Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":

Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 8 Persecution of Converts

This page in: -- Arabic? -- Cebuano -- Chinese -- English -- French -- Georgian -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Kirundi -- Russian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Uzbek -- Yoruba

Previous booklet

01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI

8 - Dole ne Kowane Musulmin da ya zama Krista ya Mutu?



8.01 -- Dole ne Kowane Musulmin da ya zama Krista ya Mutu

Manzo Bulus ya furta tare da duk wadanda suka karbi Kristi daga addinin Yahudanci da Islama cewa: Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci, aka kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka (Zabura 44:22), Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun wuce ma a ce mana masu nasara (Romawa 8:36 – 37).

Manzo zuwa ga al’ummai ya tabbatar da wannan shaida tawurin mutuwarsa da aka fille kansa a shekara ta 63 A.D., kamar Yakubu, dan’uwan Yesu, wanda aka kashe shekaran da tagabaci wannan. Haka ma an ce an giciye Bitrus a rataye kafa a sama, ka a kasa a Roma a shekara ta 64 A.D. Ubangiji wanda ya tashi daga matattu ya ba wadansu daga cikin mabiyansa daman su dandana wahalarsa (Romawa 5:3 – 5; Filbbiyawa 1:20 – 23; 2:16 – 17; Kolossiyawa 1:24; II Timoti 2:10 – 13; 1 Bitrus 4:16 – 19).

Mutuwa, kamar yadda Bulus ya rubuta, abu mai wuyar ganewa ne, kamar yadde nasara ya hada duka al’amarin tunani da rayuwar wadanda aka baratar dasu. Ya halarta sabobin tuba daga Islama su kauda al’adarsu ta da da ruhun addininsu daga mataki zuwa mataki, yayinda suke girma cikin bangaskiya har sai sun gama shiga cikin Yesu Kristi da Ikkliesyarsa.

8.02 -- Nasara Ta Ruhaniya Bisa Rayuwa Irin Ta Islama

Duk wanda yayi Magana da Musulmi game da Yesu Kristi da kuma ceto, zai iya samun bangaye kashi uku da zai rushe idan zai magance matsalolin Islama.

Kristi, Dan Allah Rayayye

Da farko, Musulmi bai aminci akan zancen Allahntakan Yesu Kristi ba. Da wannan hali, ya zame kansa daga yarda da sanin Allah a matsayin Uba, Da da Ruhu Mai Tsarki ya ki amincewa da dayantakan Trinity Mai Tsarki ya cire kansa daga kammalalliyar fansa, ya musanci barata tawurin alheri kuma baya so ya yi wani abu akan sake haihuwa. Ma shaidin Kristi ya zama masa dole ne ya roki Yesu ya bashi hanyoyin da zasu taimaka masa da zai jawo ra’ayin musulmi har ya yarda cewa Dan Maryama shine Dan Allah wanda ya cece mu daga zunubai.

Duk wanda keda Dan, yana da rai. Wanda bashi da Dan Allah kuwa, bashi da rai”. (I Yahaya 5:12).

Ba zai zama da taimako ba a fara zance da Musulmi nan da nan akan Dan Allah ne domin Musulmai dayawa sun fahinci wannan Magana akan Allah yayi jima’i ne da Maryama sa’annan aka Haifi Kristi, suna nuna adawa da wannan tunani.

Giciyen Kristi

Bango na biyu da ke sa musulmi baya iya gane Kristi da fansarsa ba shine kin amincewa da giciyen Yesu (sura al-Nisa 4:157). Musulmi baya iya gane ma’anar mutuwar Yesu a maimakon mu, kokuwa hadaya ta sulhu da wanke dukan zunuban mu. Babu musulmi kuwa da zai sami gafaran zunubansa muddin ya ki Kristi giciyayye! Duk wanda yayi Magana da Musulmai game da halitta da Shari’a, game da Ibrahim da Musa, game da Mu’ujjizan Kristi da komowansa zuwa wurin Allah bai riga ya taba ainihin Matsalar ba. Yakamta mu taimaki musulmin ya gane cewa shi mai zunubi ne. Sa’annan zamu iya bayyana masa cewa Kristi ya dauke zunuban mu (Yahaya 1:29 – 31).

Amincin Baibul

Bango na uku da ya sa bashi yiwwa Musulmi ya gaskanta Allah-Ubansa shine zaton da suke yi na gurbata Baibul. Tawurin irin wannan zato, ruhun Islama ya kabantas da dogaron Musulmai da yawa akan Attaura da Linjila. Sun gaskata cewa duk abubuwan da Yahudawa da Krista suke fadi, tatsuniyoyi ne kuma Maganganu ne cike da kuskurori. Duk wanda yake so ya taimaki musulmi ya sami ceto wanda aka riga aka kammala a maimakonsa cikin Kristi dole ne ya nemi yadda zai sa shi ya yarda cewa Baibul managar Allah ne na gaskiya wanda baya canzawa.

Wadannan bangaye guda uku ba matsalar tunani ba ne da za a iya warware shi tawurin dabarun nuna shaida da iya muhawara ta salon musulunci ba. A nan mun ga sarkoki na yaudara wadanda alherin Allah ne cikin ikon Ruhu Mai Tsarki zai iya kwance su. Adu’a da bangaskiya cewa za a amsa wadannan adu’oi suna da Muhammanci kamar fita shelar bisharar a tsakanin musulmai a matsayin shaida na tawali’u da gaskiya wanda Ruhu ne ke jagoranta. Kaunar Yesu Kristi, kuwa, shine harshen da zai ratsa cikin kurkuku mafi duhu.

Cin Nasara da Tunanin Islama akan Allah.

Idan wani a cikin sunan Yesu ya ci nasara akan bangaye guda ukun nan na kin amincewa na Islama, zai iya kai wa zuciyar matsalar Islama. Ganewarsu akan Allah na da tasiri akan al’adunsu a kowane fanni, a imani, rayuwa, shari’a da halaye. Wannan kam ba zai iya yin nasara da tsoron mutuwa ko kuwa na ranar Shari’a ba. Duka fanonin Islama sun maida karfinsu tsoron Allahn ne. Duk wanda zai taimake shi ya fita daga Islama dole ne ya bayyana masa Uban Yesu Kristi wanda shine amsar ruhaniya ta Linjila wajen fahimtar Allah.

Wanene Allah?

Musulmi yakan furta a Kalmar shahada cewa: “Babu wani Allah sai Allah. Allah daya ne ba uku ba! Shi Mai girma ne babu mai iya kwatanta shi, bubu wanda zai iya kusantar sa kuma mai iko me. Duk tunanin tauhidi game da shi basu isa ba kokuwa akwai kuskure. Sunayensa da halayensa sukan rufe juna wani lokaci ma su rufe juna. Babu kwakwalwan dan adam wanda zai iya gane Maigirma duka. Ya riga ya kaddara kome kuma yana bukatar biyaya daga wurin kowa. Allah ba allahn kauna mara iyaka ba ne. Yakan yaudari wanda ya ga dama ya kuma biyar da wanda ya ga dama (surorin al-Aan’am 6:39; al-Ra’d 13:27; Ibrahim 14:4; al-Nahl 16:93; al-Fatir 35:8; al-Muddathir 74:31). Shi ba Allah mai gaskiya ba ne, domin ya kira kansa mafi wayo (surorin al-Imran 3:54; al-Anfal 8:30; al-Nisa’ 4:142) shi mai alfarma ne (sura al-Hashr 59:23). Yakan yi wa Musulmai masu ibada rahama da duk wadanda suke bada dukiyarsu kuma suna yin jihadi don yada addinin Islama (surorin al-Baqara 2:195; al-Imran 3:76; 134, 148, 159; al-Ma’ida 5:13, 43,93; al-Tawba 9:4,7,108; al-Mumtahana 60:80 d/s). Ruhu Islama na gaba da Uba, da Da, da Ruhu Mai Tsarki kuma ya ki karbar Triniti (sur al-Ikhlas 112:1 – 4 d/s).

Ubanmu Wanda Ke Cikin Sama

Amsar Linjila ga fahimtar Allah a Islama shine Uban Yesu Kristi. Allah madaukaki Ubanmu ne wanda ya hada dangankata har abada da mu masu zunubi da aka halicce mu daga yumbu, tawurin alkawali na Dan sa Yesu Kristi, wanda ya shafe mu da Ruhunsa Mai Tsarki.

Linjilarmu bata koya mana wani irin Allah wanda ke nesa, wanda ba a iya kusantarsa kuma ba a iya gane shi, amma na nuna mana Allah Uban mu wanda ke kusa da mu. Yana Lura da kowane dayan mu kuma ya san mu fiye da yadda muka san kanmu. Ya san yawan gashin kanmu (Matiyu 10:30; Luka 12:7). Ya bada dansa tilo hadaya don ceton mu daga Shari’a ta ranar karshe. Tawurin Ruhunsa Mai Tsarki yana so ya zauna a cikin mu. Allah uban mu ne wanda ya maida mu ‘ya ‘yansa kuma cikin ruhaniya ya sake mu. Ruhu Mai Tsarki na jagorantar mu mu daukaka sunan Ubanmu a rayuwarmu.

Bambancin da ke tsakanin Islama da addinin Krista na da girma Kaman bambancin da ke tsakanin Allah na Islama da Uban Yesu Kristi. Jim kadan da tuban Musulmi yakan sami rabuwa da ‘yan ‘uwa kuma Allah mara tausayi yakan kishi har sai in sabon tuba ya sami ceto tawurin fada wa a hannun Ubanmu wanda ke cikin sama.

Canzawa

Irin wannan canji ba yakan faru a tunani bane kadai amma yakan shafi duka rayuwan mutum. Duka rayuwarsa zai canza zuwa surar uban. A yayin da Musulmi ya zama Krista, ba shi yiwuwa ya cigaba da kasancewa cikin al’adar da ke adawa da Kristi na lokaci mai tsawo ba. Dole ne ya mika wa Uba duka bangarorin rayuwansa. Yakan koyi yin Magana da Ubansa cikin Adu’a wanda zai amsa masa adu’arsa. Yayin da Musulmi ya zama da na Allah, dole ne ya tube Muhammadu ya kuma yafa Yesu Kristi! Zai sami daman yin girma cikin al’ada ta Yesu Kristi kuma ya zama daya daga cikin iyalin Ubanmu wanda ke cikin sama. Wannan na nufi zai musanci rayuwarsa na da sa’annan ya sami sabontuwa tawurin Ruhu Mai Tsarki. Daukan mataki na farko na nufin shiga cikin duniya ta ruhaniya wanda Islama bata sani ba. Ruhun uban mu na so ya ratsa duka sassan rayuwarsa. In babu tsarki, mutum bazai iya ganin Ubangiji ba! In ba tare da sabontuwa ba babu wanda zai iya zama cikin Kristi ba. Wannan irin canji yakan zo ne tawurin aikin alheri na Ubanmu muddin muna sauraron Dansa da yin godiya domin kiran da yayi mana.

