Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 4 Titles of Christ
Previous booklet -- Next booklet
01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI
4 - Sunaye da lakabobi Na Kristi Chikinkur’ani da Baibul
4.01 -- Sunaye da lakabobi Na Kristi Chikinkur’ani da Baibul
Wandanda suna karanta Littafi Mai Tsarki zasu iya samun sunaye, lakabi da halaye 350 na Yesu a cikinsa. Wanda yana binckiken Kur’ani zai iya samun sunaye, lakabi da halaye 25 na Isa kamar amsa-kuwwar Islama ga bishara. Hanya daya da zai taimaka a matso kusa da musulmai shine a cika ma’anar sunayen Kristi a Baibul cikin lakabin dan maryama a bayyana wa musulmai cewa dan mutum shine Dan Allah Kamar yadda Yesu da kansa ya bayyana. In wani yana tsammani zai iya yin nasara ba tare da yin amfani da ma’anonin kalmomin Kur’ani ba yana hatsarin yi wa musulmai magana a bakon harshe.
4.02 -- Isa ko Yesu?
Isa, sunan Yesu a cikin musulunci ya bayyana sau 25 cikin Kur’ani. Kotayaya, Isa ba Yesu bane, domin an musanci Allahntakansa a littafin musulunci. Bai mutu a kan giciye ba a cewar Kur’ani. Ba wanda ya san tabbas, abinda ya sa Muhammadu ya zabi suna Isa ba a maimakon Yesu, tunda a harshen larabaci “ ana amfani da “Jasu’u a Litattafan Larabawa Krista a maimakon sunan Yesu.
Limaman Ikklesiyar Otodoks sun ce, kalma Isa an same shine daga lafazin mutanen Siriya in zasu kira suna Yesu a harshen Helenanci. Wadansu sun ce wai Muhammadu ya canza baki na farko da na karshe a sunan larabci “Jasu’u” sa’annan ya kirkiro sa daga cikinsa. A fadin wadansu al’adun mutanen Afirka wannan hanyace ta la’anta mutumin da ake magana akai. Kamus na “Lisan al-Arab” ya gabatar da matukar bayani tawurin bude tushen kalma isa (Ais) wanda yana nufin “Maniyin ingarma” wanda yake da dafi wanda kan yi kisa a nan take.
Yawancin Krista larabawa basa amfani da suna Isa a lokacin da suke zance da musulmai, sa’annan mishanarai daga ketare sun dage cewa da wuya musulmai su iya ganewa idan ana magana akan Yesu. Saboda haka sukan yi kokarin cika ma’anar sunan Yesu daga Baibul sunan Isa na Kur’ani.
Sai mu tuna cewa a Sabon Alkawali, su nan Yesu ya bayyana sau 975. wannan shine sunan da ya fi Muhaimmanci bisa duka sunaye da lakabi na Dan Allah, ku ma wanda aka fi amfani da shi. Zai zama abin sha’awa ga musulmai cewa sunan “Yesu” da aka ba wa dan Maryama an bayyana shine tawurin wahayi kashi biyu, na daya an bai wa Yusufu wanda yana da hakin tarbiyyad da shi (Matiyu 1:21), na biyu kuma ga uwarsa ta hannun mala’ika Jibra’ilu (Luka 1;31; 2:21). Mala’ikan ya bayyana ma’anar wannan suna na musamman wanda aka zaba kafin a halicci duniya: “za shi ceci mutanensa daga zunubansu’ (Matiyu 1:21).
Wadanda suka iya harshen Ibrananci zasu iya samun tushen sunan Yesu (Yod-shin-ayin) wanda an rubuta shi sau 281 a Tsohon Alkawali dangane da sunan Allah “Yahweh”; sau 68 a isimin da ke magana akan ceto da taimakon Yahweh, kuma sau 213 a fi’ili inda Yahweh da kansa ke aikin ceto. Ta haka, ma’ana da manufan sunan Yesu an kaddara su tun kafin halitta, kamar yadda wani marubucin wakar kristimati ya rubuta “An haifi firist mai ceto”
Kalma ceto (sotar) a Helenanci ba yana nufin mai ceto daga wahalun duniya ko hukumcin Allah ba kadai. A da lakabi ne na girmamawa ga mai mulkin Roma wato Augustus wanda ake yabonsa da cewa shine tabbacin samun salama tunda ya kafa gwamnatinsa tawurin cin nasarar yaki.
Malaikan Allah Jibrailu yayi wa Yusufu bayani da cewa, babbar matsalar mutum shine zanubansa, yana raba shi da Allah, saboda haka Yesu dan rago na Allah, ya dauke zunubin duniya kuma ya sulhunta mu da Allah tawurin kafarar da dokar idin ketarewa tawurin mutuwarsa a maimakon mu. Jininsa shine kudin fansa wanda ya biya domin samun cetonmu daga zunubi, shaidan da fushin Allah (Sura al-Saffat 37:107).
Musulmai basu san ikon da ke cikin sunan Yesu ba. Mu yi adu’a Allah ya bamu hikima da jagora na Ruhu Mai Tsarki a cikin yin magana da musulmai saboda mu iya nuna musu ma’anar sunar Yesu, saboda a tilasta shaidan ya sake ‘yan kurkukunsa cikin Islama su sami ‘yanci, su kuma karbi gafaran zunubansu da godiya. Domin Yesu ya kamala aikin ceto domin su (Yahaya 19:30). bari mu kaunaci Yesu, saboda musulmai su ganshi cikin kumamanci mu.
4.03 -- Kristi Shafaffe
Lakabin Hidima na Yesu a Baibul shine; shafaffe wanda ake nufi Almasihu ko Kristi. An rubuta wannan lakabi sau 569 a Sabon Alkawali da kuma sau shadaya a Kur’ani. An samo kalmar larabci “al-Masih” daga wannan ma’ana “a goge” da kuma “a shafe’’. Duk da ma’anar wannan kalma, yana da wuya musulmi ya sani cewa al-Masih na nufin “shafaffe”.
Zamu iya yin kokarin yi musu bayani cewa a Tsohon Alkawali, sarakuna, firistoci da annabawa akan shafe su da mai wanda aka tsarkake don ya zama alama cewa Ubangijin alkawalin ya basu iko tawurin Ruhun sa Mai Tsarki domin nawayar da aka danka musu. Yesu da kansa ya bayyana wannan lakabinsa na daraja a Nazarat “Ruhun Ubangiji na tare da ni, domin ya shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aikoni in yi shelar saki ga daurarru” ( Luka 4:18-19).
Babu wanda zai iya bayyana wannan lakabin “Kristi” fiye da shi kansa. Ya bayyana a takaice dayantakan Trinity Mai Tsarki kamar haka “Ubangiji, Ruhu da shi Kansa”. Ya kuma bayyana cewa shafewan Ruhu Mai Tsarki yana da manufa ta Musamman: yayi shehar bishara ga” matalauta”, saboda a gyara zukatansu da suka kakkarye.
Littafi Mai Tsarki ya bayana cewa Yesu Kristi sarkin sarakuna ne, Babban firist Madawwami kuma kalmar Allah ne cikin jiki. Shine Ubangiji kaman yadda Sabon Alkawali ya tabbatar mana sau 216! Yana da duka iko da sarauta a sama da kasa. Lakabin “Ubangiji” da aka ba wa Yesu baya cikin Kur’ani. Muhammadu ya dage cewa musulmai ba za su taba karbar mutum a matsayin Ubangiji ba. An musanci Allahntakansa gaba daya (Surorin Al’Imran 3:64; al-Ma’ida 5:17, 31; al-tawba 9:30, 31 d/s) musulmai suna ganin sa a Ubangiji a cikin biyayyar mu ta bangaskiya?
Wandannan sunaye da lakabobi guda uku: Yesu, Kristi, Ubangiji, gaba daya sun dauki kashi 65 bisa dari na duka wuraren da sunansa ya bayyana a Baibul. Duk wanda ya gane muhimmancin wadannan sunaye guda uku na Dan Allah, ya bada gaskiya ya kuma furta su, ya zama Krista. In haka ya faru, shima yana da dama ya maimaita shaidar Yesu a Luka 4:18.
