2.14.8 -- Masu Ceto A Islama

’Yan sufi za’a misalta su da kura ce a tsakanin musulmai masu jin takaici. Musulmi dan ta’adda za’a iya kiransa shaho a tsakaninsu. Sukan yi gunagunin cewa, “Duk sallah, azumi da biyan zaka duk aikin banza ne. Dole ne mu yi wani abu da kanmu. Dole ne mu sadakar da ranmu da jininmu saboda mu kau da zargi; daga musulunci mu kuma ci nasara da rashin gaskiya a cikin al’umman musulmai da karfi.

Hassan al-Banna, wanda ya kafa kungiyar Musulim Brazas ya koyas cewa Sallah da Azumi basu isa cikakken rayuwan musulmi ba. Ya kara da cewa musulmi na kwarai dole ya taurare zuciyarsa har sai in ya shirya ya kashe abokan gaban musulunci. Dokoki dari a Kur’ani na kiran musulmai su hada hannu a yakin jihadi wanda zai nuna imaninsu.

Musulim Brazas da gwamnati ta tsanansu sun rarrabu zuwa kungiyoyin ta’adda kasha hamsin. Ayatollah khomeini a bagaren ’yan shi’a ya dauki tutar Jihadi kuma ya aika da ’yan kunan- bakin wake zuwa kasashe da dama don kisa, Kaman masu kisa a zamanin Jihadin Krista wadanda sun sa duniya zaune tsaye.

Hisbollah, Hamas, da al-Djihad da sauran kungiyoyi suna horadda mabiyansu su kai hari irin ta kunar- bakin wake. Kur’ani ya bayyana cewa Allah da kansa zai rubuta bangaskiyar islama a zukatansu ya kuma karfafasu a cikin wannan manufa da ruhunsa (Sura al-mujadila 58:22). Wannan ita ce ayar da ke magana game da dangatakar musulmai da ruhu daga wurin Allah. Wadanda suka mutu cikin jihadi an yi musu alkawarin aljanna. Baqara 2:154; Al’mram 3:157-158, 161-171, 193-195; al-Nisa’ 4:74; Muhammad 47:4-6; d/s) Ba za muyi adalci ba in mun kira wadannan mayaka, wadanda suka mutu garin kisa, ‘yan ta’adda domin suna ganin kansu a masu ceta ne wadanda suka sadakar da ransu domin nasarar islama. An gaya musu cewa ba sune suke kisan abokan gaban islama ba, amma Allah ne da kansa. Shine yakan yi harbi a cikin harbinsu ya kashe abokan gaban islama (Sura at Anfal 8:17).

Wadansu ‘yan jarida da masu tausaya wajama’a suna kira irin wadannan ‘yan tsiraru cikin addinin alusulunci. Wadannan suna yin kuskure! Don wadannan ‘yan ceto sune suke biyaya da dokar Kur’ani, suna aikata abinda Allah ya Umurta ko ta yaya (Surorin al-Baqara 2:191-193; al-Anfal 8:39; al-Tauba 9:15; d/s).

Musulmai masu tausaya wa jama’a ana kiransu matsorata da masu cin amana inji Kur’ani. Akan nemi salama da wadanda ba musulmai ba, idan musulmai basu da isasshen kudi da kayan yaki. Ko wani yanayin da ya fi karfinsu.

Abinda ya faru a shekaru hamsin da suka wuce kewaye da Israila a yaki mara tsarki zai cika litattafai da yawa. Kame jirgin sama, jefa bomb a hotel, kona tankoki cikin harin 'yan kunar-bakin wake da sauransu.

Lokacin da aka kashe ‘yan yawon shakatawa na kasar Swis, an yanke gababuwan jikunansu, an yi wa matansu fyade kusa da kaburburan sarakuna a Luxor, ‘yan “Ceto” sun ce, “Allahu akbar” (Allah da girma yake). Haka kuma suka ce a Indonesiya lokacin da taron Jama’a suka kone Ikklesiyu suka yi wa ‘yanmatan kasar sin fyade. A tsibirin Mindanao a kasar Filifins Krista da dama sun mutu a yakin duniya na biyu. Haka ma dubban mutane sun mutu a Arewacin Nigeria don basu yarda a mallakesu da shari'ar musulunci ba.