Tarkon Addini Da Al’ada

In mutum bai rabu da Allahn Islama ba ya manne wa Allah Uba ba, sabon rayuwansa zai zauna a ka ne, ba zai shiga cikin zuciya ba. Wadansu tubansu kan zama rabi-rabi ne wani sabon tuba yace, “Ni na yarda kuma na gaskanta cewa Allah (na Islama) shine Ubana na sama, wanda ya bani rai madawwami”. Wannan mutum ya so ya daidaita addini Islama da na Krista. Shi Krista ne yana tare da Krista, amma day a ga matansa da ‘ya ‘yansu da ‘yan ‘uwansa yakan koma musulmi a cikin musulmai. Sakamakon wannan yakan zama rudani ne na ruhaniya. Bambanci tsakanin haske da duhu, tsakanin rai da mutuwa, na da muhimmanci. Saduwa da Kristi tawurin bangaskiya kan tilasta Musulmi ya juya wa Allahn Musulunci baya, kuma ya zauna cikin Uba. Amma yawancin Musulmai suna shakkan juyawa gaba daya; sukan so su yi haka a sannu- a- sannu yayinda suke girma cikin bangaskiya.

Menene ake Nufi da Alheri?

A cikin Kur’ani, Kalma “alheri” an rubuta shi sau 39. Musulmai sun gaskata cewa suna rayuwa a cikin alherin Allah na din-din-din. Amma a cikin Islama, alheri na nufi wani abu dabam da abinda yake a Baibul. Rahaman Allah na kan Musulmai wadanda suke da karfi, nasara, lafiya da daraja. Wanda yana da ‘ya ‘ya, dabbobi, motoci, rakuma da kudi da yawa ya sami alheri mai yawa daga wurin Allah. Allah ya jagoranci Muhammadu ya nemi zainab matar bawansa wanda ya karbe shi a matsayin da wato zaid (sura al-Ahzab 33:37). Wannan ma an dauke shi a matsayin alherin Allah!

A cikin Linjila kuma, alheri da farko na nufin samun gafarar duka laifofin mu! Yesu yana bamu adalci a kyauta domin ya sha wahala kuma ya mutu domin mu. Yawancin lokaci, kaskantattu, marasa lafiya, tsofaffi da masu bakin ciki sukan karbi wannan alherin Allah fiye da masu arziki, masu karfi, masu kyau, wadanda a cikin ruhaniya fanko ne. “Masu albarka ne wadanda ke da talauci a ruhu”! (Matiyu 5:3). Kari a kan alheri da ke kawo barata, masu bada gaskiya sukan karbi kyaututtukan alheri, wadanda albarku ne na Ruhu Mai Tsarki: “kauna, hankali da kamunkai” (Galatiyawa 5:22 – 23). Dole ne sabon tuba ya sani cewa arziki na duniya, abubuwan duniya wadanda mutane suke darajata, girmamawa ta duniya da samun iko da mulki sun sha bambam daga wurin Uban mu na sama.

Zunubi ko Mai Zunubi?

A cikin Islama akwai dogon jerin zunubai bisa ga girmansu: Kananan zunubai sune laifuffukan da za a iya hakuri dasu, laifuffukan da ba a saba yinsu ba, ainihin zunubi zunubi ya hada da laifuffukan da suka shafi Shari’a, laifuffukan mugunta, manyan zunubai da zunubin daba a gafartawa. A koyarwar Kur’ani, musulmi zai iya wanke zunubansa tawurin aikata nagargarun ayuka, wadanda ba a gafartawa ne kadai ba zai iya wanke wa ba (surorin al-Tawba 9:111; al-Ankabut 29:7).

Ba ya ganin kansa a matsayin mai zunubi! Wannan kalma zai kaskantar da duka iyalinsa! Zai zama abin kunya musulmi ya furta cewa shi mai zunubai ne!

Krista na gaskiya sun sani cewa su masu zunubi ne, batattu lokacin da suka gwada kansu da nagarta da kuma tsarki na Ubansu wanda ke cikin sama. “babu wani nagari sai Allah” (Matiyu 10:18). Muna cike da kuskurori, kasawa, mun bata, an hukunta mu cikin jikin mu na mutuntaka. Babu dan adam wanda yake da nagarta na kansa. Tsarki na Ubanmu na bayyana alhakin laifofinmu (Matiyu 5:48). Zunubanmu da laifofinmu sun fito ne daga ruba mara iyaka. Alherin Yesu Kristi ne kadai begen mu. Jininsa na wanke dukan zunuban mu, kuma Ruhunsa kan gina sabon halitta a cikin mu. Idan musulmi bai gane rubewarsa tawurin hasken Allah ba, bai sani cewa matsalarsa ta kai intaha ba, amma yakan cigaba da tunani cewa shi ba ya bukatar mai ceto ko hadaya a maimakonsa ba.

Kaddara Ko Zabe?

Kur’ani na koya wa musulmai cewa Allah madaukaki ne, masanin kome da kuma duka hikima. Cikin Tauhidi, sakamakon wadannan halaye shine Allah ya kaddara kowa da komai, komai kankantarsa (surori al-Furqan 25:2; al-Qamar 54:49; al-Talaq 65:3). An riga an kaddara yaro tun yana kwana 40 cikin cikin uwarsa (sura al-Najm 53:32). Duka zunubai, baye-baye da abubuwan da zai aikata an riga an kaddara su kafin su faru. Kur’ani ya dada da cewa Allah ya kaddara duka Musulmai da su shiga wuta (sura Maryam 19:71 – 72)! Bayan haka kuwa, Allah zai ceci wadanda suke tsoronsa, ko kuwa sun bada arzikinsu don yin jihadi.

A cikin wasika zuwa ga Afisawa (sura 1:3 – 4) Krista zasu iya karantawa cewa Ubanmu na sama ya zabe mu cikin Kristi Yesu don muyi rayuwa ta tsarki a gabansa, cikin kaunarsa, saboda mu canza zuwa kamanin kaunataccen Dan sa (Romawa 8:29 – 30). Wannan zabe ba wani irin likkafani ne da zai rufemu har ya kashe mu ba amma yakan ba mu kuzari da zamu yi kauna, yabo da ‘yin hidima cikin aniya da gaskiya. Ubanmu ne ya kaddara mu cikin Yesu Kristi, shi ba azzalumin sarki mai yawan sake shawara ba ne! za a iya ganin shirinsa na asali a cikin Farawa 1:27 tare da fadada shi a ruhaniya cikin Matiyu 5:48 da Yahaya 14:9 – 11).

Gaskiya ko karya?

A Islama an baka dama kayi karya a cikin hali kashi hudu: cikin Jihadi (in kana Magana da wadanda ba musulmai ba), in za a sulhunta musulmai guda biyu, maigida zai iya yi wa matarsa karya, mace kuma zata iya yi wa mai gidanta karya. Za a iya karya rantsuwan da aka yi cikin hanzari: (sura al-Tahrim 66:2). Allah da kansa yakan yaudari wadanda sukan yaudare shi (sura al-Nisa’ 4:142). Ba a bin mamaki ne ba a duniyar Islama rayuwa da kasuwanci ba a aiwatar dasu bisa yarda gaskiya da aminci.

Yesu yace: “Bari “I” naku ya zama “I”, kuma bari “Aa”, ya zama “Aa”, Duk abinda ya wuce wannan daga wurin Mugun ne”. (Matiyu 5:37). Yesu da kansa gaskiya ne (Yahaya 14:6). Ruhu Mai Tsarki gaskiya ne. (Yohana 14:17; 16:13). Ubanmu na sama gaskiya ne (Yahaya 4:24). Kalmarsa gaskiya ne (Yahaya 17:17). Sabon tuba ma Kaman mu ada ne ya koyi yadda zai zama da gaskiya! Kauna in babu gaskiya, karya ce, kamar yadda gaskiya in babu kauna yakan zama kisan kai ne na ruhaniya. Dole ne mu koyi fadin gaskiya cikin kauna, kuma mu hada hidimar kauna da gaskiyar bishara.

Auren Mata Daya ko Fiye da Daya?

Kur’ani ya ba Musulmai dama su auri mata daya, biyu, uku, ko hudu, idan mutumin zai iya kula dasu daidai (sura al-Nisa’ 4:3). (An soke wannan doka a Turkiyya, Maroko da Tunisiya). Haka kuma, Musulmai da yawa basa iya auren sama da mata daya ko biyu ba don basu da kudi. Ko ta ya ya, aure a Islama ba haduwar abokan tarayya da ke daidai da juna ba ne. Mai gida zai iya horasda matarsa in bata daddara ba zai iya dukan ta (sura al-Nisa’ 4:34). Miji shine gaba da matansa, kamar yadda a cikin kotu shaidar mata biyu ne ke daidai da na namiji musulmi daya. (sura al-Baqara 2:282). Bugu da kari, an bashi dama ya dauki kwarkwarori daga cikin bayinsa mata duk sa’anda ya so. Kur’ani ya yarda wa mai gida ya mulki gidansa Kaman karamin sarki. Hadakai na maigida da matarsa don warware matsalolin rayuwa tare baya cikin Islama. Islama na nufin mika wuya har a cikin aure.

Kristi ya tabbatar da cewa Allah ne ya kafa shirin auren mata daya-daya tun halitta (Markus 10:6 – 9). Manzo Bulus ya shaida cewa mace ta yi biyaya da mijinta shi kuma zai sadakar da kansa don matarsa, kamar yadda Kristi da kansa ya bada kansa hadaya don Ikklesiya (Afisawa 5:21 – 33). A cikin auren Krista ba a maganar ko wanene yake mulki ba, amma wanda ya fi hidima da kaunar dayan! Kamar yadda bambanci tsakanin Allahn Islama da uban Yesu Kristi ke da girma, hakane akwai bambanci mai girma tsakanin fahimtar aure da zaman iyali tsakanin addinan biyu.

Malamai A Makaranta

A da, wani lokaci ma a yau-Allahramma yakan tilasta almajiransa duka don su haddace surorin Kur’ani. Malamin yakan zama Kaman dan karamin Allah bisa almajiran. Baya karfafa su su yi tunani kuma su fahimta amma sai dai haddace. Zamanu da yawa na Malaman Kur’ani sun siffata al’adar Musulunci a matsayin hanyan tunani wanda baya canzawa a cikin Musulmai.

A inda Krista suke, malami mai kyau Kaman Uba ne da aboki wanda yake bi da almajirin zuwa fahimta, tunani, tankade da rairaya da kansa. Rayuwansa na gina almajirin fiye da koyaswarsa. Ba ya zama a gabansu Kaman sarki amma yakan tsaya a tsakiyarsu. Yesu ya fadi wannan a kansa “Dan mutum bai zo don a yi masa hidima ba, amma don shi yayi hidima ya bada ransa fansa don mutane da yawa”. (Matiyu 20:28). Tunanin hidima ta aminci ya ratsa kowane bangaren rayuwar duka Krista, maimakon sha’awar yin mulki. Wannan ya bukaci canji gaba daya, ba cikin rayuwar saboda tuba daga Islama ba kadai amma ga kowane mutum, domin sha’awar zama da girman kai na cikin kowane mutum.