4.04 -- Kristi – Dan Sakon Allah ne?
Muhammadu ya yarda da aikin Isa a tsakanin jama’a kuma ya kirashi jakadan Allah sau biyar (Sura Al’Imran 3:49; al-Nisa 4:157, 171; al-Ma’ida 5:75; al-saff 61:6). Ya kuma ambace shi sau da yawa tare da sauran annabawan Allah (Sura al-Baqara 2:87; 253; al-Hadid 57:27).
Ma’aikin Allah ya fi annabi girma a Kur’ani Annabi yana da nawayan shelar wahayin Allah yadda aka saukar masa. Ma’aiki yana da Karin aiki bisa annabci. Shine mai tabbatar da an bi dokokin Allah. A cikin kalmar shahada, musulmai sukan furta cewa Muhammadu ma’aikin Allah ne ba ananabi kadai ba. Musa shi ya zama misali ga Muhammadu. Musa matsakanci ne tsakanin Yahweh da mutanensa wanda ya shugabance su a matsayin mai kafa doka da Alkali. Muhammadu ya gama kansa da Isa dan Maryama da irin ikon da aka ba Musa.
Wata kila Muhammadu ya ji a wajen Krista na Makkah da Madina cewa Yesu yayi zancen mulkin Allah, Mulkin sama a cikin Linjila. Yesu yayi magana akan mulkin wajen sau 100, amma yayi magana akan Ikklesiya sau uku kacal. Muhammadu ya zaci Kristi ya zo a matsayin ma’aikin Allah saboda ya kafa mulkinsa da karfi. Kalma “mulki” da larabci ya sami asali daga mallaka (mulk) kuma yana nufi “mahalicci ne ma mallakin duka abinda ya halitta” (sura al-An’am 6:75; al-A’raf 7:185; al-Mu’minun 23:88; Yasin 36:83). Kristi ya zo don karbe mallakar Ubangiji daga hannun Israilawa (Matiyu 21:33-46).
Muhammadu bai sani cewa bayan giciye Yesu, tashinsa zuwa sama da zubowar Ruhu Mai Tsarki a bisa mabiyansa ya canza wa’azin manzannin Yesu. A cikin ayukan manzanni da wasiku, mazannin sun yi magana akan Ikklesiya ninkin yadda suka yi magana akan mulkin! Daga wannan lokaci kan maganar ceto ya koma akan “wadanda aka kira” daga Israila da sauran al’umman duniya. Ko ta yaya burinsa na dawo da duka halitta gareshi bai tsaya akan gina Ikklesiya ba kadai. Yesu da kansa ya aike mutanensa kirayayyu da su je cikin duniya duka su ribato duk wadanda zasu ji muryarsa.
Ko da shike muhammadu ya gane aikin Yesu a fuskar addini, karfin soja da siyasa, bai ji abinda Yesu ya ce ba: “mulki na ba na duniyan nan ba ne… ni sarki ne. domin haka musamman aka haifeni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya yakan saurari muryata” (Yahaya 18:36-37).
Muhammadu baya cikin gaskiya. Baya so ya mika wuya ga Yesu Ubangiji shi yasa ya kamanta Isa kaman shugabane na addini da siyasa a manzon Allah kamansa!
Yesu kuwa bai jinkirta kiran kansa aikakke ba sau da dama a cewar Bishara daga hannun Yahaya, amma ya nanata cewa “Ubansa” ne ya aikoshi ba wani Allahn da bai damu da kowa ba. A wannan hanya ya bayyana mana cewa shi dan Allah ne da duka ikonsa: “Rai madawwami kuwa, shine su sanka, Allah makadaici na gaskiya, da kuma Yesu almasihu da ka aiko” (Yahaya 17:3) “Kamar yadda uba ya aikoni, haka ni ma na aike ku” (Yahaya 20:21).
4.05 -- Kristi Dan Maryama
Muhammadu ya rude yayin da ya ga cewa Budurwar da bata san namiji bane ta haifi Yesu – babu uba. Ya yarda da wannan abin mamaki kuma ya kirashi Isa dan Mayama sau 23 a Kur’ani. Yayi kokarin baratadda Maryama tawurin tabbatarda cewa ba cikin shege tayi ba (Sura Al’imran 3:45-47; Maryam 19:16-23 d/s). Muhammadu ya ce Jibra’ilu ne ya lumfasa (hura) ruhun Allah a cikin Maryama (Sura al-Hajj 21:91; al-Tahrim 66;12). Tawurin wannan bayani Muhammadu ya zo kusa da bishara amma ya kasa a furcinsa na barin Jibra’ilu ya fadi cewa ba a haifi Isa tawurin Ruhun Allah a cikin Maryama ba amma an halicce shi ne, ta haka ya sha bambam da shaidar bangaskiyar Krista wanda duka Ikklesiya ke furtawa:
Firist Allah ne daga Allah.
Haske daga haske.
Allah na gaskiya daga Allah na gaskiya,
an haifeshi ne ba halittarsa aka yi ba
shi daya ne da Uba.
Muhammadu ya zama magabcin Kristi tawurin musun Allahntakar Kristi (1 Yahaya 2:22-25; 4:1-5).
A Kur’ani an rubuta sau 17 cewa Isa ba dan Allah ba ne. Muhammadu ya ki tunanin aurayya tsakanin Allah da Maryama. Duka Krista ma sun ki irin wannan tunani. A kwai wata kungiyar Krista a kasar Larabawa a lokacin Muhammadu da ta kira Maryamu “Uwar Allah” sa’annan ta dauki Triniti Mai Tsarki a Allah Uba da Da da Uwa” (Sura al-maida 5:116). Wannan koyaswar karya ce Muhammadu ya ki. In mun tabbatar da wannan kiyayya akan karkatacciyar ganewa a kan haihuwar Kristi a zancen mu da musulmai, za a kara samun fahimtar juna.
Littafi Mai Tsarki yayi magana akan yadda Maryamu ta yi juna biyu tawurin Ruhu Mai Tsarki da shaida cewa” Allah Uba, Kalmarsa, da Ruhunsa” daya ne. Kiran Maryama “Uwar Allah” wanda Ikklesiyar Otodoks da ta Katolika suke yi bata da tushe a Littafi Mai Tsarki kuma yana sa zance da musulmai na zama da wahala.
An rubuta sau 59 a Baibul game da Dan Allah. Yesu kuma ya ambaci “NI NE” sau 50 cewa shine Ubangiji da ya bayana kansa ga Musa a dutsen Horeb (Fitowa 3;14) a “Nine wanda Na kasance”. A lokacin da aka gabatar da shi a gaban majalisar Yahudawa ya tabbatar musu da cewa shi dan Allah rayayye ne (Matiyu 26:63-68; Luka 22:70). Don ya fadi wannan ne aka yanke masa hukumcin kisa. Muhammadu yaki kuma yana nuna gaba da shaidar cewa Kristi “Dan Allah ne’ har ya kai ga la’anta duka Krista masu wannan shaida har da rokon Allah ya kashe su (Sura al-Tawba 9:30)!
A lokacin da yake a duniya, Yesu ya sani duk wanda ya kira kansa Dan Allah a Israila za a dauke shi a mai yin sabo. Saboda haka ya kira kansa “Dan mutum” sau 80 a cikin linjila. Yin amfani da wannan suna ya kai mu ga annabcin Annabi Daniyel 7:13-14, in da dan mutum” ya bayana a wahayin a matsayin dawwamamen sarki da mai sharia. Amma yawancin Yahudawa sun gane wannan suna a sama-sama ne suna tsammani Yesu ya dauki kansa a mutum ne kawai. Ko ta yaya, yacika wannan magana tasa da ikonsa na Allahntaka.
Rabin ayoyi game da Dan Mutum na nuna mutuntaka, tawali’u da kaskantarda kai na Kristi. “Don mutum bai zo domin a yi masa hidima ba, amma domin ya yi hidima, ya kuma badaransa fansa domin mutane da yawa”. (Matiyu 20:28).
Da wannan zance Yesu ya canza salon shugabnci. Babba zai zama karami domin sarkinmu da kansa ya bayyana kamar bawa ne, wanda zai bishi ba zai zama maigida ba sai dai bawa.
