Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":

Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 7 The Cross

This page in: -- Arabic? -- Cebuano -- Chinese -- English -- French -- Georgian -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Kirundi -- Russian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Uzbek -- Yoruba

Previous booklet -- Next booklet

01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI

7 - An Bayyana Giciye: Abinda Ke Kawo Tuntube Ga Musulumai



7.01 -- An Bayyana Giciye: Abinda Ke Kawo Tuntube Ga Musulumai

7.02 -- Muslumai sun ki Amincewa da Mutuwar Kristi don ́’Yan Adam

Duk wanda yayi magana da musulmai game da Yesu da kuma ceton da yayi, yakan kai inda musulmi baya iya magana kuma sai dai yayi murmurshi. In ka tambayae shi dalilin wannan zai iya kada baki ya amsa cewa: ku Krista kuna bin kawalwalniya! An riga an yaudare ku! ( Sura al- Fatiha 1:7). Ba a kashe dan mayama ba, bai kuwa mutu a kan giciye ba. (Sura al- Nisa 4:157),maimakon haka, Allah ya dauke shi zuwa wurinsa (Sura al- Imram 3:55, al-Nisa 4:158). Ba a taba giciye shi ba.

  • Wadansu musulmai sun ce Allah mai adalci ne. saboda haka ya ceci Kristi mara laifi daga azabar giciye. A maimakonsa ne ya sa aka giciye Yahuza Iskaryoti ma ci amana ( sura al- Nisa 4:157. har wa yau musulmai sun yarda da wannan zance.
  • Wanda ya zurfafa sani akan dalilan da suka sa musulmai suka ki amincewa da zancan mutuwar Kristi a giciye yadda aka bayana a Kur’ani, zai iya samun dalili na uku daga ciki jakar da ke tattare da karerayi wadanda uban makaryata ya tattara: babu mutum inji Kur’ani da ke da hakkin daukar zunuban wadansu a gaban shari’ar Allah ( Sura al-Aar’am 6:154, al-Isra 17:15, al-Fatir 35:18, al-Zumar 39:3, al-Najim 53:38), kowa zai roki gafarar zunubansa daga wurin mai tsarki. A musulunce, bashi yiwuwa wani ya dauki zunubin wani.
  • Hujja ta hudu akan rashin yiwuwar mutuwar Yesu akan giciye a cewar Kur’ani shine Allah baya bidar matsakanci, hadaya ta jini, raguna ko wani ya tsaya a madadin wani don ya gafarta zunubai. Shi mai iya yin komai ne, yakan gafarta wa wanda ya ga dama kuma ya battad da wanda ya ga dama (Surorin al-An’am 6:39, al- Ra’d 13:27, Ibrahim 14:4, al- Nahl 16:93, al-Fatir 35:8, al- Muddathir 74:31). In Allah ya yaudari mutum, babu wanda zai iya taimakonsa kuma (Surorin al-Nisa 4: 88, 143, al-Ar’raf 7:7:178,186, al-Ra’d 13:33, al-Isra’ 17:97, al-Kalf 18:7, al- Zumar 39:23, 36, Ghafir 40:33, al-Shura 42:44,46)
  • Hujja ta biyar, daga kirkire–kirkiren shaidan gaba da muhimmancin mutuwar Yesu saboda yan Adam. Musulmai na gani zasu iya samun barata tawurin kokarisu. Sun yi imani cewa nagagarun ayukansu zasu kori munanan.( Sura Hud 11:114). Suna da begen samun ceto in sun aikata dokokin Allah( Shari’a). Saboda haka, suna tunanin ba sa bukatar mai fansa ko kuwa giciye. Wannan gado ne daga adinin Farisawan Yahudawa.
  • Masana shari’ar musulunci sun ce Allah ya riga ya kaddara rayuwar kowane mutum tun yana cikin uwansa, kuma babu wanda ya isa ya canza abinda Allah ya rubuta. Sun yi imani da cewa babu abinda zai iya faruwa a rayuwar mutun sai abinda an riga an rubuta a littafin aljanna. Basu ga baicin a giciye wani har ya mutu don wadansu ba.
  • Yawacin musulmai basu da masaniya akan wannan muhawara ba. A takaice, akwai yarda a cikin al’umman musulmi cewa, giciyen Yesu haram ne ga musulumai. Suna tsammani ana amfani da giciye don siyasa ko jihadi ne na neman rushe karfi da al’adun kasashen musulmai.
  • Gaba da musulmai ke da shi a kan giciyen mai fansarmu na da tushe ne daga dauri wanda ba za a iya cin nasara da shi ba ta wurin iya muhawara ba kadai. Yin amfani da ilimi don bayyana ma’anar giciyen Kristi yakan dan taimaka kadan ne. Mu yi musu adu’a saboda su gane gaskiyar su kuma bada gaskiya. Wannan ruhun da ke gaba da Kristi dole ne a tumbuke shi a yar cikin sunan Yesu da kuma kaunar Allah.
  • Idan mun dubi kiyayya da ake yiwa Yesu da giciyen sa da karya, mutun zai iya cire zuciya ga kai wa musulmai bisharar ceto. Ko da haka, duk wanda ya yarda da cewa alkawuran da suke a Tsohon Alkawali, shirin Allah ne don kawo ceto, bai kauce daga gaskiyar Sabon Alkawali ba, kuma idan ya dauke rubuce-rubuce na duniya ko Karkattatun ayoyin Kur’ani wadanda ke nuna giciyen Kristi, wannan mutumin zai iya shaida tare da manzo Bulus da gabagadi da kuma tabbaci cewa:

To, da ya ke mu kubutattu ne tawurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu” (Romanwa 5:1.)

Asalin gaskiyan nan guda biyar sun fi hujjoji bakwai na musulmai karfi. Bari cikin adu’a mu yi shelar nasarar giciyen Kristi bisa musulunci a duniya duka.

7.03 -- Alkawura Game da Mutuwar Almasihu a Tshohuwar Alkawali

Musulmai da yawa sun gaskata kadarar kome. Duk wanda zai nuna musu zahiri cewa a cikin Ataura, Zabura, da Annabawa, mai fansa da an alkawarta dole ne ya mutu a giciye a maimakonmu, ana nuna musu cikar wadannan anabce-anabce a rayuwar Kristi, zai iya taimakon musulmai su bada gskiya da mutuwar Yesu a kan giciye. Mu bincike alkawura 333 a Tsohon Alkawali da cikansu a Sabon Alkwali don daidaita tunanin mu akan bangaskiyar musulmai game da kaddara. Yesu da kansa ya yi nasara da shaidan da kuma shakkar almajiransa sau da yawa da kalmomin nan “An rubuta” (Matiyu 4:4; 6-7; Luka 18:31; 21:22; 24-:46; Yahaya 5:46 da sauransu)

Musa ya Daga Macijin Jankarfe

Yesu ya bayyana wa Nikodimu, mutum mai tsoron Allah wanda yana cikin majalisar Yahudawa (Sanhedrin) manufa da abinda yasa ya zama tilas Yesu ya mutu kan giciye. Ya yi wannan ta wurin nuna masa abinda aka rubuta a Attaura; kamar yadda Musa ya daga macijin nan a jeji, haka kuma dole a daga dan mutum domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami. (Yahaya 3:15).

Da wannan misali Yesu yana Magana ne akan macijin karfen da Musa ya kafa ta wurin umarnin Allah duk wanda maciji ya sare shi in ya dubi wannan” alamar muguntar” yakan warke nan da nan.

Me ya sa Yesu ya kwatanta kansa da maciji, wanda kowane lokaci ana misalta shi da mugunta (Farawa 3:1-5)? Cikin kaunarsa ya shanye zunuban dukan masu zunubi, har ya zama kamar mugun har da haka yana da tsarki, kamar yadda Bulus ya rubuta a wasikarsa zuwa ga Korintiyawa; shida bai san zunubi ba, Allah ya maida shi zunubi saboda mu domin mu mu sami adalcin Allah to wurinsa. (II Korintiyawa 5:21).

Yesu ya nanata cewa babu wata hanyar samun ceto ga wadanda mugun ya yaudare su, sai mutuwarsa da yayi dominsu. Ya zo ne kuma ya sha wahala domin zunuban bil adama.