Aiki Maiwuya Ko Kulawa Da Jama’a

A Turai mutane sukan yi murmushi su ce in mutum ya san abinda aiki yake in bai guje ma sa ba wannan mahaukaci ne! A zamanin da mutane da yawa sun yi rayuwa bisa wannan ka’ida. A kasashen Musulunci akan wulakanta ma’aikaci kaman bawa. A kauyuka, inda gwamnatin gurguzanci bai shafesu ba tukuna, ana girmama wadanda suka mallaki gonaki Kaman kananan alloli. Wadanda suka dogara garesu kan sumbaci hannaye da kafafunsu. Yawanci lokaci ma’aikata sukan karbi albashinsu da latti har na wata biyu ko uku saboda kada su gudu. Akwai lokacin da a wata ma’aikata a wani gari, masu yi musu aiki sun yi yajin aiki, mai ma’aikatar ya sayar da abinsa kuma ya kori duka ma’aikatan.

A Sudan akwai lokacin da wadansu mutane da makamai na yaki suka auka wa wani kauye, sun kashe mazajen kuma suka kwashe mata da yara a matsayin bayi. Ba a riga an soke dokar bautar da mutane ba a cikin Kur’ani da Shari’a musulunci ba. Musulmai sun dauki kansu a matsayin iyayengiji. Arna za a bautar dasu ne ko kuwa a kashe su. Krista da Yahudawa za a yi hakuri dasu kuma a “tsare su” a matsayin barori wadanda zasu rika yi wa iyayengidansu musulmai hidima. (sura al-Tawba 9:28 – 29).

Kristi kuwa, yayi rayuwa a tsakanin mu Kaman bawa. Shi mai hankali ne da tawali’u. Yayi aikin kafinta ne ba dan kasuwa ba. Yesu ya kira masunta masu ruhun tuba, wadanda suka saba da aiki mai wuya su bi shi. Kristi bai nada iyayengiji ba, amma masu hidima. Allahn mu mai rahama ne cike da kauna. Duk wanda ya bi shi zai zama kamarsa. Mai bada gaskiya wanda ya dauki ma’aikata zai kula dasu ba zai zalunce su ba. Mulkin gurguzanci zai iya girma a wuraren da addinin Krista ya riga ya shirya hanya ne.

Demakuradiya na Adawa da Islama ne?

A Lebanon wani lokaci iyaye sukan ba ‘ya ‘yansu bakin sunaye Kaman: Napoliyon, de Gaulle, Bismarck, Stalin da Nasser. Za a iya samun wadannan sunaye a rajistan makaranta ko a takardun shaida (satifiket). Watarana wani malami ya kai wa abokinsa ziyara: “Ai Hitila bai biya kudin makarantarta ba”! Yayin daya nemi tabbaci, ya samu ai sunan uban wata yarinya ana kiransa Hitila. Mutane da yawa a kasashen Yahudawa da Larabawa suna sa zuciya da zuwan wani wanda zai kawar da toshiya da rashawa da kamar sharewar tsintsiya. Gamal Abd al-Nasser, Khomeini da Saddam Hussaini irin azzaluman shugabanni ne da talakawa da yawa suka bi kwarai.

Za a iya karanta “Saddam shine sarkin duka duniya” da aka rubuta a bango a mazaunin matalauta a Sekondaraba, Indiya! Musulmai suna jiran azzaluman masu mulki, kananan alloli, ba shugabannin demokuradiya ba wadanda za a iya zabensu ko a ki zabensu ba. Suna shirye suyi fada don wadannan shugabanni, Kaman yadda kungiyoyin Hamas da Hisbollah sukan sadakar da rayukansu don Allah.

Amma Yesu yace: “Masarauta ta ba ta wannan duniya bace. Ni saki ne. Domin wannan dalili aka haife ne, domin wannan kuwa na zo wannan duniya, don in yi shaida domin gaskiyar. Duk wanda shike na gaskiyar yakan saurare ni”. (Yahaya 18:36 – 37). Dole ne Musulmi ya koyi yadda zai fahimci abinda Yesu yace wa Bitrus: “ka maida takobinka a kubarsa, duk wadanda ke kisa da takobi, shi ne zai zama ajalinsu” (Matiyu 26:52).

Duk wanda ya zo wurin Yesu zai sami sakewa” mai girman kai zai zama da kaskantar da kai zama da kaskantar da kai, malalaci zai zama mai himma wajen aiki, mai tsatstsauran ra’ayi zai zama mai tawali’u, kuma azzalumi a gida zai zama mai yi wa kowa hidima. Bangaskiya cikin Yesu na canza mu mu zama Kaman Ubanmu cikin sama. Yayinda muke adu’a: “A tsarkake sunan ka”, wannan roko yakamata ya kawo babban sauyi a zukatanmu, a Ikklesiyunmu da kuma cikin sabobin tuba. Samun sakewa na ruhaniya dole ne ga Krista cikakke. Wannan za a iya samunsa cikin iko da kaunar Ubanmu (Roman 5:5) tawurin Ubangijinmu da mai cetonmu Yesu Kristi kadai.

8.03 -- Kasancewa Ko Rabuwa Da Iyali?

Mutane daga gabas ta Tsakiya da Musulmai dayawa basa rayuwa su kadai. Suna da kakkarfan dangankata da iyalansu, ransu da dabi’arsu. Suna raye tare da duka ‘yan ‘uwansu, suna bin ka’idodi iri daya, addini daya, kuma suna daukan nawayan juna. Iyali sukan taru su yanke shawara a akan aure, zuwa karatu, karban matsaya a gwamnati d/s. Mutanen da suke zaune a kasashen Larabawa da na Yahudawa sukan ji kamar sun bata in basa tare da iyalensu.

A manyan birane mutum yakan zauna shi kadai. A haukali yakan kwance kansa daga abubuwan da suka daure shi da danginsa. Saboda haka tunanin mutanen gabas sun fara canzawa daga “mu duka” zuwa “Ni kadai”. Wannan ya shafi yawancin musulmai. Amma dangantakansu da kauyensu ya fi duk abinda suke yi a birni karfi.

Har yanzu mutanen gabas basu bar dangantakansu na iyali ba Kaman mutanen Amerika da sassan kasan Turai. Har yanzu mutumin gabas, daya ne daga cikin danginsa. Masu shelar bishara sai su yi hankali sa’anda suke kiran musulmi shi kadai domin har yanzu basu kadaita ba, baya ganin kansa Kaman “Ni” amma yana cikin “Mu”. Baya iya yanke shawara shi kadai sai da tofa yawun iyali ko danginsa.

Dangi-Babban Matsalar da ke hana Musulmai su Zama Krista.

Al’adar zama tare na dangi shine babban matsala wanda ke hana musulmai zama Krista! Iyali baya yarda masa ya fita daga dangi. Babu yadda za a yi a kunyata dangi a kowane hali balle ma ma a ce dansu ya fandare ya kuma kafirta. In musulmi ya bi adinin kwaminisanci ko ya ki yarda da Allah, za a iya yin hakuri dashi a cewa ya rude ne. Amma wanda ya zama Krista ya shiga uku. Wani darikar Islama sun ce in wani dansu ko ‘yarsu tayi ridda wannan na runa alama cewa uwar mazinaciya ce! Ko ta halin kaka sukan yi kokarin su sa kowa ya zama mai biyaya cikin al’amarin addini da na zaman gari.

Duk wanda yake da marmarin kai wa musulmai bishara yakamata ya ziyarci iyalinsa in zai yiwu, kada ya raba shi da su. Bari iyaye da ‘yan’uwa su ga cewa wadannan sabobin abokan masu gaskiya ne da aminci. Yana da muhimmanci kada mu ci amana. ‘Yan darika, ‘yan siyasa, ‘yan daba ma suna kokarin jan ra’ayin mutane.

A rubuce yake a Kur’ani cewa kada musulmi ya yi abokantaka da Krista ko Yahudawa don ba za su basu salama ba sai in sun ja ra’ayinsu (sura al-Ma’ida 5:52 – 57 d/s). Amma kuma cikin Kur’ani dayan an rubuta cewa cikin magabtan musulmai, Krista ne suka fi kirki don suna nuna tausayi kuma basu da girman kai (sura al-Ma’ida 5:82).

Bisa ga dandanawa a fannin kai wa musulmai bishara, yawan cin lokaci dangi guda kan ki yarda a yi musu bishara. Duk da haka sai mu yi kokari don wani lokaci akan sami iyali dungum da sukan tuba su karbi Yesu!

Zafin Rabuwa Da Dangi

Sa’anda iyali sun ga daya daga daga cikinsu na karanta Baibul, ba za a hana shi wannan karatu da nazari ba amma za a yi hakuri dashi zuwa wani lokaci. A zamanin kimiyya da sadarwa bai kamata mutane su zama da jahilci ba, amma kada su gaskanta abinda suka karanta! Sun yarda cewa samun ilimi na Baibul na da kyau amma an haramta kowane irin dangantaka na kud-da-kud da addinin Krista.

Da zara ya bayyana a fili cewa matashin na da sha’awa sosai na bin Kristi da Bisharansa, akan roki kawunsa yayi Magana dashi don ya dawo hanyar Islama, ya gargade shi ya ma yi masa burga, in bai yi alkawarin barin abinda ya sa a gaba ba.

In wannan gargadi bai iya juya shi ba sai a fara bashi horo. Za a iya hana shi kudin aljihu, a boye tufansa, a hana shi zuwa makaranta, ana iya dukansa, a yi masa fada, a boye wasikunsa ko kuwa a ba wa mai kawo wasiku toshiya don kada ya rika kawo masa. Abokansa da malamansa za a sanar dasu don su matsa masa wani lokaci har da duka. A kulle ‘yan mata a kananan dakuna a hana su ruwa da abinci kuma kullum ana yi musu duka don a tilasta su su yi biyaya. A matsanancin hali ne aka kai sabon tuba wajen ‘yan sanda a yi masa shaidan zur wanda kan sa ‘yan sanda su azabta mutumin babu tausayi har sai in an gane cewa laifin ya shafi addini ne kawai ba laifin sumoga, ludu ko kuwa cin amanar kasa ba. In iyalin wanda ya tuba sun yi burgar kashe shi bai kamata yayi wasa dashi ba. Duk wadannan abubuwa akan yi su cikin kiyayya, dacin rai da tsoro. Manzo Bulus ya rubuta: “Da gaske an a kisan mu muddar yini, amma cikin dukan wadannan al’amura mun fi gaban masu nasara tawurin wanda ya kaunce mu”.

Rai Madawwami Ba Shi Da Iyaka

Saboda a nuna yada masu bada shawara baza suyi wasa da wannan al’amari ba, mun bada wannan labari na abinda ya taba faruwa:

A kasar Bangladesh wani Mishanare ya sami matsowa kusa da yara matasa ‘yan Shekaru 16 zuwa 18. Wadansu sun karbi Kristi.. Mishanaren nan daya ji sh’awan wannan abu sai ya shawarci matasan dasu: “Je gida ku fada wa iyalenku cewa Yesu ya baku rai madawwami”!