Daga rabin ayoyi akan Yesu Dan mutum na nuna daukakarsa da babbar ikonsa lokocinda zai dawo mai shariar duk bil adama: “Sa’anda dan mutum zai zo cikin daukakansa tare da duka mala’ikunsa tsarkaka, sa’annan zai zauna a kursiyinsa cikin daukaka ta sama. Duka al’ummai zasu taru a gabansa…” (Matiyu 25:31-32 d/s). Yesu ya kasance mutum ne na kwarai, an jarabce shi kamar mu, amma ba yayi zanubi ba (Ibraniyawa 2:17-18). A sakamakon haka ya iya tabuwa yana gane kowa zai yi masa sharia ta gaskiya.
Zai yi kyau in muna shirye mu koyi wannan hanya mai taimakawa wurin Yesu, wanda ya rufe Allahntakansa, kuma ya bayyana asirin bayyanuwarsa cikin jiki a kalmomin “Dan mutum” wannan suna shine daya daga cikin mabudi zuwa cikin zukatan Yahudawa da Larabawa. In kayi magana akan Dan Allah daga farkon zance da musulmi za ka ga yadda za a kulle maka kofofi. Amma in ka koya daga wurin Yesu zaka zama da hikima kuma baza ka musanci gaskiya ba. Maimakon haka zaka yi shaidar gaskiyar cikin kauna da hikima yadda masu sauraronka zasu iya ji.
4.06 -- Kristi – Kalmar Allah Cikin Jiki
Muhammadu ya tattara halaye, lakabobi, da sunaye na Kristi a kur’ani, saboda ya ja ra’ayin Krista zuwa musulunci. Yayi ta saka kalmomin Sabon Alkawali a cikin ayoyin sa saboda a yadda shi annabi ne na kwarai ya so ya ja ra’ayin Krista daga Abisiniya da wakilai daga Arewacin Yemen tawurin kwaikwayon bangaskiyarsu. Saboda haka muna da dama muyi amfani da magaganun da ya ara daga baibul, a dauke su daga kur’ani a mai da su a asalinsu cikin bishara wannan zai iya taimakon musulmai, wadanda suna neman gaskiya, su nemi hanya ta ceto cikin Kristi.
Daga bishara daga hannun Yahaya, sau hudu Muhammadu ya dauki wadannan kalmomi cewa Kristi “Kalmar Allah” ko “Kalmarsa” (Sura Al’imran 3:39, 45, 64; al-Nisa 4:171) malamai na musulnci daga bisani sun ga wadannan sunaye na Kristi suna da hatsari ga bangaskiyar Islama sai suka yi kokari suka ce wai Kristi wai halittaccen kalma ne na Allah, wannan bashi da ainihin kasancewar Allah madaukaki. A matsayin wanda ya halicci Kristi, da Allah zai ce ‘ka kasance, sa’annan ya kasance”. Haka kuma malamai na musulunci sunce Kur’ani. (Al’lmran 3:47) na da ainihin kasancewar Allah, nufinsa da ikonsa.
Muna da dama mu bayyana wa musulmai cewa duka ikon Allah na halitta da ke cikin kalmar Allah, ikonsa na warkaswa, ikon gafarta wa mutane zunubansu. Jinkansa mai kawo ta’aziya, ikon sabonta abu duka suna cikin Yesu. Cikin Kristi duka halaye na kamar Allah a bayyane suke. Nufin Allah, Hikiman Allah, fushin sa, kaunarsa, jinkansa, Hakurinsa, Duka abubuwan da Allah ya ce ayi, ko yayi alkawali ko kuma ya hana sun bayyana a jiki cikin Yesu. A cikin sa duka anabce-anabce na Allah sun zama tabbas duk wanda yake so ya gane nufin Allah dole ne ya dubi Yesu: shine bayyanuwa a cikin jiki na wanda Allah ke jin dadinsa. Ya ce: “Maganar da nake fada muku, ba domin kaina nake fada ba, Ubane da ke zaune cikina yake yin ayyukansa” (Yahaya 10:30).
Wani furci na musamman a Kur’ani game da bayyanuwar Yesu kalmar Allah cikin jiki, ya bayyana cewa Kristi ‘kalma ne na gaskiya”. Gaskiya da adalci anan sun bayyana halaye da sunanyen Allah, wanda ya sa ayar na nufin: Kristi furcin Allah ne cike da adalci da gaskiya (sura maryam 19:34). Ko ta yaya wadansu malamai masu sharhi sun karkatar da wannar zahiri sunce wadannan kalmomi basu da ma’ana don suna kalkashin wata jumla ce. Amma wannan ba gaskiya ba ne. Yesu ma shine bayyanuwar gaskiya da sharia a Kur’ani (Yahaya 14:6). Yesu yafi gaban annabi – shine kalmar Allah cikin jiki! Wadannan kalmomin zasu iya zama kayan yakinka masu karfi a aikin kai wa musalmai bishara.
4.07 -- Kristi – Ruhu Daga Allah
Wani furci kuma a Kur’ani na hamayya da matsayin musulmai masu suka akan Allahntakar Kristi domin an kira shi “Ruhu daga wurin Allah” (sura Al-Nisa 4;171). Wannan furci ya nuna cewa Kristi ba kamar sauran ‘yan adam bane Kaman su Musa da Muhammadu, amma Ruhun Allah ne wanda ya bayyana cikin jiki. A cewar Alkur’ani, Buwayi ya lumfasa kadan daga cikin ruhunsa cikin Maryama (sura al-Anbija 21:91; al-Tahrin 66:12). Don haka an dauki Isa ruhu ne mai tafiya cikin siffan mutum. Cikin jikinsa na ruhu, bayan rayuwarsa a duniya, ya koma wurin Allah. A Islama, Kristi ba mutum bane kamar sauran ‘yan adam, ba annabi ne kamar sauran annabawa ba amma ruhu ne daga wurin Allah! Ta wurin wannan furci, Muhammadu ya furta cewa Kristi ba ya cikin jinsin mutanen da aka halicce su daga kasa. Sai dai shi da ne tawurin ruhun Allah, ko kuwa dan Allah na ruhaniya – tawurin fadin kur’ani kuma!
Malaman Musulunci sun gane kumamancin wannan wuri a Kur’ani sai suka karkatar da ma’anar sa. Sun rubuta: Tabbas, Kristi ruhu ne daga Allah a cikin jiki, amma – “Halittacen” ruhu! Madawwamin ruhu mai cin gashin kansa a cikin Allah, mai kasancewa da Allahntaka ba zai taba kasancewa a cikin addinin Islama ba, Duka ruhohin Allah halittatun ruhohi ne, Kaman mala’iku, aljannu, Jibra’ilu da Munka’ilu. An ce Kristi daya ne daga cikin wadannan halittatun ruhohin Allah.
Amma mun sani cewa an haifi Kristi daga Ruhun Allah dawwamamme. Ubangiji ya ce masa “kai dana ne, yau ne na zama mahaifin ka” (zabura 2:7). Bugu da kari, malaika Jibra’ilu ya ce wa Maryama “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon madaukaki zai lullube ki. Saboda haka mai Tsarkin nan da za a Haifa, za a kira shi Dan Allah” (Luka 1:35).
Musulmai zasu iya sanin wannan zahiri, kamar yadda sarki Hassan II na kasar Moroko ya tabbatar bayan taron majalisar Krista a Rabat, cewa babu mutum ko Ayatollah wanda ke da daman ya kira kansa ruhun Allah (Ruhullah), sai dai Isa, dan Maryama; don shi kadai an hafeshi tawurin Ruhun Allah!
4.08 -- Kristi Mara Zunubi ne – Har a Kur’ani
Lokacin da aka sanar da haihuwar Kristi a Kur’ani, Jibra’ilu wanda a ganewar Musulmai ruhun Allah ne da kuma dan sakonsa, ya yi wa Maryama alkawarin zata haifi da maitsarki, mara aibi (Sura Maryam 19:19). Wannan Kalma ya cika tunanin yawancin malamai. Wadansu sun rubuta a fili cewa an haifi Isa babu zunubi kuma da tsarki, domin haihuwarsa na ruhun Allah ne.