A kasar Jamus, musulmai masu tsatstsauran ra’ayi 32,000 sun sami mafaka don Gwamnatocin kasashensu na musulunci na neman su ruwa a jallo. Gwannatin Jamus na sa musu ido. Kisa kamar wanda aka yi a lokacin wasan Olympic na 1972 a Munish zai iya faruwa. A cikin Kur’ani Allah ya kalubalanci duka musulmai masu biyaya da su kashe magabtan Islama (sura al-Baqara 2:1919-193; al-Nisa 4:39, 91, al-Tawba 9:5 d/s). a kai wa Yahudawa da Krista hari a cewar sura ta tuba (Sura al-Tawaha 9:28-29). Domin basu gaskanta Allah na gaskiya ba, basa bin sharia kuma addininsu ba gaskiya bane. Islama a cewar Kur’ani, ruhu ne mai hallakaswa.

2.15 -- A Takaice

Duk wanda zai kai wa musulmai bishara, dole yayi la’akari da cewa ba duk musulmi ne ke tunani kamar dan’uwansa ba. Duk wanda zai yi musu hidima dole ne ya fara sauraron su kuma ya tambayesu inda suka fito, abinda suke tunani game da siyasa, addini da rayuwarsu nan gaba.

Duk wanda bashi da hikima a irin wannan zance ya roki Yesu don yayi masa jagora ya sami irin musulmai wadanda Ruhu Mai Tsarki ya riga ya shirya zukatansu. Kauna ta aminci ta zama yaren da kowane mutum a duniya yake ganewa. Duk wanda ya taimaki baki don warware matsalolinsu da hukuma zai iya jagorantar su yadda zasu girmama su kuma gane Kristi.

Kada muyi tsoron ruhun islama, domin albarkar Yesu Kristi ya fi la’anar Mahammadu iko “Wanda yana cikinku ya fi wanda yake cikin duniya karfi” (I Yahaya 4:4). Mu rika yin kyakkyawan shiri in zamu yi Magana da Musulmai. Akwai kungiyoyin da suna shirye so goyi bayan wadanda zasu yi aiki da litattafai da horaswa.

Zaka iya samun amsoshin da zasu taimakeka a aikinka cikin kungiyoyin Musulmai a cikin Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali, Kur’ani, wadansu Litattafai da dandanawar ka ubangiji zai iya bude kofa zuwa cikin zuciyar Musulmi kuma ya baka Kalmar da ta dace a lokacin da ya dace tawurin jagorar Ruhu Mai Tsarki.

RAI MADAWWAMI KUWA, SHINE SU SANKA,
ALLAH MAKADAU NA GASKIYA, DA KUMA YESU
ALMASIHU DA KA AIKO.

YAHAYA 17:3

2.16 -- Tambayoyi

In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan

Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.

Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.