Nur al-Alam yayi biyaya, daya tafi gida sai ya cewa Ubansa: Baba, Yesu ya bani rai madawwami! Uban ya harari dansa ya tambaye shi: “Waya baka mene”? Yaron ya amsa: Dan Maryama ya sa ruhunsa da kaunarsa a cikin zuciyata”. Nan ne uban ya kira yayunsa: ku kawo tsumangu”! Kuma ya umurce su da su yi ta dukansa har sai iskokin sun rabu dashi. Nur al-Alam daga bisani ya fada “sun yi ta tambaya: “Yanzu iskokin da sun shige ka sun rabu da kai” Dan ya amsa: “Baba Rai madawwamin da ke cikina ba iyaka. Ba zai taba bari na ba” Uban ya sake kiran ‘yan ‘uwansa: “ku kawo wukaken”! Suka yayyage tufafinsa suka tsatstsaga jikinsa da wukake daga wuyansa har zuwa sawayensa. Yaron ya tsaya a gabansu yana zubar da jini, Uban ya sake zuwa ya tambaye shi: Yanzu ka sami ‘yanci daga ruhun madawwamiyar yaudara? Yaron ya amsa yana hawaye: “Baba, zaka iya kashi ni. Amma zan rayu har abada. Rai madawwami cikin Yesu ba zai taba bari naba”. Cikin fushi uban yace a kawo masa barkono da gishiri! Sun shafa wannan barkono da gishiri a duka jikinsa. Don zafi yayi kururuwa. Suma sun yi kuka tare dashi don suna so su cece shi daga gidan wuta. Basu iya daure ganin abinda ke faruwa basu dukansu suka bar shi a cikin dakin kwance cikin barkono da gishiri. Bayan wani lokaci yaron ya iya fita cikin ruwa ya wanke kansa, ya sami dan kwalekwale ya haye inda mishanare yake ya kwankwasa kofa ya jira.

Sa’anda mutumin ya bude kofa ya ga yaron jina-jina a gabansa, sai ya gigice yace: “Ba zai yi kyau ka shiga gidana ba don na tabbata suna bin ka a baya. Ka tafi gaba zuwa gidan wani amintaccen Krista, zasu karbe ka”. Ya zama ma yaron tilas ya shiga duhu shi kadai ya tafi.

Kada mishanarai su yi amfani da sabobin tuba don ribato wadansu a hanyar turawa ba, amma dole su gane yanayinsu, su sha wahala tare da su su kuma dauki nauyinsu.

Ana Bukatar Hikima Da Aminci

Bai kamata nan da nan a kira sabon tuba ya bada shaidar tubansa a fili ba; jariri baya iya tafiya ko yin Magana ba. Bari sabon tuba ya girma cikin maganar Allah, hikima, adu’a da kauna, sai in shi – da kalmomin da suka dace, a lokacin daya dace – zai iya furta bangaskiyarsa. Yawancin lokaci baya iya fada wa iyalinsa a fili, amma zai iya yin shaida tawurin sabon rayuwarsa, hidimarsa, kirkinsa da adu’aoinsa wadanda zasu nuna cewa sabon abu ya shiga zuciyarsa.

Kada sabon tuba ya bar gidan ubansa don an matsa masa lamba. In an fidda shi a kofar gida ya bita bayan gida ya shiga. Babu wanda ya fi kaunarsa fiye da iyayensa! Yin aikinsa sosai babu wani surutu da ban girman da yake ba iyayensa sukan yi Magana fiye da kalamai da sukan kawo kiyayya ne da fushi. Ko ta yaya da zaran an ga rayuwarsa na matukar hatsari, sai mai bashi shawara ta ruhaniya, kungiya ko Ikklesiya inda ya tuba, a karbe shi, a tsare shi kuma a kare hakkinsa. Amma a yi hattara akan bada irin wannan taimako ga yaran da basu balaga ba don hukuma bata yarda da haka ba.

Za a iya samun burgar sakin aure a wajen ma’aurata idan namiji ko mace ta bada gaskiya ga Kristi. Ridda daga addinin Islama yana daya daga cikin abubuwan da zasu iya sa mace ta nema a sake ta. A irin wannan yanayi, duka ‘ya ‘yan matan ne. In maigida ne ya saki matarsa don ta bada gaskiya ga Kristi, ‘ya ‘yan nasa ne, kuma za a iya a koreta daga gidan. A nan zamu iya ganin yadda wadansu iyaye mata suke shan wahala don Yesu a kasashen Musulunci.

Masu Tserewa Ta Barauniyar Hanya.

Ba safai ba Musulmai kan azabta su kuma kashe daya daga cikin iyalinsu. Kashi biyu bisa uku na Musulmai masu budadden zuciya ne kuma basu damu sosai ba akan zancen addini. Amma don kada a bata musu suna su rasa karbuwa a cikin al’umman Musulmai ba zasu iya ajiye maci amanar addininsu ba sukan yi kokarin rabuwa da wanda yayi shirka, in abu mai yiwuwa ne sai su tura shi kasar waje.

Amma daya bisa uku na Musulmai kan husata da duk daya daga cikin danginsu wanda ya karbi Yesu. Dole ne su horeshi don neman su cece shi kokuwa su halakad da shi. Duka sashe biyu kan zama da ciwo in dayansu ya zama Krista amma, ‘yan kalila ne suna shirye don kashe wanda yayi ridda.

A wannan zamanin, sabobin tuba wadanda rayuwansu na cikin hatsari basa jinkirtawa, amma sukan tsere kafin a kashe su. Sukan boye wurin abokai kokuwa su gudu zuwa wadansu kasashe suna moran wadansu sunaye.

Sabon tuba wanda bai riga ya sami ‘yanci kansa ba, wanda yana rayuwa cikin dangi yakan zama da burin ribato ‘yan ‘uwansa zuwa ga Yesu bayan daya karbi ruhun kauna ta Kristi sa’anda ya tuba. Amma wannan yakan zama shine dalilin da sukan kishi kuma su tsane shi (Yahaya 16:1 – 4). Duk da haka sabobin tuba sukan dafewa shaidar Manzo Bulus tawurin bangaskiya wanda ya kalubalanci mai tsaron kurkuku, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, zaka sami ceto, kai da iyalinka” (Ayukan Manzanni 16:31).

Shin, me yasa muke tsunduma sabobin tuba cikin irin wannan wahala: “In bin Yesu yana kawo irin wannan matsananciyar wahala, bai kyautu mu bar Musulmai su cigaba da bin addinin suba? In mutum yana fadin haka, to, shi da kansa bai fahimci Muhammadu ba kokuwa Kristi. A cikin Islama babu ceto, babu tabbacin gafarar zunubai, ba fansa, babu salama, babu Ruhu Mai Tsarki, ba rai Madawwami. Zama Musulmi in mutum bashi da Yesu Kristi shi batacce ne kuma matacce a ruhaniya! Dan Allah ya ce, “Nine hanya, Nine gaskiya, Nine kuma rai. Ba mai zuwa wurin uba sai tawuri na (Yahaya 14 :6). Babu wata hanyar gaskiya zuwa wurin Allah illa ta hanyar giciye! In zaka so hana sabobin tuba shan wahala kana Kaman Bitrus ne wanda yaso ya hana Yesu zuwa giciye (Matiyu 16:22 – 23). Amsar da Yesu yaba Bitrus ya kamanci duk wadanda suke so su hana sabobin tuba shan wahala.

A bayyane Ubangijinmu yace, “kowa ya bar gidaje, ko ‘yan ‘uwa mata, ko ‘yan ‘uwa maza, ko uwa, ko uba, ko ‘ya ‘ya ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu dari, ya kuma gaji rai madawwami”. (Matiyu 19:28 – 30; Markus 10:29; Luka 18:29). Yesu ya cigaba da cewa, “Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye dani, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko ‘yarsa fiye dani, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma bai dauki giciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba. Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi ya yi” (Matiyu 10:37 – 38; 16:24 – 25; Luka 9:23 – 26; Yahaya 12:25).

Abu mai sauki ne yin Magana ko kuwa a rubuta wa wadansu wadannan kalmomin, amma aikata su da wuya. Saboda haka nawayar karban sabobin tuba da aka tsananta musa cikin iyali na ruhaniya ya rataya a wuyanmu. Zamu kula dasu har sai in sun iya kulawa da kansu.

Lokacin da sabon tuba yana girma cikin ruhaniya kuma yana kokarin fita daga cikin kangin danginsa, yakan fuskanci jarabobi na musamman wadanda yana da bukata yayi nasara akansu ko da shike shi sabon shiga ne.

Wane Wahayi Ne Na Gaskiya Daga Allah?

A matsayin Musulmi sabon tuba, ya zaci cewa duka Litattafan da aka saukar kamar Attaura, Zabura, Linjila da Kur’ani an samo su ne daga, Littafi na ainihi a sama kuma sun yarda da juna. Amma jim kadan sabon tuban zai ga bambanci sosai tsakanin Baibul da Kur’ani. Linjila ta shaida cewa Kristi Dan Allah ne sau 50, Kur’ani ya musanci haka sau 17. Kwanaki na karshe na rayuwan Yesu cikin jiki sun nuna shan wahala da mutuwan sa. Amma Kur’ani yace, “…basu kashe shi ba kuma, amma an kamanta shi ne a gare su” (sura al-Nisa’ 4:157). Linjila ya bayyana sau 187 cewa Allah uba kuma Ubanmu ne. Kur’ani kuwa yace Allah ba Uba ba ne kuma babu mai kamarsa (sura al-Ikwas 112:1 – 4). A cikin Bible mun sami koyaswa akan yin auren mata daya-daya, game da hana sakin aure, gafarta wa makiyanka laifofinsu, da kuma game da Ruhu Mai Tsarki wanda yake zaune a cikin mabiya Kristi. A cikin Littafin Musulmai kuwa, Allah ya yarda a yi auren mace fiye da daya, maigida na iya sakin matarsa lokacin da ya ga dama, ya halarta mutum ya rama muguntar da aka yi masa ko kuwa ya biya kudin jini,kuma bashi yiwuwa.

Mutum ya Karbi ruhun Allah-Allah kadai ne mai girma! Duk sauran halittu bayinsa ne har ma da Yesu da Ruhu Mai Tsarki.

Sabon tuba yakan fuskanci wannan tambaya: Wane Littafi ne wahayi na gaskiya, wanene ne jabu ko kuwa karya? Wannan tambaya ba yakan zo daga waje ba, amma daga cikin zuciyarsa ne. Kada mu bashi amsa kai tsaye shi da kansa yana bukatar gane gaskiyar, saboda ya iya yin tsayayya da harin da iyali ko dangi zasu kawo masa. Dole ne mu goyi bayansa da adu’a, mu jagorance shi da ayoyi na Littafi Mai Tsarki da zasu taimaka masa, mu tsaya tare dashi cikin wahalunsa, har sai ya gane da kansa tawurin Maganar Allah cewa: Baibul ne kadai Maganar Allah! Yana cike da iko da rai. Kur’ani yaudare ce, jabun wahayi ne daga ruhun da ke gaba da Baibul ne.

Zunuban Da Ba A Gafarta Su

Wata jaraba zata sake iya shafan rayuwa ta ruhaniya ta sabon tuba. Kur’ani ya nuna cewa akwai zunubai guda uku da baza a taba gafarta wa mutum ba in ya aikata su:

An la’anta duk wanda ya hada Allah da wani (sura al-Tawba 9:29).

Duk wanda ya bar Musulunci ya zama Krista za a la’anta shi sau uku (sura al-Baqara 2:161).

Fushin Allah na kan duk wanda ya kashe musulmi a wata manufa sai dai in ramako ne yayi (sura al-Nisa’ 4:93).