Wadansu hadisai na Muhammadu sun kara bayyan wannan: Akan haifi ‘ya ‘ya babu zunubi amma da zaran sun fito, shaidan yakan harbe su da zunubi. Shi ya sa kowane jariri yakan yi kuka – amma ban da Maryama da Isa! An tsaresu daga gubar shaidan domin matar Imrana ta boye ‘yarta da jikanta a kalkashin tsaro na musamman na Allah daga sharrin shaidan kafin a haifesu (Sura Al’lmran 3;36).
Tun da Kristi kalmar Allah ne wanda ya bayyana a cikin jiki a Kur’ani, bai yi wa’azinsa kadai ba amma yayi rayuwar da ta nuna haka. Babu bambanci tsakanin kalmarsa da rayuwarsa. A Kur’ani ma, Isa shine kadai mutunin da yayi rayuwa babu zunubi. Rayuwarsa kalmar Allahne bayyananne. A cewar Kur’ani, da Yesu yayi zunubi da ya mutu da kuma yana cikin kabari yana jiran shari’an Allah. Amma an dauke Kristi zuwa wurin Allah a cewar Kur’ani yana zaune tare da shi. Shi daya ne daga cikin makunsantan Allah. Yakan yi zance da shi fuska da fuska (Sura al-Maida 5:116-118). Babu zunubin da zai raba shi da Mai Tsarki. Kristi mai tsarki ne, kamar yadda Allah Mai tsarki ne. a bayyane Kur’ani yayi maganar zunuban su Ibrahim, Musa da Muhammadu (Sura Ghafir 40:55; Muhammad 47:19; al-Fath 48:2; al-Nasr 110:3). Amma game da Kristi ba a dai ambaci wani zunubi ko laifi ba ko a hadisi.
A Linjila an nuna mana har ma aljannu sun gane asirin cewa Yesu mai tsarki ne, domin sun yi kuwwa suka ce: “Na san ko wanene kai, Mai tsarkin nan ne kai na Allah” (Markus 1:24; Luka 4: 4:34). Daga karshe, tashin da Yesu yayi daga matattu ya nuna tsarkin Kristi. In da yayi zunubi ko daya a maganarsa, aikatawa, tunani ko cikin mafarki, da mutuwa tayi nasara akansa Amma Kristi ya tashi daga Matattu! Mugun bai hana shi tashi ba.
4.09 -- Kristi – Ayatollah na Gaskiya
A kwai ayoyi guda biyu a Kur’ani da suke cewa Kristi da uwatasa “alama ne na Allah domin duniya (Sura al-anbiya 21:91; al-Mu’minun 23;50). Wata ayar kuma ta ce dan maryama kadai shine alama ga duka duniya (Sura maryam 19:21). Kalmar da aka juya alama itace (ajatun) tana kuma nufi mu’ujjiza ko kuwa alama ta mu’ujjiza. Duk wanda ya karanta wannan kalma “alama” tare da kalma “Allah” zai san “Ayatollah”. A kan haihuwarsa na ban mamaki, an dauki Kristi da uwarsa alama mai ban al’ajibi na Allah kasancewarsa na musamman ba alama ce da Krista da Yahudawa kadai ba, amma a mabiya addinin Hindu, Buddha, Musulmai da wadanda basu yarda da Allah ba. Kristi alama ne na Allah ga dukan ‘yan adam. Shi da uwarsa sun zama abin al’ajibin da ya shafi sama da lahira, don Kur’ani ya yi magana akan alamar Allah don duniyoyi, a nan duniya da lahira. Kristi shine Ayatollah na gaskiya, don bai sami wannan lakabi don yayi karatu a jami’a ba amma ya karbe shi daga wurin Allah. Isa shine kadai Allah ya nada shi Ayatollah. Muhammadu bai yi kuskure ya dauko wa kansa wannan lakabi ba, domin ubansa da uwarsa sanannu ne.
Tawurin Linjila zamu ga wannan aya a hanya ta musamman. Yesu ya ce. “Duk wanda ya ganni, ai yaga Uban” (Yahaya 14:9). Dan Maryama shine kamannin Allah mara ganuwa, shine walkiyar daukakarsa da kuma hasken duniya. Shine alaman da Allah ya ba duka mutanen duniya. Ya cika ainihin manufan halitta “Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum”. (Farawa 1:27). Tun daga nan babu wanda ya iya cewa; duk wanda ya ganni ya ga Allah, sai Yesu, Dan Allah, domin shi daya ne da Ubansa wanda yake cikinsa (Yahaya 17:21-24). Yana marmarin ya canza mu zuwa kamaninsa. Zunubi ne yasa muka gaza kamar yadda Bulus ya rubuta. “gama ‘yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuwa ga daukakar Allah’ (Romawa 3:23). Yesu yana so ya dauke zunubanmu sa’annan ya cika duk inda muka kasa (I Yahaya 3:1-3). Shaidar rayuwarka a yawancin lokaci kan fi yi wa musulmai bishara fiye da kalmomin ka.
4.10 -- Kristi – Jinkai Daga Wurin mai Jinkai da Juyayi
An kira Isa “Jinkai daga wurin Allah” a Kur’ani (Sura Maryam 19:21). Muhammadu ya ji labarin mu’ujjizun Yesu, cewa ya warkar da makafi da kutare, ya tada matattu ya ba almajiransa abinci daga sama. A gareshi, Yesu jinkan Allah ne cikin jiki. Wannan aya ta taba wata kungiyar masana Kur’ani. Wadansunsu su sunce: “Allah ne mai jinkai duka (al-Rahman), Ruhu Mai Tsarki shine mai mai Juyayi (al-Rahin) kuma Kristi ne mai Rahama (al-rahmat)” dan Maryama yana da abinda Allah yake da shi a cikinsa, ruhu daya ne ke cikinsu.
An rubuta wannan aya a cikin harshen larabci a jam’i. Allah ya fadi cewa dan Maryama jinkai ne daga gare “mu” saboda haka wadansu masu neman gaskiya sun furta cewa “Kristi jinkai ne na mai yin jinkai da mai juyayi”,wanda a kaikaice Kur’ani ya tabbatan da dayan takan Triniti Mai Tsarki. . Jinkan Allah cikin Yesu Kristi kuwa, alheri ne mai barataswa tare da ikon Ruhu Mai Tsarki wanda zai taimakemu mu cika sabon dokan Kristi tawurin alheri kadai.
Amma Muhammadu ya so ya hana wannan bayani, saboda haka ya kira kansa mai jinkai daga wurin Allah a Kur’ani! Ta yaya jinkan Allah ya zama a bayyane a rayuwa da ayyukan Muhammadu? Duka ayoyinsa a Kur’ani da Hadisai sune aka hada suka zama shari’ar musulunci. Tawurin wannan sharia ne yayi kokarin siffata mabiyan sa a duniya da lahira. Ko ta yaya, kowace doka tana kawo hamayya da fushi babu wanda zai iya cikakken bin doka har abada. Shari’ar Islama daga karshe zai shar’anta duka musulmai. Ya zama wa Muhammadu tilas ya furta cewa duka musulmai zasu gidan wuta (Sura Maryam 19:71-72).
Yesu kuwa, ba ya kawo mana sabon doka bane kadai, amma ya yi mana jinkai na samun gafara. Ya kuma bamu iko mu cika dokarsa ta kauna. Ya bamu daman zama ‘ya’yan Allah, ya bamu rai Madawwami. Jinkai na Allah a cikin Muhammadu doka ne kadai wanda daga wanda a kaikaice Kur’ani ya tabbatar da dayantakan Triniti Mai Tsarki. Jinkan Allah a cikin Yesu Kristi kuwa, alheri ne mai barataswa tare da ikon Ruhu Mai Tsarki wanda zai taimakemu mu cika sabon dokan Kristi tawurin alheri kadai.
4.11 -- Yaya Nagartan Kristi Yake a Kur’ani?