  1. Wadanne addinai uku ne suka gabaci addinin Islama kuma ta albarkarsu aka kafa ta?
  2. Yaya dangantakar Yahudawa da Krista a kasar Larabawa, Musamman Yemen?
  3. Wace ma’anan wannan furci daga Kur’ani “Mutanen Litattafai” ke da shi ga Muhammadu?
  4. Wanene Muhammadu ya dauka shine Musulmai na farko?
  5. Me ya sa Muhammadu ya dauki Musa ya zama abin koyi gareshi ba Yesu ba?
  6. Me ya sa Muhammadu ya furta cewa Yahudawa sune abokan gaba mafiya hatsari ga Musulmai? Ta yaya ya ci nasara dasu?
  7. Wannene a cikin manyan Ikklesiyu uku da suke da mabiya a duka duniya da ke da kakkarfan tasiri a bayyanuwar Islama?
  8. Wane irin hoto ne Ikklesiyar Otodoks ta sa a zukatan Musulmai kuma me yasa za a iya kiranta “Ikklesiyar da ke shan tsanani na tsawon shekaru 1370”?.
  9. Me yasa musulmai da yawa sun dauki Ikklesiyar Katolika ta zama Ikklesiyar da take yaki? Ta yaya zaka bayyana wannan a tarihi?.
  10. Me yasa babu albarkacin Ikklesiyoyin Furotesta a kafa Islama? Me yasa Musulmai suna tuhumar Krista da ke Ikklesiyoyin bishara (Ebanjelika)?
  11. Ikklesiyoyin Krista masu zaman kansu guda nawa ne a duniya yau kuma menene ya hada su sun zama daya?
  12. Menene ke bambanta duka Krista daga Musulmai?
  13. Su wanene ‘yan Sunna kuma menene yawan su ,bisa dari na dukan al’umman Musulmai.
  14. Su wanene ‘yan Shia, mabiya nawa ne a cikin wannnan kungiyar?
  15. Wane Shekara ne mataki na uku na yada Musulunci a duniya ya fara? Menene ya iza wannan kuma menene manufarta?
  16. Me yasa kowane Musulmi ya sha bambam da dan’uwnsa Musulmi? Ta yaya zamu iya gane abinda ke damunsu, tunaninsu, bangaskiyarsu da abinda zasu iya yi?
  17. Wadanne halaye ne na musamman zamu iya gani a cikin musulmai masu ra’ayin mazan jiya da masu tsatstsauran ra’ayi kuma ina yawan musulmai da suke bin ka’idodinsu?
  18. Tayaya zamu iya kusantar musulmai masu tsatstsauran ra’ayi kuma me ya sa?
  19. Musulmai nawa ne masu sassaucin ra’ayi kuma wace irin rayuwa suke yi?
  20. Me yasa akwai gaba kuma har ma da yakin basasa a tsakanin kungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi da gwamnatin musulmai masu sassaucin ra’ayi?
  21. Wace shawara ce ma’aikatan ubangiji zasu dauka idan sun ga rabin duka musulmai mata ne? Wanene zai iya kai musu bishara?
  22. Wadanne irin matsaloli ne mata suke fuskanta a cikin addinin musulunci?
  23. Wane irin kalubale ne zai fuskanci ma’aikacin ubangiji in ya ga cewa rabin al’umman musulmai suna kasa da Shekaru 18 a wadansu kasashen musulmai ma suna kasa da Shekara 16?
  24. Ta yaya zamu iya ,kai wa majiya karfi da matasa a kasashen musulmai bishara?
  25. Ta yaya zamu fuskanci wannan gaskiya da muhimmanci cewa kashi biyar bisa dari na yawan al’amman musulmai suna cikin takaici game da addinin musulunci? Bada dalilan da ke kawo musu takaici? Ta yaya zamu iya samunsu?
  26. Me yasa wadansu mutane basu yarda da Allah ba amma suna Kiran kansu musulmai? Islama addini ne ko ya fi haka?
  27. Wadanne dalilai ne suka sa musulmai kashi 10 – 20 bisa dari na duka musulmai suka zama ‘yan sufi? Ta yaya suka sha bambam da sauran musulmai? Menene suke kokarin tabbatarwa.
  28. Wadanne abubuwa ne masu kyau da suka isa yabo na ‘yan sufi a Islama? Menene ke hanasu karban Yesu ya zama mai cetonsu?
  29. Me yasa ‘yan ta’adda musulmai suna kiran kansu “Masu ceto”? Me yasa zasu ce su kadai ne musulmai na kwarai?
  30. Menene irin wadannan “masu ceto” ke begen samu in sun sadakar da ransu har ga mutuwa a fada ko yaki.
  31. Menene babbar manufar wannan ‘yar Littafi?
  32. Me yasa bai kamata mu ji tsoron kai wa musulmai bishara ba?
  33. Wadanne wurare ne guda biyar da zamu iya samun taimako da amsoshi idan muna zance da musulmai?

Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.

Naku cikin Hidimarsa

Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.

Ku aika da amsoshin ku zuwa:

The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.

Ko

GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY

Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on June 03, 2013, at 08:39 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)