Duk wanda ya kira musulmi don ya karbi Yesu, yana kiransa ne daya aikata a musulunce zunubai guda biyu wadanda baza a taba gafartawa ba wadanda suka yi daidai da zunubin saba wa Ruhu Mai Tsarki a cikin Linjila. In za a cewa Krista ya saba wa dayantakan Trinity Mai Tsarki, ba zai yi wata-wata ba zai ki. Sabon tuba ma yana da irin wannan matsalar a cikin sa wanda yana bukatar cin nasara da shi. Dole ne ya yarda ya saba wa abinda daya tsarkake, saboda ya sami Kristi da rai madawwami. Kada mu matsa masa ya yanke shawara da sauri, amma mu taimake shi da adu’a da kuma shawara, kuma mu taimakeshi ya kahu da samun tabbaci cikin maganar Allah (Romawa 8:14 – 16; I Korintiyawa 12:2 – 3).

Ga musulmi akwai gargadi a Kur’ani na cewa duk wanda ya bar Musulunci zai rasa ladan ayukansa nagari kuma bashi da abinda zai nuna a ranar Shari’a inda za a gwada zunubansa (sura al-Khaf 18:105; al-Zumar 39:65 d/s). Amma Kristi ya bashi tabbaci cewa: “Alherina ya isheka! Ayukan ka basu isa su baratar da kai ba. Jini na da na zubar ne adalcin ka”!

An Yanke Hukuncin Kisa

Wani abu mai daci da dole sabon tuba ya hadiye shine yanke hukuncin da Shari’a Musulmunci tayi na cewa duk wanda yayi ridda dole ne ya “mutu” (sura al-Baqara 2:217). Abin mamaki shine Kur’ani bai ce dole ne a “kashe shi” ba. Wannan zahirin gaskiyar ya sa masana Shari’ar Musulunci suka yi bincike cikin hadisai ko Muhammadu yayi wani furci akan kisan wanda yayi ridda. Amma tunda kashe musulmi don dalilin da ba a same shi a bayyane a Kur’ani ba shi halarta ba, sai Malamai suka nemi hujja tawurin yarda da hada ra’ayin masana Shari’a. Sun sami bambancin ra’ayi akan tsawon lokacin da ya dace a kulle wanda yayi ridda a kurkuku don ba shi lokaci yayi tunani kafin a kashe shi Wadansu sun ce kwana uku, wadansu kuwa wata daya, a wannan lokaci ne za a sake koya masa Musulunci saboda a dawo dashi tushensa. In ya ki amsa kira na dawowa musulunci, sai a kashe shi.

Yawancin kasashen Musulmai kuwa basa kisan sabobin tuba! Dokokin neman ‘yancin ‘yan adam na duka duniya basa goyon bayan Shari’ar Musulunci. Saboda haka, kasashen Musulunci masu neman ‘yanci sukan ki aikata wannan doka ta Musulunci. Sukan nuna aya guda daya a Kur’ani wanda ke maganan mutuwar sabon tuba kadai ba “kisansa” ba (sura al-Baqara 2:217). “Allah zai hukunta shi kuma zai bar shi ya mutu wata ran, ba a ba gwamnati ikon kashe shi ba”, a cewan wadansu masu bada shawara a fannin Shari’a.

Masu halin rikau a cikin Musulmai kuwa, tunaninsu daban ne. Sukan nema a aiwatar da shari’a gaba daya, a kashe wanda yayi ridda babu nuna tausayi. Don wannan dalili ne sabobin tuba cikin Kristi wadanda ke fuskantar tuhuma akan kullesu a kurkuku, a bincikesu, a tsananta musu, kuma a rikesu na wadansu watanni, har sai in ‘yan siyasa ko shugabannin wadansu kasashe suka sa baki sai a sake su. Sa’anda suna a tsare, akan yi musu alkawarin in sun koma musulunci sun furta Kalmar shahada sau biyu, za a sake sun an take. Wata mace da aka kulle ta a kurkuku ta ce, “Na gwammaci a tsare ni tare da Yesu Kristi a maimako lura da ‘ya ‘ya na ba tare da Kristi ba”. Sa’anda maigidanta yayi Kalmar shahada sau biyu don ‘ya’ yansa, sai suka yi masa dariya suka ce, “karya kake yi cewa ka koma Musulunci don ‘ya ‘yanka. A cikin zuciyarka kai Krista ne. Saboda haka ba za a sakeka ba”.

Krista da yawa a kasashen Yamma da Koriya basu sani a Shar’ance abinda ake nufi da Musulmi ya zama Krista ba. In da gwamnati bata kashe mai ridda ba, danginsa masu halin rikau ya zama musu dole su cire wannan mugun iri tawurin kashe shi. A Saudiyya da kuma kasar Iran, harma da Fakistan da kuma kasashe masu rike da ra’ayin mazan jiya, akan yi wannan kisa ne a bainin jama’a. Sarkin Moroko mai barin g ado, Hassan II, Amnesty International (kungiya masu neman ‘yancin ‘yan bursuna) sun taba yi masa tambaya, ga amsar daya basu: “A kasar mu muna da doka ta asali: Allah, sarki da kuma kasar. Idan wani ya zo da cewa akwai wani addini wanda yafi Islama, zamu kaishi asibitin kwararru a gwada shi ko yana cikin hankalinsa. In yana cikin hankalinsa ya kuma cigaba cikin kafircinsa dole ne mu hukunta shi”.

Ko Duka Krista Musulmai ne?

Wata jaraba ta wayo da zata iya fuskantar sabon tuba wanda zai iya zuwa daga bangaren Mishanarai masu son mutane. A Kur’ani zasu ga ayoyin da ke cewa duka mabiya Kristi Musulmai ne (surorin al-Imran 3:52; al-Ma’ida 5:111). Wadanda basu da zurfi a sanin Kur’ani basa gane cewa wadannan ayoyi guda biyu tarko ne da Muhammadu ya dana wa tawagar Krista daga Arewacin Yemen. A cikin wadannan ayoyi ya sa manzanni Krista sun furta cewa su Musulmai masu nagarta ne, saboda Bishof da sarkin Wadi Nadjran su fahimta: In manzannin Yesu musulmai ne-to, muma ai musulmai ne-Krista! Sa’annan zamu yi zaman salama ba za tsananta mu ba. Amma shi sarki da Bishof masu saurin fahimta ne cikin ruhu basu fada cikin wannan tarko ba. Sun cigaba da kasancewa Krista, bayan ‘yan Shekaru na fatattakasu an koresu daga kasarsu. A yau irin rada ta Muhammadu ta kawo jarabtawa na yaduwa a duka kasashen Musulmai kuma: “Ba dole ne sai kun zama Krista a fili ko a boye ba. Ku gaskata Allah da Muhammadu! Zaku iya zama Musulmai da Krista a lokaci daya. Kaman yadda akwai Yahudawa da suka gaskata Masihu, haka ma za a iya samun Musulmai Krista!

Wadannan annabawan karya basu san Islama ruhu ne mai gaba da addinin Krista ne (I Yahaya 2:21; 4:1 – 5). Kuma yana misali na karkataccen wahayi daga bakin mala’ikan daya fadi daga sama. (Galatiyawa 1:8 – 9). Musulmai daurarru ne tare cikin wani ruhu kuma suna bukatar ‘yanci tawurin ikon Kristi. In kana tsammani zaka yi wa Musulmai bishara ba tare da gaya musu zance Dan Allah giciyayye ba, kalmomin Kristi zasu Shar’anta ka a cikin Matiyu 10:32 – 33; 16:23 – 25; Romawa 1:16 – 17; I Korintiyawa 1:18 – 24 d/s).shugabankasar Sudan mai rasuwa wato Turabi yayi amfani da wadannan ayoyi biyu daga Kur’ani ya sanar cewa duka Krista na Sudan duka Musulmai ne da kuma cewa Krista maza zasu iya auren ‘yan matan Sudan Musulmai. Ta haka ya bi sawayen Bal’amu wanda ya shawarci Balak ya sa mutanensa su gauraya da Isra’ilawa tawurin aurayya. Tawurin haka al’adun dangin su zasu mamaye na Isra’ilawa a cikin ‘yan Shekaru kadan (Littafin Kidaya 31:16; II Bitrus 2:15; Yahuza 11; Wahayin Yahaya 2:14). Malaman Shari’a na kasar Saudiyya sun soki Turabi akan alkiblarsa da ke gaba da ka’idodin Musulunci.

Zagon Kasa-Kuskure ne?

Manufan masu koyar da bishara ta zagon kasa a bayyane yake. In sabon tuba ya bayyana a musulmi kuma ya kasance a musulmi, amma shi kuma Krista ne a lokaci guda, ba zai sha tsanani, wahala ko mutuwa ba, kuma ba zai kawo wa Ikklesiyarsa matsala ba, hatsari ko kuwa sadakarwa. Amma wadannan Malamai basu yi la’akari da cewa mutum ba zai iya gauraya ruwa da wuta ba, kuma dare na guje wa rana. Magariba bata kasancewa din-din-din.

A Misrah, Mishanare mai aikin zagon kasa ya ribato wani hafsa na yin aiki asirce domin Yesu kuma ya tabbatar masa da cewa zai iya kasancewa Musulmi sa’annan kuma Krista a lokaci guda. Wannan hafsa ya ji dadin wannan domin ta wannan hanya, kofofinsa na saduwa da manyan mutane a bude suke. Shi kuma ya ribato Musulmai da yawa cikin wannan shirka. Amma bayan Shekera daya da rabi sai ya ji Kaman shi jemage ne ba amintaccen Musulmi ba, ba Krista na gaskiya ba, sai ya nema a yi masa baftisma a wata Ikklesiya. Bayan wannan ‘yan ‘uwansa sun tuhume shi da laifin yin ridda daga Musulunci kuma sun tsanantshi da irin azaba wanda ya yi wa wadansu a da don dawowa da su cikin Islama. Amma shi bai koma da baya ba, ya cigaba da aminci cikin Yesu, da taimakon abokai ya iya tserewa zuwa kasan ketare.

Baya dan lokaci kadan, duka kungiyar da ke bi asirce ta bayyana kuma duka an kame su aka kulle cikin kurkuku. Jaridu sun yi rubutu da fushi kuma sunyi musu ba a suna cewa: “Kyarketai na Krista cikin fatun tumaki na Islama suna kokarin lalatar da musulmai da ke cikin jahilci”! Iyalai wadanda ba ‘yan kasan Misrah ba wadanda aka tsare, sun sami ‘yanci da taimakon ofisoshin jakadun kasashen su bayan ‘yan makonni kadan, an kore su daga Misrah.

Wadannan abokai na kirki watakila basu taba la’akari da cewa an fahimci aikin bishara a tsakamin Musulmai a matsayin lalata kuma da tashin haukali ne ba. A fadin Kur’ani, wannan laifi na da tsanani fiye da kisa (sura al-Baqara 2:217). Duk wanda ya kawo hargitsi a gari hukuncinsa kisa ne ko a rataye shi. Za a iya yanke hannunsa da kuma kafarsa ko kuwa a koreshi daga kasar (sura al-Ma’ida 5:33). A cewan Kur’ani da Shari’an Musulunci, aikin bishara laifi ne daya cancanci kisa. Wadanda suke yaudara da wadanda aka yaudare su, hukuncin su kisa, ko da ma’aikata ne Krista daga wata kasa ko wadanda suke rayuwa a matsayin Musulmai Krista.