A sura Al’imran mun karanta cewa Isa ma daya daga cikin nagargaru (3;46). A cikin sura al-an’am mun sake karanta cewa Ibrahim, Isyaku, Yakubu da Nuhu suna cikin masu adalci har ma da Dauda, Sulemanu, Ayuba, Yusufu, Musa, Zakariyya, Yahaya da Yahaya mai Baftisma amma Isa yana cikin “nagargaru” (6:83-85). A cikin kur’ani, zama nagari baya nufin mara zunubi amma rayuwa a musulmi mai tsoron Allah.
Yesu ya riga ya warware wannan matsala lokacin da ya amsa tambayar saurayi mai arziki “Ba wani managarci sai Allah kadai” (Markus 10:18) saurayin ya riga ya kira Yesu malam “managarci,” amma Yesu ya rushe marmarinsa na so ya zama nagari a addinance, kuma ya bayyana wa mai neman sanin gaskiya, cewa cikakken kaunar Allah ne kadai magwajin da za’a iya sani ko mutum nagari ne. Dukanmu mukan kasa, muna da mugunta kuma mun gurbata kanmu – Yesu ne kadai ya bambanta! Ya so ya jagoranci wannan saurayi ya gane kuma ya furta cewa shi, Kristi ne “Managarci” Allah cikin jiki, kauna mai tsarki cikin bayyanuwar mutum.
Amma Muhammadu ya musanci wannan gaskiyar kuma ya kira Yesu daya daga cikin nagargaru. In muna magana da musulmai, zai zama da taimako in mun karkatar da tunaninsu daga darajata abubuwa na mutuntaka, a jawo hankulansu zuwa ga kaunar Allah. In wani yace shi nagari ne ko musulmi mai ibada, zamu iya tambayarsa: “Kai kana da nagarta kamar yadda Allah nagari ne?” Ba zai yarda ba, daga nan sai ka nuna masa kasawarsa wanda shine ainihin zunubinsa.
4.12 -- Kristi – Mai Tawali’u da Adalci
A sura maryam an kira Isa. “Mai adalci, cike da ibada da kuma lura da uwatasa. Ba zai zama yamutsatstsen kato ba ko mai ci da karfi ba” (Sura Maryam 19:32). Wadannan halaye na Kristi a Kur’ani a kaikaice suna nuna halinsa na gaskiya. Kristi ba mai adalci da ibada bane kadai. Shine mai barataswa da kansa, a cikinsa tsarkin Allah yake a bayyane. A cikin wannan fadi daga kur’ani za a ga yawancin halaye na Yesu.
Muhammadu ya gane cewa Isa ba gago bane wanda duka jama’a suna tsoronsa (jabbar), kuma ba mai nasara bane tawurin nuna karfi (qahar) kamar yadda Allah yake a Islama, amma shi mai tawali’u ne da kaskanci cikin zuciyarsa. Bai biya muradin zuciyarsa da karfi ba. Bai yi yaki ko kai wa wani hari ba, kamar yadda Muhammadu yayi sau 29. Ya umurci Bitrus: “Maida takobinka kube. Duk wanda ya zari takobi, takobine ajalinsa” (Matiyu 26:52). Ya gwammaci ya mutu don abokan gabansa, a maimakon shi ya kashe su. Kristi mai kauna ne, cike da jinkai da juyayi. Ya taimaki marasa galihu da marasa lafiya kuma bai juya zuwa ga masu arziki da mulki ba. Ya ce “Kuzo gareni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasheku. Ku shiga bautata, ku kuma koya a gareni, domin ni mai tawali’u ne, marar girman kai, zaku kuwa sami kwanciyar rai. Domin bautata sassauka ce, kayana kuma marar nauyi ne” (Matiyu 11:28-30).
4.13 -- Kristi – Mai Albarka Duk Inda zai Kasance
Wannan lakabi na Kristi a Kur’ani ya sa shi ya zama tushen albarkar Allah mara karewa (Sura Maryam 19:31). Wannan gaskiya yayi daidai da bayanin Bulus a wasikarsa zuwa ga Ikklesiya ta Afisu: “Yabo ya tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da ubansa kuma, wanda yayi mana albarka da kowace albarka na ruhu, basamaniya, cikin Almasihu”. (Afisawa 1:3).
Aya na Kur’ani game da Kristi mai albarka ya motsa musulmai a Indiya da Fakistan su kusanci Krista da ke kewaye da su su yi musu adu’a don Kristi rayayye ya warkar da su. A wannan aya bamu karanta cewa Kristi zai iya sa albarka, ya warkar kuma yayi ceto a wannan duniya kadai ba, amma zai iya yin wannan a duniya mai zuwa bayan tafiyarsa zuwa sama. Krista na Asiya basu bada amsar bukatarsu da wuri ba amma sun ce: “Adu’ar mu da zamu yi muku babu amfani sai in kun bada gaskiya ga Kristi, kun tuba daga zunubanku kuma kun roki gafara daga wurin Kristi” Musulman da suke neman taimako nan take suka mai da martani sukace: “Mun bada gakiya ga Isa, ruhun Allah cikin jiki, wanda ya warkar da marasa lafiya ya kuma tada matattu. Yana iya warkaswa a yau, domin yana zaune tare da Allah yana albarkatar duk wanda ya zo gareshi.” Yesu kuma ya ji adu’ar wadannan musulmai masu bangaskiya, ya warkar da su ya taimake su ya ciresu daga bakincikinsu. A cikinsa akwai jinkai da yawa. Yana da ikon Allah. Duk wanda ya gaskanta da shi in ma bangaskiyarsa Kamar kwayar zarra ce, in yayi kuka “yi mini jinkai”! Zai iya samun jinkai da albarka daga wurin Ubangijinmu rayayye da mai ceto.
4.14 -- Isa Kamar Adamu ne Kadai?
Muhammadu ya bayyana Isa tawurin sunaye da lakabobi babam-dabam har guda 25 a cikin Kur’ani. Yawancin wadannan sunaye suna darajanta dan Maryama fiye da misali kuma ana daukaka shi birbishin duka annabawa da manzannin Allah. Kotayaya Muhammadu ya shaida wannan gata na Kristi saboda ya ja ra’ayin Krista zuwa musulunci, tawurin maida addinin Islama ya zama Kaman na Krista.
Domin kada ya rudar da musulmai, saboda kada su bar musulunci su kama addinin Krista, dole ne ya kawo Isa wanda ya riga ya daukaka daidai da gaskiyar musulunci! Bayan kwana uku na tattaunawa irin ta neman gane juna a Madina da Bishof da sarkin Wadi Nadjran da tawagarsu ta Krista mutum 60 masu magana cikin harshen larabci, Muhammadu ya takaita muhawaran da suka yi akan Kristi a wannan aya; “Lalle ne, misalin Isa a wurin Allah kamar misalin adam ne, (Allah) Yahalitta shi daga turbaya, sa’anan ya ce masa: “ka kasance! Sai ya kasance. Gaskiya daga ubangijinka take, saboda haka kada ka kasance daga masu shakka’. (Sura Al’imran 3:59-60).
Musulmai a yawancin lokoci sukan maimaita wannan aya domin su nanata cewa ba Isa ne kadai aka haifa ba tare da uba ba. Adamu ma an halicce shi tawurin kalmar Allah, Hauwa’u kuma da daya daga cikin hakarkarinsa. Saboda haka ba a ganin haihuwar Yesu wani abu na musamman.
Amma Muhawara irin wannnan bata da zurfi. A cewan Kur’ani, ba a halicci Isa daga yumbu ba amma tawurin Ruhun Allah cikin Maryama. Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi a fadin Kur’ani amma Isa bai yi zunubi ba. An kori Adamu da Hauwa’u daga gonar aljanna sun kuma mutu sun rabu da Allah. Amma dan Maryama na raye tare da Allah a fadin Kur’ani. In mun bi littafin musulmai zamu iya gani cewa bai kyautu a ce wai Isa kamar Adamu ne ba, domin an halicci Adamu daga yumbu ne, amma Isa ruhu ne daga Allah a cikin jiki.