Ma shaidin Kristi wanda yake ado da tufa irin na Musulunci kuma yana yi Kaman shi musulmi ne ana daukan shi a matsayin musulmi wanda yayi ridda ne kuma yana da hukuncin kisa. Bugu da kari an dauke shi a munafuki, mai ha’inci da bidi’a. A cewar Shari’a za a iya kashe shi nan take.

Yawancin lokaci Musulmi ba yakan san dokokin Shari’a filla-filla ba. Duk wanda yake yin hidima tsakanin Musulmai kada yayi saurin jagorantar su su tuba a sama-sama ba, kuma kada ayi saurin yi musu baftisma. Yakamata sabon tuba ya zama da cikakken sanin abinda ake nufi da mutum ya zama Krista. Girma cikin ruhaniya ya fi rahoton da za a bayar na yawan mutanen da aka yi musu baftisma muhimmanci. Inganci ya fi yawa.

I dan mutum yayi tunani game da ire-iren matakai wadanda musulmi kan bi don fito wa daga al’umman musulmi, dangi da iyali, zai iya fahimta cewa sabon tuba zai iya fadin wadannan kalmomi na Bulus Manzo.

Saboda kaine ake kashe mu yini zubur, An lasafta mu kamar tumakin yanka. Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, harm un wuce ma a ce mana masu nasara, tawurin wannan daya kaunace mu. Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko malaiku, ko al’amuran Yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai kowace irin halitta ma, ba zasu iya raba mu da kannar da Allah ke yi mana twurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba. (Romawa 8:36 – 39).

8.04 -- Karban Sabobin Tuba Cikin Ikklesiyoyi

Daya daga cikin manyan matsaloli da Musulmai da suka karbi Kristi suke fuskanta shine na karbansu cikin Ikklesiya. Yawancin Ikklesiya ta Otodoks, Kalolika da Furotesta a Asiya da Afirka wani lokaci har ma a Turai basa son karban sabobin tuba daga Islama. Akwai dalilai da dama da suka haddasa haka:

  • Wadansu Musulmai suna neman wani taimako ne na kudi kuma suna shirye su canza addininsu Kaman riga don kudi-muddin kudin na nan, suna cikin wannan addini. “Wanda ya bada abinci, ra’ayinsa ake bi” Wannan ka’ida mai ci ne a duniyar Islama.
  • Sau da yawa akan sami yarinya da ta bada gaskiya ga Kristi ta kawo saurayi musulmi a yi masa baftisma, saboda ta aure shi sun sani ba a yarda da auratayya irin wannan ba. Irin wannan niyya yayi daidai a garesu, amma dangi, Shari’a da mutane suna gaba da shi. Irin wannan tuba makirci ne, kuma zai iya kawo matsala.
  • Bisa ga ka’idodin Islama don ‘yan tsiraru, kowane aikin bishara tsakanin Musulmai an haramta Krista ‘yan kasa yi (surorin al-Baqaar 2:217; al-Ma’ida 5:33). Ikklesiyar da ta bar daya daga cikin Membobinta yayi wa Musulmai bishara za a ba ta horo ko kuwa a rufe ta. Zamu iya fahimta cewa Firistoci, Fastoci da Bishof-Bishof sukan yi matukar kula su tabbatar cewa babu memba nasu wanda zai yi bishara a fili a tsakanin musulmai kuma daga helkwatansu ne aka umurce su, domin akan wannan gwamnati zata iya rufe Ikklesiyar.
  • Kungiyoyin Bishara na kasa da na waje wani lokaci sukan dauki musulmai masu Sha’awa zuwa Ikklesiya saboda Fasto yayi musu baftisma kuma ya karbesu a sabobin tuba. Sukan yi mamaki cewa wannan dattijo baya nuna sha’awa ba ko yakan ki karban wannan sabon zuwa. An yarda da wannan don bai kamata kungiyar Bishara ta yi aiki ba tare da sanin wadansu dattawa ba wadanda zasu goyi bayan aikinsu. Yakamata a sanar da wadannan dattawan don goyon bayan wannan kungiya cikin adu’a da kuma shiri don karban sabobin tuba cikin iyalensu don tsare su daga hari, kuma da jagorantarsu zuwa matakai na gaba.
  • In tsuntuwa tana so ta saka kwai takan yi sheka ne da farko, ba kwai ba! Duk abokai wadanda ke shirye suyi aikin bishara a kasashen Musulmai abinda zasu yi da farko shine gina kungiyoyin adu’a a cikin Ikklesiya da kuma waje, wadanda zasu goyi bayan hidimar da kuma daukar nawayar duk bukatu. In mutum ya tara irin wadannan kungiyoyin adu’a zai ga nasarar aikin fiye da ‘yan bishara dadi wadanda bad a jimawa ba zasu bar wurin aikin. Akwai mutane kima a cikin Ikklesiyu da suke da marmarin kai bishara ga wadanda ba Krista ba. Dole ne kayi adu’a don samunsu.

Zumunci Tare Da Jama’an Ubangiji

Idan musulmi, lokacin samun canji na ruhaniya da kuma bayanda aka koreshi daga dangi da kuma al’umman musulmi in yayi kokarin kusantan zumuntar masu bi, ko Ikklesiya ko Krista, Firist da Fasto, yakan gigice. Yakan ji kamar: basu yarda da ni ba! Suna tsammani ni maroki ne, ko kuma ina so in yi lalata da daya daga cikin ‘yan matansu ne, ko suna tsammani ni dan leken asiri ne. Yakan ji Kaman an zuba masa ruwa mai sanyi ne sa anda yana shiga kofar addinin Krista!

Tabbas, Musulmai suna amfani da tsarin kalmomi dabam-dabam a rayuwan yau da kullum fiye da yawancin Krista kuma idan sun yi amfani da wadannan kalmomin, zai zama suna dauke da ma’anoni dabam-dabam.

Rayuwansu da adonsu dabam ne da na Krista, yadda kowa yakan bambanta su kenan. Krista da musulmai suna sane da wannan bango wanda ba a gani.

Abu na farko da sabon tuba ke bukata shine yarda, fahimta da kauna! ‘Yan ‘uwa cikin bangaskiya maza da mata masu adu’a su zo su same shi, su yi Magana dashi, su gayyace shi zuwa gidajensu su sa shi ya ji cewa: ka zama daya daga cikin mu dukan mu mun zama daya! Amma kada ayi irin wannan gayyata a gidan da akwai ‘yan matan da suka isa aure, domin irin wannan gayyata zai iya kawo rashin fahimta.

Ikklesiya ne zai zama sheka inda sabon tuba zai ji yana gida zununta tare da mabiya Yesu zai zama masa sabon “iyali” wanda yake bukata bayan an koreshi daga danginsa. Kaman yadda kai bishara na da Muhimmanci haka ne shirya mutanen Allah don karban sabon tuba.

Kada dattawa da Fastoci su karfafa kawo sabon tuba akan bagade ko dora shi akan wani abu mai bisa don bada shaidar bangaskyarsa. Ba zai zama da amfani a sa sabon tuba inda zai ji kamar shi mai girma ne da Muhimmanci-wannan zai kumburar dashi Kaman balo-balo. Bari a bashi kananan ayuka wadanda zai zama Kaman sauran mutane. Kamar yadda muke, shi ma mai zunubi ne wanda ya sami barata tawurin alherin Allah.

In Iyalin Krista ta karbi sabon tuba, suna da nawayar kare shi. Ana darejata baki a tsakanin Krista da Musulmai na Gabas ta tsakiya. Akwai wani dan’uwa wanda ya taba tsare kofa ya hana ‘yan ‘uwansa masu daukan fansa kashe wani dan’uwa. A tsaye a kofa ya gaya musu, sai dai in kun kashe ni kafin ku iya samun wannan mutum. Sun tafi basu iya cim ma burinsu ba don al’adar Larabawa ta karban baki.

Zaka Yi Zuffa Kafin Ka Ci Abinci

Idan Musulmi ya zama Krista kuma yana zaune a inda Musulmai suke, yakan rasa aikinsa domin akan dauke shi a wanda Allah, Mala’iku da Musulmai suka la’anta (sura al-Baqara 2:16). A garesu ya kazantu (sura al-Tawba 9:28). Babu Musulmin da zai yi zumunci da wannan Maciyin alade da mashayin giya balle a bashi aiki!

Yayi kyau Fasto ko jagorar bishara ya hanzarta ya nema wa sabon tuba aiki. Ko da shike abu mai kyau ne a gayyaci sabon tuba zuwa gida don cin abinci. Daga bisani, wannan kan zama da kaskanci. Za a kuma iya ba sabobin tuba ‘yan kyaututtukan kudi amma musulmi mai martaba wannan zai zama masa abin kunya! Su ba maroka bane, amma ‘yan ‘uwa ne maza da mata. Abinda suke bukata shine aiki mai kyau ko koyon sana’a. Wadansun su sai an koya musu yin aiki sosai.

Wani Fasto ya sa anyi wa Ikklesiyarsa Fenti sau da dama a Shekara guda don ya samar wa sabobin tuba aikin yi. Ya so ya ga ya taimake su ko ta halin kaka. Tawurin haka yasa su sun ji dadin cin halal dinsu. Wadansu Fastoci sukan basu aikin Faskare, noma, sharan gida, aikin masinja, aiki da kaken rubutu, juya litattafai, sayar da Litattafai da sauransu, saboda a basu aiki kada su zama Kaman maroka.

Wadansu sabobin tuba basu da wata sana’a ko kuwa basu gama makaranta ba. Wadansu ‘yan mata suna bukatar horaswa akan dinki, samari akan konfuta, ko direban tasi kokuwa kudin agaji don kamala karatunsa. Duk wadannan na bukatar kudi. Kada a bada wadannan kudade kyauta ba, amma a bada su rance. Da farko, kada a bada makudan kudi da yawa. Sai idan an iya biyan kananan kudade cikin aminci, sa’annan za a sa zuciya a biyan manyan kudade in an karbe su”. Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu” (Luka 16:10).

Akwai Lokacin da wani Musulmi ya zo wurin masu bugawa da sayar da Baibul (wato Baibul sosaiti) a wani garin musulmai ya ce a bashi Baibul ya sayar a kasuwa. Lokacin da mai sayarwa ke shakka, sai musulmin yace: ka gwada ni da guda biyu kadai, ni zan kawo maka kudin guda daya, sa’annan kudin dayan zai zama ladana”. A wannan ranar ya kawo kudin wanda ya sayar ya kuma karbi Baibula hudu don ya sayar. Bayan kwana biyu ya kawo kudin Baibula biyu ya sake harban takwas. Ya zama da aminci akan kudi kadan, wannan yasa an iya amincewa dashi an bashi 16 har 20 inda ya sayar da Baibula inda bashi yiwuwa Krista su kai Baibul.

Sa’anda za a nemi aiki don sabon tuba yakamata a sami kungiyar adu’a da zata goyi bayan kungiyar bishara. Tunda yawancin masu goyon bayan cikin adu’a suna aiki, za su iya sanin wuraren da ake bukatan ma’aikata.

Aikin bishara a tsakanin Musulmai baya bukatar bada shawara kadai, amma har da kulawa da bukatunsu. Bayan kungiyar dalibai na Makarantar Littafi Mai Tsarki da suka yi aiki a tsibirin Fort Lamy a cikin Tekun Indiya suka dawo da bakin ciki bayan aikin bisharan da suka yi bai yi nasara ba, sai wani matashi, musulmi daga tsibirin ya bayyana a kofar dakin daya daga cikin daliban bayan mako daya. Ya fada masa cewa ya tsinci daya daga cikin ‘yan takardunsu wanda aka yar. Don wannan sha’awa kadai masu tsatatsauran ra’ayi a tsibrin sun kore shi. Dalibin da aka zo dakinsa ya tambayi malaminsa: “Menene zamu yi da wannan matashi a yanzu”? Lokacin da ya bashi amsa “ka sami dan’uwa”, ya amsa nan da nan, “I, dan’uwa cikin ruhu”! Lokacin da aka tambaye shi menene zai yi in da’uwansa na jiki zai zo wurinsa neman mafaka, y ace”, zan bude kofar dakina sosai in gaya masa: “ Gado na gadonka ne, na bude wurin ajiyar abincina gareka”. Yayinda aka fada wa dalibin cewa wannan Musulmin da aka kora ba dan’uwansa na ruhaniya bane kadai amma dan’uwansa ne na kwarai wanda zai dauki nawayarsa sai ya sunkuyar da kansa cikin kunya domin ya sami fahimta cewa aikin bishara cikin Musulmai baya nufin hidimar ruhaniya kadai ta maganar Allah, amma ya hada da sadakar da abubuwan da muka mallaka.

Bai Kyautu Mutum Ya Kasance Shi Kadai Ba.

Duk matashi ko matashiya da ta kai Shekara 30 da haihuwa a kasashen Musulunci danginsa da abokansa zasu yi ta zarginsa ko ba lafiya ne. Wajibi ne kowane sabon tuba namiji ya auri wanda ta bada gaskiya cikin Kristi.

Musulmai da yawa sun dauki baftisma kamar tsarki ne wanda Musulmi kan yi kafin ya yi Sallah. Amma idan ya auri yarinya Krista abinda ya hadasu da danginsa da al’umman Islama ya yanke. Auren mace Krista na nufin kara zurfafa rabuwansa da Musulmai da yawa fiye da baftisma.

Abin takaici, yakan zama da wuya iyaye Krista su bar ‘ya ‘yansu mata su auri sabon tuba. Suna tsoron irin halinsa na Musulunci, watakila ya yi wa ‘yarsu duka. In kuma ya fadi Kalmar shahada sau biyu cikin fushi, zai koma Musulunci. Sa’annan duka ‘ya ‘yan zasu zama nasa shi kadai, matarsa zata iya samun daya bisa takwas na duk abinda suka mallaka.

A wani bangaren kuma, ‘yan mata sabobin tuba daga Musulunci sun fi so su auri Krista daga wadansu kasashe saboda su iya barin kasarsu. Saboda haka sukan bar Krista ‘yan kasa su kadai, babu aure. Don haka, samarin sukan koma su auri ‘yan mata Musulmai. Bangaskiyarsu takan zama cikin hatsari. Domin matarsa da Musulma ce zata iya nema a raba aure su duk lokacinda tag a dama tunda shi ya bar musulunci, akan wannan duka ‘ya ‘yansu da kuma duka mallakarsu nata ne.

Akwai bukatar hikima da jagora ta jinkai daga wurin Yesu Kristi in mai yiwuwa ‘yan ’uwa, miji da mace wadanda suna da tushe daga Islama su auri juna. Da haka za a tabbabtar da iyali mai albarka cikin Kristi. Wannan ma zai iya zama tushe na Ikklesiya a cikin gida.Wannan zai yiwu idan iyalin Krista sun yarda su shige hatsarin taruwa a asirce a cikin gidansu. In an gano irin wannan taron Ikklesiya, za a iya kulle iyalin a kurkuku kuma a kwace abinda suka mallaka. Aure cikin sunan Yesu Kristi na da sakamako mai girma kuma hanya ce ta kafa sabobin gidajen adu’a.

‘Yan’uwa maza da mata wadanda ke jagorantar Ikklesiyoyi su yi kokarin shirya yadda samarin da ‘yan matan da suka isa aure zasu rika haduwa su tattauna. Wannan zai iya zama da wahala a kauyukan da Musulmai suke, amma babu matsala a manyan birane. Yadda samari da ‘yanmata suke cudanya a jami’oi, dakunan karatu. Filin jirgin sama da wuraren shakatawa yana nuna inda aka dosa.

Wani misali wanda wata tsohuwar Mishanariya tayi da zai kalubalance mu.

A Moroko an yi wani mutum Krista mai kyaun gaske wanda shugaban makaranta ne. Bai iya samun mataimakiya mai dacewa ba. Saboda haka sai yace, “Nayi alkawarin zama Kaman Adamu da Allah”. Kamar yadda mahalicci ya sa wa Adamu barci mai nauyi, sa’annan ya dauki daya daga cikin hakarkarinsa ya halicci Hauwa’u da ita, macen da tafi kyau ni ma bazan sake neman mata ba, amma zan jira Allah ya bani wacanda ta fi ko wacce kyau.

Ubangiji kuwa ya aika da wata tsohuwar Mishanariya wacanda ta zo ta gaishe shi ta ce dashi “Emiya, lokaci yayi da zaka yi aure”! Ya amsa mata yace”, Na gode wa Ubangiji”! Ta cigaba da Magana”, Ina da jerin sunayen ‘yan mata Krista guda 80 wadanda zasu so su auri wanda yake bin Kristi”. “Da kyau” inji Emiya. Matan ta cigaba da cewa, “yanzu ka zabi daya daga cikinsu” Emiya yace, “Amma ban san ko daya daga cikinsu ba”. Mishanariyar tace, “wannan bashi da Muhimmanci. Ka dauki fensirinka, ka rufe idanunka, ka yi adu’a hannunka ya taba takardar. Duk wacanda fensirinka ya taba, ita ce matar da Ubangiji ya shirye maka. “Emiya ya furta, “zan mutu”! tsohuwar matan tace”, kada ka damu. Yanzu shine lokacin yin aure”. Emiya yayi ajiyar zuci, ya dauki fensirin, da rawan jiki ya dora fensirin a bisa takardan, ya bude idanunsa kuma ya karanta sunan zababbiyar. “A ina take da zama”? Ya lumfasa “wajen kilomita 500 daga nan, kudu maso gabar da teku”, ne amsar da ta bashi. “Ka dauki motarka, ka je ka sameta ka gaya mata cewa, “Allah ya aiko ni zuwa gareki don muyi aure”.

A gigiye, Emiya ya dauki motarsa, ya tafi, ya kai inda take zaune, ya ga gidanta, ya buga kararrawa, abin mamaki tana gida. Ya bada sakonsa, bada dadewa ba suke yi aure.

Bayan ‘yan watanni, kuwa, Emiya ya rubuta wa abokansa: ku yi mini adu’a in koyi yadda zan kaunacci matata, domin tana da taurin kai, kuma bata son abinda ina so, in kuma ta so wani abu, ni bazan so shi ba. Zaman mu tare muna mutuwa ne kullum. Ni Krista ne, bana so in duki mata ta ko kuwa in sake ta. Ku yi mini adu’a don in koyi yadda zan kaunaci matannan tawa mai taurin kai. Yau suna da ‘ya ‘ya da yawa, kuma sun sami albarka don sun iya taimakon juna.

Ba kowa ba ne zai yi sha’awan hanyar da wacannan tsohuwar mishanare ta bi ba mu ma bamu yarda ko kuwa mu karfafa a bi ba! Amma ta hada Krista da yawa aure fiye da masana tauhidi da yawa. Samari da yawa sun lumfasa sun ce, “Ni ma da Allah zai aiko mini irin wannan Mala’ika”!

A kasashen Musulami kamar Maroko, ana aure ne a gaban malami (sheik). Amma a yawancin lokaci in an bashi kyauta ta musamman yakan cika takardar auren ko bai kasance a bikin ba, saboda kada mutum ya dora hanunsa bisa Kur’ani. Amma ‘ya ‘ya na irin wannan aure musulmai ne. A Moroko, babu wata hanya ta Shari’a da za a bi don mutum ya canza addininsa daban da wanda yake a Fasfo na shi.

Yayin da sabon tuba da mace mai bi sun yi aure, a yawancin kasashen musulmai wannan na nufi an hada dangogi biyu kenan. Tattaunawa, bincike da yin shawara na da muhimmanci har sai an biya sadakin aure. Bayan bikin da kan hada dangogin biyu, ma’aurata Krista sukan sake daura auren a cikin Ikklesiyarsu ta boye, wanda shine ainihin masomin rayuwarsu ya aure.

Banda matsalar samun macen da ta dace don yin aure, akan sami wadansu matsaloli a kasashen musulmai:

Sabobin tuban da ke da aure sukan sami matsalar samun karba a Ikklesiya domin suna da mata hudu da ‘ya ‘ya masu yawa. A Sudan wata Ikklesiya da ta yanke shawarar yi wa irin wannan iyali baftisma in mai gidan ya shaida a gaban mutane cewa yayi zunubi a cikin jahilci ya bi dokar da bata dace ba. Ba zai saki matayen sa da ‘ya ‘yan ba nawayansu na kansa. Dole ne ya furta a fili cewa, a matsayinsa na mai mata da yawa, ba za a bashi shugaban cikin Ikklesiya ba.

A Indiya, wani Likita mai mata hudu da ‘ya ‘ya 20 ya zama Krista. Yayi wa matsayensa wa’azi saboda ya saki wadanda basu karbi bishara ba. Amma ya rike duka ‘ya ‘yan. Ramakon da wani babban dansa na wajen daya daga ciki wadanda ya saka yayi shine bayan mutuwar uban, sai ya bizne shi a hanyar musulunci.

Hada hannu da Ikklesiya, neman aiki da hada auren Krista ne muhimman matakai guda uku na kawo sabon tuba cikin Ikklesiya. Matsalolin da ke addabe da wadannan matakai wani lokaci sune bukatar adu’a, bangaskiya, lokaci da kuma karfi fiye da yi wa Musulmi bishara da rabuwarsa da danginsa. Wadansu sabobin tuba sukan boye bangaskiyarsu cikin Yesu daga ‘yan ‘uwansu har sai in sun iya tallafa wa kansu kuma sun iya auren mace Krista.

Abubuwa Masu Hatsari Da Kan Auku

Bayan da sabon tuba ya karbi Krista, shi jariri ne yana bukantan lokaci don yayi girma cikin bangaskiya, kauna da bege. Dole ne kamar yadda muke shi ma ya karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma ya yi adu’a kafin ya yanke kowace shawara ta sa. Zai koyi yadda zai rika gafarta wa wadanda suka yi masa laifi, kamar yadda Yesu ya gafarta mana (Matiyu 6:14 – 15). Umurnin Yesu na kada mu Shar’anta laifofin wadansu ma na ciki (Matiyu 7:1 – 5).