Littafi Mai tsarki sau da yawa ya yi shaida cewa Yesu ya zama mutum har ma jariri. Ya zama kamar Adamu kuma an jarabce shi Kaman mu, amma ya kasance babu zunubi. Yesu ya kira kansa dan’uwanmu. A wannan lokacin kuma shine Ubangijin duka duniya kuma Allah na gaskiya daga Allah na gaskiya. Shi da ne na Ibrahim kuma dan Dauda ne daga karshe kuwa shi Dan Allah ne kuma shi daya ne da Uba. Yesu kuwa cikakken mutum ne kuma Allahne. Wannan bangaskiya bashi da makama a tunanin mutuntaka, amma abin na ruhaniya ne kwakwalwanmu ba zai iya gane wannan asiri ba in ba tare da hasken Ruhu Mai Tsarki ba! Dole ne muyi hakuri da musulmai lokacin da basu iya gane wannan gaskiya biyu da wuriba, da kuma gaskiyar na Kristi wanda yafi gaban ganewar dan adam da kansa ba. Yin adu’a don musulmi mai nuna sha’awa da kuma samu kubutarsa daga ruhu mai gaba da Kristi yana da muhimmanci daidai da rokon da mukan yi na samun shaida wanda Ruhu Mai Tsarki kan jagoranta da mukan roka cikin adu’a.
4.15 -- Kristi – Bawan Allah ne?
A kur’ani, Isa ya gabatar da kansa a matsayin “bawan Allah (Abdullahi)” a daya daga cikin maganganun da yayi sa’anda yana jariri (Sura Maryam 19:30). Sau da yawa Muhammadu ya kira Isa da wannan lakabi (Sura al-Nisa’ 4:172; Maryam 19:93; al-zukhruf 43:59). A kowane yanayi yana so ya kawar da zancen Allahntakar Isa daga tunanin musulmai.
Tawurin irin wannan rage daraja Muhammandu ya kawo Kristi kusa da alkawalin Allah game da zababben bawansa a cikin Ishaya 40 – 66. duk abinda aka bayyana anan game da bawan Allah za a iya yin bayani game da Isa bawan Allah kwatanci da wanda aka yashe shi a fadin Ishaya 53:4-12, ya dauki laifofinmu da horonmu a bisa kansa – wannan zai iya ba musulmai haske. A wannan nassin bamu karanta inda aka rubuta “Dan Allah” ko kalma “giciye”. Domin wannan musulmai zasu iya yarda kuma su gane wannan alkawali game da bawan Allah. Manzo Bulus ya yi bayani cewa an riga an cika babban alkawali na Ishaya 53 a lokacin da yake girmama Kristi a wasikar sa zuwa ga Ikklesiya ta Filibi “sai ma ya maida kansa baya matuka ta daukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin dan adam. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya kaskantar da kansa ta yin biyaya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta giciye. Saboda haka ne kuma Allah ya daukaka shi mafificiyar daukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da ke birbishin kowane suna, domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a sama da kasa, da kuma can karkashin kasa, kowane harshe kuma ya shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin daukaka Allah Uba”. (Filibbiyawa 2:7-11)
4.16 -- Isa – Annabi, a Cewar Kura’ni
Muhammadu ya cigaba da musuluntar da dan Maryama kuma ya taba kiransa annabi (Sura Maryam 19:30). Kafin haka ya kirashi manzon Allah sau biyar da kuma kalmarsa. Amma tawurin furta lakabinsa na annabi yana so ya bayyana a fili cewa Isa bai fishi girma ba. A ta kowace fuska bai so ya mai da kansa karkashin Kristi ba.
Kur’ani ya ambaci annabawa da yawa daga Tsohon Alkawali da sunayensu. A Hadisai, Muhammadu yayi magana akan annabawan Allah guda 200,000 amma bai kira sunayensu ba. Sun kawo albishir daga wurin Allah (Sura al-Baqara 2:213; al An’an 6:61) da fadakar da mutane akan shari’arsa (Sura abbagqra 2:61; 87, 91; Al’Imran 3:21, 112, 113, 181, 183; al-Nisa 4:155, 157; al-Maida 5:70). A cewar Kur’ani, Isa ya bi sawayensu ne (Sura al-Maida 5:46).
Lakabin annabi da aka ba Isa yana bamu yiwuwar gabatar da shaida ta Kristi daga Linjila: “kada kuyi zaton na zone in shafe attaura da koyarwa. Na zone ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cikasu. Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da kasa su shude, ko wasali ko digo na attaura ba zasu shude ba, sai an cika dukan kome” (Matiyu 5:17-18).
“Matsayin Isa a annabi a cikin islama zai taimaki cin nasara da sukan da musulmai kan yi na cewa an caccanza wadansu abubuwa a Tsohon alkawali.”
4.17 -- Yesu na da Rai – Kusa da Allah!
Bakon abu, Muhammadu bai iya yin musun kasancewan Yesu na har abada ba. Yayi shaida sau biyu cewa Allah ya dauko shi zuwa wurinsa (Sura Al’lmran 3:55, al-Nisa 4:155). Isa yana matsayin “Mai daraja sosai a wannan duniya da kuma duniya ta gaba” kuma “daya daga cikin wadanda sune makusantan Allah” Muhammadu na da wayo. Bayan ya bayyana wa Krista cewa Isa bai mutu a kan giciye ba, sai ya bar Allah ya dauke shi zuwa wurinsa a sama (Sura Al’mran 3:55; al-Nisa 4:158).
Ga abin mamaki! Kur’ani ya tabbatar: Yesu yana da rai! Shi bai mutu ba! Bayanin sharia (fatawa) daga Saudiyya ya tabbatar mana a kwanakin mu cewa Isa ya tashi zuwa wurin Allah da jikinsa, rai da ruhu. Yana cikin bayin Allah da ke a sama. Yana da tagomashi ana kuma bashi girma sosai. Babu wanda zai iya shiga sama in ba yabi ta wajen Kristi ba. Wadansu masu bada shawara a ayukan ruhaniya sun ce wannan kalmar (wajihun) ya yarda mana mu ce Kristi shine matsakanci, babban firist da mai kare mabiyansa, wanda yana da alkawali mai karfi da Allah (Sura al-ahzab 33:7).
Kristi, a fadin Kur’ani, yana tsaye a gaban Allah Kaman manyan malaiku, Jibra’ilu, Kerubim da Serafim. Hasken Allah bai kasheshi ba domin shi ruhun Allah ne kuma yayi rayuwa a duniya babu zunubi. Muhammadu ya karbi ra’ayoyi da yawa daga koyaswar Krista. Amma bai taba yarda cewa Kristi yana zaune akan kursiyi tare da ubansa ba (Wahayin Yahaya 3:21). Ya bar Isa ya zo kusa da kusiyin, kusa-kusa amma bai zauna akan kursiyin tare da ubansa ba Muhammadu ya saba yi haka. Yesu yana da rai Muhammadu matacce ne! Wannan shine takaitaccen labari mai ban sha’awa na mutane biyu da suka fi yin tasiri a tarihin duniya wanda ya bi Yesu yana bin addinin rai! Wanda ya bi Muhammadu, yana kokari ya shiga hannun mutuwa.
4.18 -- Zance Tsakanin Allah da Kristi a Sama Daga Kur’ani
A sura al-Ma’ida mun karanta zance tsakanin Allah da Kristi a sama bayan Isa ya mutu cikin salama kuma Allah ya dauke shi sama zuwa wurinsa (Sura al-Ma’ida 5:116 – 118). Lokacin da Kristi ya kai sama, ma daukaki ya tambaye shi ko shine ya koyawa mabiyansa su yi masa da uwarsa tare da Allah sujada? Kristi ya musanci wannan suka a kur’ani ya kuma nuna rashin laifinsa.
Ko ta yaya, a shaidarsa Kristi ya kira Allah shaida da kuma waliyai mabiyansa, kamar yadda Yesu da shi shaida ne da waliyai A wannan zance na sama Allah da Kristi suna da suna guda (shahid). Zamu iya yin amfani da Zabura ta 23 ya zama inda aka samo wannan kalma a Littafi Mai Tsarki inda Dauda ya ce. “Ubangji makiyayi na ne!” Ta wannan hanya Yesu ya furta a Bishara cewa shi da kansa ne makiyayi mai kyau wanda ya ba da ransa don tumakinsa (Yahaya 10:11). A Islama, Isa yana da wadansu halaye na Allah (Sura al-Nisa 4:159)! A Kur’ani wadannan halaye na Allahntaka da Kristi ke da shi ba a ba wani dan adam ba.
4.19 -- Kristi – Masanin Ranar Tashin Kiyama
A cikin zurfin zuciyarsu, musulmai suna tsoron ranar tashin kiyama, domin a lokacin ne Allah zai shar’anta ayukansu. Kristi yana da Muhimmiyar matsayi a sha’anin abinda zai faru bayan tashin kiyama. Hadisai da yawa sun ce Isa zai dawo ya kashe Antichrist, ya kashe duka aladun duniya, ya rushe alaman giciye akan majam’u da kaburbura. Bayan haka, zai yi aure ya haifi ‘ya ‘ya. A matsayin mai kawo canji a Islama, zai musuluntar da duka mutanen duniya har ma Krista (Sure al-Nisa 4:159). Lokacin da ya kamala wannan aiki, zai mutu sa’annan a bizneshi a tsakanin kabarin Muhammadu da na Abubakar a Madina. Wannan shine sa’a ta sanin in da mutane zasu kasance, ko a wuta, ko aljanna, a wannan sa’a ne Allah zai shar’anta duka duniya, zai tada Muhammadu da Isa daga matattu, ya nada su su zama cikin wadanda zasu shar’anta duniya. Muhammadu zai shar’anta masulmai wadanda basu yi sallah, bada kudi ko jihadi ba, Isa kuwa zai shar’anta duka Yahudawa da Krista wadanda suka ki addinin musulunci. Mutuwar Kristi bayan zuwansa na biyu a Kur’ani ana kiransa “sanin sa’ar” (sura al-Zukhruf 43:61), domin shine farkon abinda zai faru a karshen duniya.
Wata malama (Krista) a Indonesiya, wacanda ta koyar da darasin addinin Islama a makaranta gwamnati ta ce: “Lokacin da ya zama dole in bayyana wa yara na ka’idodin Islama game da karshen duniya na kan ji haushi domin Isa wanda yana da kumamanci, da tawali’u an ce zai kashe AntiChrist! Ba a fadi wani abu game da Muhammadu wanda shi annabi ne da jarumin yaki a karshen duniya! Na so in ga Muhammadu ne ya zama mai nasara, ba dan maryamu ba! Ko ta yaya, na yi tunani in Kristi zai zo daga sama, zai yi kyau in shirya kaina don dawowansa. Ya kamata in karanta abubuwan da zai tambayeni, abubuwan da ya umurta da abubuwan da ya haramta. Ta haka kayaswar Islama akan dawowan Kristi ya jagoranci zuwa karanta linjila kuma ya taimake ni har na sami rayayyen mai ceto a cikin maganarsa”. Yau ita malama ce kuma Krista mai kwazo kuma tana shaidar Yesu na kwarai da zancen dawowansa na biyu.
4.20 -- Menene Isa ya Rasa a Kur’ani?
A wannan zamanin mu da mutane da yawa sun gurbata bangaskiyarsu kada mu bar kyawawan sunaye da lakabobi na Kristi a Kur’ani su makantar da mu, amma mu yi amfani da su a masomin zance na yin bishara ga musulmai saboda mu jagorance su zuwa ga cikakken bishara. Kristi na Musulunci bashi da ikon ceton musulmi ko ya canza shi ya sami haihuwa ta biyu.
Mu sani cewa a Kur’ani babu lakabobi na Allantakan Kristi da ikonsa. Babu wani abu da aka rubuta akan mutuwarsa akan giciye a madadin ‘yan adam ko ikonsa na babban firist, Ruhu Mai Tsarki. Kristi a Kur’ani ba shine tushen rai madawwami ba kokuwa shugaban Ikklesiya. Sashe na biyu da na uku na bangaskiyarmu wanda ake samu a shaidar bangaskiyar Krista ta Nasiya (Nicene creed) gaba daya basu a addinin Islama. Muhammadu bai gane abinda ya hada Kristi da Ikklesiyarsa ba. Saboda haka zamu iya amfani da sunayen Kristi da aka ambace su a Kur’ani su zama abubuwan da zasu taimake mu don mu bayyana wa ‘ya’yan Isma’ilu cikakken bishara.
4.21 -- Kristi – Sarkin Salama
Manufan kwatanta sunaye da lakabobin Kristi a Baibul da kuma Kur’ani ba domin samun hanyoyin yin magana da musulmai kadai ba, amma kuma don nuna halayen Yesu na musamman a duka addinan biyu. Yesu shine mutumin da ya fi kowa girma cikin duka ‘yan adam da suka taba rayuwa a doron kasa – Kur’ani ya goyi bayan wannan. Muhammadu bai musanci zahirin gaskiya cewa dan maryama mutum ne mai kawo salama. Annabin Larabawa jarumi ne na yaki. Akwai jini sosai a hannunsa. Muhammadu yayi sha’awar ganin yadda Kristi ya canza mabiyansa koda shike shi mai tawali’u ne. Shi yasa yace a sura maryam: “Salama ya tabbata gareni ranar da aka haifeni, ranar da zan mutu, da ranar da za a tayar da ni ina mai rai” (Sura Maryam 19: 33).
Tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa har ma da tashinsa daga matattu, Allah na jin dadin Dan Maryama. Kristi ya kawo salama tsakanin Allah da mutane. Ya mutu dominsu a maimakon kisansu. Yesu mai tawaliu da kaskanci a zuciya. Bai taba maida kansa wani abu da karfi ba. Ya ci nasara tawurin bangaskiyar sa, kaunarsa, hakurinsa da sa zuciya. Shi yasa musulmai sukan furta wadannan kalmomi “salama ta kasance gareshi!” (as-salamu ‘alayhi) duk lokacin da suka kira sunansa. Sun sani cewa Kristi shine sarkin salama na gaskiya. Ko da shike musulmai suna amfani da wadannan kalmonmi na darajantawa ga sauran annabawa. Amma sauran annabawan sun sami salama ne. Yesu kadai ne tushen salama. A Linjila Yesu ya bayyana: “Salamata nake baku. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa na ke baku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro”. (Yahaya 14:27) Yana da iko ya canza mabiyansa su zama masu kawo salama (Matiyu 5:9).