Nan da nan sabon tuba yakan gane kasawan wadansu Krista. Yakan ga yadda Fasto kan hau bagade a tsaye yayi wa’azi da muryar daya sha bambam da yadda ya saba Magana. Ya ga cewa akwai Krista attajirai da matalauta a Ikklesiya kuma ana daukaka masu arziki, sa’annan matalauta ba a kula da su. Irin adon da ake yi don a nuna a lokacin sujada ranar lahadi a bayyane yake kamar tsegumin da ake yi in wani dan’uwa baya wurin. Amma idan mutumin da ake yin zancensa ya bayyana, sai su yi kaman su abokansa ne. Nan da nan sabon tuban sai yace “Munafukai ne su”. Wadansu Fastoci sukan yi kaman dawisu wanda yana nuna gashinsa, zaka ga kauna kadan, fahariya dayawa da halin ko inkula. Bada dadewa ba zai ce, “Krista da Musulmai babu bambanci! Akwai rarrabuwa, buri da rashin hankali a nan”.

Abinda sabon tuba zai koya shine asirin gafarta wa juna, yi wa wadansu adu’a kin kai, ganin kansa mai laifi a gaban Allah, tawali’u na ruhaniya. Asiri na duka Krista shine gafartawa ba zama cikakke ba! Dole ne mu gafartwa wa dan’uwa ko ‘yar’uwa sau 490 kullum.

A wani bangaren kuwa, Krista da suka riga sun girma kada su yi saurin kushe sabobin tuba. Kalmomi na musulunci zasu iya fita daga lebunan su wadanda bai kamata su fada ba. Irin halayyan zaman aure a musulunci ga maigidanta dole a daina su sa’annan rayuwar ta yi wa wadansu hidima tayi girma a cikin su. Suna bukatar lokaci su koyi yin aiki na sa’oi takwas a rana guda saboda su iya ciyar da iyalensu, cikin harkar siyasa, kada su rika sukan bokan hamayyarsu, amma su kaunace su su kuma yi musu adu’a. Kiyayya wanda suke da shi don kasashe na kusa da su na bukatar fansa. Farfaganda na ban kyama a talabijin, mujallu da manyan takardu na sanarwa babu kyau. Akwai bukata Ruhu Mai Tsarki ya kawo nasara bisa irin kazantattun abubuwa dole a ci nasara basa halin zaman ban za don ana dogara akan kaddara tawurin daukan nawaya cikin Kristi. In babu tsarki sabon tuba ma ba zai ga Ubangiji ba.

Ta yaya za a warware wadannan matsaloli? Mu Krista muna da bukata mu zama da idanu irin na uwa ba irin na hafsan ‘yan sanda ba. Hafsan ‘yan sanda yakan ga laifi ya rubuta rahoton abinda aka yi. Uwa takan ga kuskuren danta, amma takan hore shi cikin kauna don kawo canji!

Uwa takan canza tsummokin jaririnta sau da yawa a rana guda. Wannan ba aiki mai dadi ba ne. Amma uwar, wani lokaci har Uban sukan yi wannan aiki don kauna. Har yaushe? Mako guda? Wata daya? Watanni uku? Sukan gaji da yin wannan aiki har su yar da jaririn tare da tsummokin? Ba zai taba yiwuwa ba! Me yasa? Uwa-uwace kuma Uba-Uba ne. Sukan wanwanke dansu sau da dama a Shekara daya, biyu har fiye da haka wani lokaci zuzzurfan kauna ce takan sa su yin wannan.

Za mu wa sabon tuba daga Musulunci hidima a cikin ruhu na Shekaru da dama har ya kahu ya zama tsarkakakke, shiryayye don yin hidima cikin sunan Yesu. Iko na Dan Allah ya fi duk abin da muke tsammani karfi: “Domin duk wanda ke haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuma it ace ta sa muka yi nasara da duniya.Wane ne ke nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ba ne”? (I Yahaya 5:4 – 5).

Kamar Yesu Kristi ne ya tilasta mu yi wa wadanda suka bar ruhun Islama sa’annan suka karbi Kristi da koyaswarsa hidima. Misalai da amincin Krista da yawa na da tasiri a jawo Musulmai ga Kristi da renon su, kamar yadda Fasto Iskanda Jadeed, wanda akan shi musulmi ya rubuta.

Idan da duka Krista na kwarai ne babu musulmin da zai cigaba da musulunci”.

8.05 -- Tambayoyi

In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan

Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.

Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.

  1. Wadanne bangaye guda uku masu yi wa Ubangiji hidima zasu yi nasara a kansu saboda su jagoranci musulmi zuwa ga Kristi?
  2. Menene babbar matsalar daya raba Islama da addinin Krista?
  3. Wanene Allah a Islama?
  4. Menene Uban Yesu Kristi ya yiwa ‘ya ‘yansa wanda Musulmai basu san komai akai ba?
  5. Me yasa Allahn. Islama ba zai taba zama Ubanmu na sama ba?
  6. Menene ake nufi da alheri a Islama kuma menene ma’anar alheri a addinin Krista?
  7. Me yasa musulmi zai iya rokon Allah ya gafarta masa kuskurorinsa amma kuma bai dauki kansa a mai zunubi ba?
  8. Menene bambanci tsakanin kaddara a Islama da zama wanda aka zaba a addinin Krista? Me yasa musulmai sukan fashe da haushi ko da shike sun yarda da kaddara bayan Krista Larabawa suna aiki, tsabta da kuma hakuri?
  9. Me yasa babu Ruhun Gaskiya cikin Islama? A cikin wane irin yanayi ne shariar musulunci ta yarda wa musulmi yayi karya ko saba alkawali?
  10. Wadanne bambance-bambance ne za a samu tsakanin auren musulmai da mata da yawa da auren mace daya na Krista?
  11. Yaya darussan da ake koyarwa a makarantun allo a karkashin allarammomi suke? Me yasa almajiran na samun sani fiye da hazaka wajen tunani da warware matsaloli?
  12. Me yasa Kur’ani da Shari’a basu kauda bauta ba, saboda musulmai a Yammacin Sudan a yau suna iya mallakan bayi? Ta yaya wadannan ka’idodi suke da tasiri bisa dangankata tsakanin masu kamfanoni ko gonaki da masu yi musu aiki?
  13. Me yasa a ko yaushe demokuradiya na gaba da Islama? Me yasa Jihadi a Islama kokari ne na kafa gwamnatin Musulunci?
  14. Fadi tsawon lokacin da yakan dauki Musulmi ya canza tunaninsa, ya rabu da al’adunsa na musulunci ya zama Krista na kwarai. Me yasa bishara ta zagon kasa bata kawo cigaba cikin kai bishara ga musulmai?
  15. Me ake nufi da cewa Musulmai da yawa har yanzu suna karkashin kangin danginsu, basu da ‘yancin yanke shawara su kadai. Tayaya wannan zahirin zai taimake mu cikin shirya dabarun yi wa musulmai bishara?
  16. A ina ne aka rubuta a Kur’ani cewa kada Musulmai su dauki Yahudawa da Krista a matsayin abokan tarayya?
  17. Me yasa iyalen Musulmai zasu yarda ‘ya ‘yansu su karanta Litattafan Krista amma su hana su zama Krista? Wanene a cikin dangi akan zabe shi don ya gargadi mai neman bin Kristi tawurin bangaskiya?
  18. Ina jerin irin azaban da Iyaye ‘yan halin rikau sukan gana wa ‘ya ‘yan su in sun bar Islama?
  19. Me yasa sabon tuba ba zai yi hanzarin barin iyayensa Musulmai ba? Wadanne halaye zai nuna in ba zai iya furta sabon bangaskiyar sa a fili ba?
  20. Ina yawan Musulmai wadanda suna da budaddiyar zuciya? Ina kuma yawan masu ra’ayin mazan jiya da suke biyayya da Kur’ani da kuma Shari’a?
  21. Tayaya Musulmi zai iya gano ko wadanne Litattafai ne da aka ce an saukar da sune ainihin wahayi daga Allah? Kur’ani daga wurin Allah yake?
  22. Wadanne zunubai uku ne daba a gafartawa a cikin Islama? Menene wannan ke nufi ga sabon tuba in ya zama Krista?
  23. Me yasa kowane sabon tuba daga Islama zuwa addinin Krista na da hukuncin kisa a kansa ko dashi ke Kur’ani bai bukaci kisa ba?
  24. Ko duka Krista “Musulmai” ne a bisa fadin Kur’ani? Menene manufar wannan tarko na musulmai kuma menene hatsarinsa?
  25. Ta yaya za a bambanta bishara ta amfani da al’adun mutane da ta zagon kasa irin wanda bashi da tushe a Littafi Mai Tsarki? (Karanta Matiyu 16:21 – 23).
  26. Me yasa kaunar da babu gaskiya karya ce kuma gaskiyar da babu kauna kisa ne.
  27. A ina ne mutum zai iya samun Ikklesiyu wadanda basu da shirin karban sabobin tuba daga Islama su zama membobinsu?
  28. Wadanne kwararun dalilai ne suka sa shugabannin Ikklesiya da dattawa kan zama da shakkar karban sabobin tuba daga Islama a tsakaninsu? Ta yaya zamu yi nasara da wannan mummunan hali?
  29. Ta yaya zamu karbi amintattun sabobin tuba cikin zumuncin mu saboda su ji kamar suna gida su kuma sami sabon gida da dangi a tsakanin mu?
  30. Me yasa yafi amfani a kasashen musulmai a fara tara masu neman gaskiya a dakunan adu’a kafin a fara kawo su cikin Ikklesiya?
  31. Me yasa dattawan Ikklesiya zasu nema wa sabobin tuba aikin yi kuma yaya za a koya ma wadanda basu da sana’a aiki? Don menene zasu koyi yin aiki sosai kaman mu?
  32. Me yasa da farko bazamu fara ba manema gaskiya ko sabobin tuba kudi ko sadaka ba kuma a maimakon haka a taimake su da kananan rance?
  33. Ta yaya zamu taimaki sabobin tuba daga musulunci su sami matayen aure Krista. Me yasa Iyalen musulmai sukan dauki auren dansu da ‘yar Krista da tsanani fiye da baftisma?
  34. Me yasa auren Krista a wadansu kasashen musulmai bashi yiwuwa babu goyon bayan Shari’a saboda ‘ya ‘yan Krista a wadannan kasashe su cigaba da zama musulmai a Fasfo nasu?
  35. Wane irin shawara kwamiti na Ikklesiya zasu yanke idan musulmi wanda yake da mata biyu, uku ko hudu ya nema a yi masa baftisma? Ya kori sauran mata ne ya rike ta farin? Menene zai faru da ‘ya ‘yan da suke da su tare da matan daya saka?
  36. Me yasa sabon tuba daga Islama zai auri mace Krista ba musulma ba? Me zai iya zama sakamakon auren Krista ko musulma?
  37. Me yasa sabobin tuba sukan gigice bisa halayyar wadansu shugabannin Ikklesiya da sauran membobin Ikklesiya? Menene asirin al’umman Krista na ruhaniya?
  38. Har yaushe za a gafarta wa sabon tuba manyan kuskurorinsa kuma har wayau ana daukan shi a matsayin Krista na kwarai?
  39. Menene babbar asirin samun nasara na kai bishara a tsakanin musulmai? Me yasa bin sawu yafi daukan lokaci fiye da kai bishara?

Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.

Naku cikin Hidimarsa

Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.

Ku aika da amsoshin ku zuwa:

The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.

Ko

GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY

Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on June 03, 2013, at 08:55 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)