RAI MADAWWAMI KUWA,
SHINE SU SANKA, ALLAH
MAKADAICI NA GASKIYA, DA
KUMA YESU ALMASIHU DA
KA AIKO
(YAHAYA 17:3)
4.22 -- SUNAYE DA LAKABOBI 25 NA ISA DAN MARYAMMA A CIKIN KUR’ANI
SUNA KOLAKABIN ISA | SAU NAWA A KUR’ANI | INDA ZA’A SAMI AYA |
---|---|---|
Isa | 25 | 2:87, 136, 253; 3:45, 52, 55, 59, 84; 4:157, 163, 171; 5:46, 78, 110, 112, 114, 116; 6:85; 19:34; 33:7; 42:13; 43:63; 57:27; 61:6, 19 |
Dan Maryama | 28 | 2:87, 25:3, 3:45; 4:157, 171; 5:17 (Sau biyu), 46, 72, 75, 78, 110, 112, 114, 116; 9:31, 19:34; 23:50; 33:7; 43:57; 57:27; 61:6, 14. |
Kristi | 11 | 3:45; 4:157, 171, 172; 5:17 (sau biyu), 75: 9:30, 31 |
Manzon Allah | 5 | 3:49; 4:157.171; 5:75; 6:61 |
Cikin Mauzannin Allah | 3 | 2:87, 253; 57:27; d/s |
Kalmar Allah | 4 | 3:39, 45, 64; 4:171 |
Kalmar Gaskiya | 1 | 19:34 |
Bawan Allah | 4 | 4:172; 19:30, 93; 43:59 |
Ruhu Daga Allah | 3 | 4:171; 21:91; 66:12 |
Alama don mutane | 3 | 19:21; 21:91; 23:50 |
Daya daga cikin managarta | 2 | 3:46; 6:85 |
Kaman Adamu | 2 | 3:59; 43:59 |
Ma shaidi | 2 | 4:159; 5:117 |
Yaro mara zunubi ko aibi | 1 | 19:19 |
Jinkai Daga Allah | 1 | 19:21 |
Annabi | 1 | 19:30 |
Daya daga cikin annabawa | 16 | :61, 91, 136, 177, 213; 3:21, 80, 81, 112, 181; 4:69, 155, 163; 17:55; 33:7; 39:69; d/s |
Mai kawo Albishiri | 2 | 2:213; 6:61; d/s |
Mai tabbatar da attaura | 2 | 5:46; 61:5 |
Daya daga cikin masu fadaka | 1 | 2:213; d/s |
Mai adalci zuwa ga uwatasa | 1 | 19:32 |
Ba mai rushewa ba | 1 | 19:31 |
Ma Kusancin Allah | 1 | 3:45 |
Masanin sa’ar | 1 | 43:61 |
Salama a bisansa | 1 | 19:33 |
4.23 -- SUNAYE 35 NA YESU A LITTAFI MAI TSARKI (YADDA SUKA BAYYANA)
SUNAN YESU | SAU NAWA |
---|---|
Yesu | 975 |
Kristi | 569 |
Ubangiji | 216 |
Dan Mutum | 80 |
Dan Allah | 59 |
Shugaba | 56 |
NI NE | 50 |
Dan rago na allah | 33 |
Sarki | 33 |
Malam | 27 |
Mai ceto | 26 |
Rai | 20 |
Mai zuwa | 20 |
Mutum | 19 |
Yaro | 18 |
Annabi | 16 |
Haske | 13 |
Dan dauda | 10 |
Bawan ubangiji | 10 |
Jiki | 10 |
Mai Tsarki | 10 |
Mai Adalci | 10 |
Babban firist | 10 |
Shugaban Ikklesiya | 10 |
Mai girma | 10 |
Madaukaki | 10 |
Mai kariya | 9 |
Alkali | 8 |
Mai kawo sulhu | 8 |
Wanda aka fifita | 8 |
Mai iko | 8 |
Kamannin Allah | 7 |
Wanda aka yashe shi | 6 |
4.24 -- Tambayoyi
In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan
Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.
Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.
- Sunaye da lakabobi da halayen Kristi nawa ne zan iya samu a Baibul da nawa kuma a Kur’ani?
- Menene ma’anar suna “Isa” ga musulmai kuma sau nawa ne aka rubuta shi cikin Kur’ani? Me yasa mishanarai daga kasashen ketare sun fi son amfani da wannan suna sa’ilin nan Krista Larabawa basa amfani da shi? Me yasa suna Isa ba daya bane da Yesu? Kaka zamu yi amfani da suna Isa a zancen mu har mu jagoranci musulmai zuwa ga Yesu na gaskiya?
- Sau nawa ne lakabi “Kristi” (al-Masih) ya bayyana a Kur’ani? Menene wannan lakabi ke nufi ga musulmai da kuma Krista? Yaya Yesu dakan sa ya bayyana wannan lakabi a linjila?
- Menene lakabin “manzo” (Rasul) ya kunsa kamar yadda aka yi amfani da shi a Kur’ani wa Kristi? Me yasa Muhammadu ya ki ba Kristi Lakabobi na “sarki” da “Ubangiji duk da rashin ganewa manufan zuwan Yesu?
- Me yasa Dan Maryama a Islama ba zai taba zama dan Allah ba? Ta yaya wannan ya yiwu ga musulmai su amince da haihuwar Yesu tawurin budurwa Maryama amma sun ki yarda da Allahntakansa?
- Wadanne kalmomi biyu ne a shaidar bangaskiya ta Nasiya da ya kawo bambanci tsakanin Islama da addinin Krista a fahimtarsu a kan Kristi?
- Me yasa Kristi ya kira kansa “Dan mutum” sau 80 a bisharu hudu sa’annan yakan jinkirta kiran kansa Dan Allah?
- Menene musulmi kan yi tunani akai in ya karanta Kur’ani ya ga an rubuta cewa Kristi kalma ne daga Allah ko kalmarsa? Wadanne ma’noni na Baibul ne za’a iya cika wadannan lakabobi?
- Me yasa Muhammadu ya kira Kristi Ruhu mai tafiya wanda ya sauko daga wurinsa kuma ya koma wurinsa?
- Me yasa bashi yiwuwa Ruhu Mai Tsarki ya kasance a Islama kamar yadda yake cikin bishara?
- Ta yaya zamu yi amfani da wannan kalma na Kur’ani “zakiy (Mara aibi) ga isa, wanda ke nufi wanda bashi da laifi kozunub tun yana yaro?
- Wace ma’ana wannan zai bamu a shaidarmu ga musulmai cewa Isa na Kur’ani shine kadai Ayatollah wanda Allah ya nada a duka tarihin duniya?
- Wace kafa ce Kur’ani ya bude mana tawurin bayyana cewa bayyanuwa Kristi cikin jiki jinkai ne daga wurin Allah?
- Yaya nagartan Kristi a Kur’ani tunda Muhammadu ya kamanta shi da daya daga cikin nagargaru? Ta yaya zamu iya nuna wa musulmi cewa Dan Maryama Managarci ne Kaman Allah?
- Me kur’ani ke nufi da cewa Isa mai adalci ne ga uwatasa? Ko akwai hanyar da zamu nuna wa musulmai adalcin Allah cikin amfani da wannan kalma?
- Ta yaya zamu canza wannan furci na Kur’ani na cewa Kristi ba yamutsatstse ko mai halin dabba bane mu maida su sashen magana da za a iya amfani da su don yin bishara?
- Menene shaidar Kur’ani game da Isa ke nufi sa’anda an kwatanta shi a mai albarka duk inda zai kasance a sama da duniya?
- Me yasa Muahmmadu ya takaita shaidarsa game da Kristi a magana daya cewa Kristi Kaman Adamu ne? Wane kuskure za a samu idan an gwada wannan magana da wadansu maganganu na Kur’ani gama da Isa?
- Ta yaya zamu cika lakabi “Bawan Allah” (Abdullahi) da aka ba Kristi a Kur’ani da cikakken bishara? A ina ne a Littafi Mai Tsarki aka kira Yesu Bawan Ubangiji?
- Me yasa Isa na Kur’ani ba daya daga cikin annabwa bane kawai amma mutum ne na musamman? A takaice ka bayyana wannan asirin.
- Yaya Muhammadu ya iya shaida cewa an darajanta Kristi a wannan duniya da mai zuwa kuma yana zaune kusa da Allah bayan ya koma wurinsa?
- Menene zai iya zama ma’anar zance na Allah da Kristi wanda aka rubuta a Kur’ani bayan da ya koma sama? (Sura al-Ma’ida 5:116-118) Me yasa an ba Kristi lakabi iri daya da Allah (shiheed – Mai Kiyayewa, ma shaidi)?
- Tayaya musulmi ke tunanin cewa bayyanuwar ranar shari’a ya danganta ne akan dawowan Kristi na biyu?
- Wadanne ayoyi ne na Kur’ani zaka bayar da zasu bayyana cewa Yesu ne kadai sarkin salama, mai kawo salama na kwarai da kuma musulmi na gaskiya a duniya?
- Wadanne sunaye ne masu Muhammanci a Baibul wadanda basa cikin Kur’ani? Me ya sa?
- Ina iyakar inda zamu iya kaiwa a kokarin mu na cika sunaye, lakabobi da halayen Kristi a Kur’ani da ma’anoni na bishara?
- Me yasa musulmai sukan fuskanci wahalar fahimtar kalmomin mu na Krista, misali in muka yi magana akan ceto ko maiceto? Me yasa yawancin furci na Krista musulmai basa ganewa?
- Har zuwa ina ne Yesu da manzanninsa sunyi wa shaidarsu gyaran fuska don yaje daidai da rayuwar Yahudawa da Al’ummai na kullum da tunaninsu don su sami gane cikakken bisharara? Ta yaya Bulus ya zama ba Yahude ga Yahudawa da ba al’umme ga al’ummai? Menene karshen sakamakon irin wannan wa’azi?
Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.
Naku cikin Hidimarsa
Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.
Ku aika da amsoshin ku zuwa:
The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.
Ko
GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY
Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net