Yesu – Dan Rago na Idin –Ketarewa

Ubangijinmu Yesu ya je bikin idin-ketarewa tare da almajiransa don ya bayyana mana shine dan rago na idin-ketarewa da Allah ya bayar. Ya bada umarnin a cigaba da cin jibin Ubangiji sa’annan ya bayyana ma Mabiyansa cewa alkawura na idin ketarewa zasu cika a lokacin Mutuwarsa (Matiyu 26:26).

  • Kamar yadda bayan yankan dan rago na idin ketarewa ta farko, ‘ya’yan Isra’ila wadanda ke bauta a Masar suka yafa jinin a bisa dagarin kofa, saboda kada hukuncin Allah ya abko musu, haka ma kowane mutun wanda ya boye a kalkashin jinin Yesu zai sami ceto daga hukumcin Allah. Musulmai basu gane wannan ba, basu yarda cewa jinin dabba zai iya tsare su ba. (Fitowa 12:7, 13, 22-23; Ayukan Manzanni 16:31).
  • Kamar yadda ‘ya’ yan Yakubu suka ci gasashshen naman dan ragon idin ketarewa saboda su sami karfin fitowa daga bauta, haka Yesu, dan ragon idin ketarewa na gaskiya, yana so ya zauna a cikin wadanda suke binsa, yana basu karfi don su guji bauta ta zunubi ta shaidan (Fitowa 12;3-6, 8-11, 43 – 48; Matiyu 26:26; Yahaya 6:35-48-59).
  • Da shike babu gafarar zunubai sai da zubar da jini (Firistoci 17:11; Ibraniyawa 9:22) daya daga cikin manufofin dan rago na idin ketarewa dawwamamme ya kasance cikakken kafara don zunuban dukan wadanda suka bude kansu don tsarkakewa tawurin jinin, sun yi imani da hadaya kuma ka gode masa domin ikon jininsa (Ibraniyawa 19:14).
  • Yesu ya kira jinin da ya zubar jinin Alkawali (Farawa 24:4-8; Matiyu 26:27-28), wanda ya yi tsakanin shi da ikklesiya har abada. Duk wanda ya shiga cikin wannan alkawali da aka hatimce da jini cikin bangaskiya, ya zama da tsarki, kamar yadda Allah mai Tsarkine (Firistoci 11;44). Ya zama mai kauna kamar Yesu (Yahaya 13:34) ya kuma gafartawa kowa kamar yadda Allah ya gafarta masa (Matiyu 6:12, 14-15).
  • Mu taimaki musulmai su gane cewa Jibin Ubangiji cikan abincin idin ketarewa ne a Tsohon Alkawali. Duk wanda ya gaskata dan rago na Allah za’a tsarkakeshi da dukan zunubansa kuma Yesu zai zauna a cikin sa.

Zabura ta Shan Wahala

Zabura ta 22 annabci ne wanda ke bayyana shan wahalan Kristi a giciye. Allah ya saukar ma Dauda wadannan ayoyi wajen shekara ta 100 BC. Cikar wannan annabci daidai na nuna manufa da abinda ya sa giciyen Yesu ya zama tilas. Akwai annabci sama da goma akan shan wahalar Kristi akan giciye a zabura. Duk wanda yana so zai iya samun jagora da ganewa tawurin gwada wadannan ayoyi da kuma cikarsu a mutuwa da tashin Yesu daga matattu.

ZABURA 22 Mt. 27 Mk. 15 Lk. 23 Yah. 19
6. Mutane sun yasheni kuma suna Yi mini ba’a 33 29 36-37 -
7a. Duk wadanda sun ganni suna wulakantani 33, 41-44 29 36-37 -
7b. Suna zagi suna girgiza kawunan su. 39 29 - -
8. Ya dogara ga Ubangiji, bari ya kubutas da shi tunda yana jin dadinsa 43 - - -
11. Babu mai taimako 42 30-31 37 -
15: Harshe na ya manne da bakina - - - 28
16a. Taron mugaye ta kewaye ni 41-43 31-32 - -
16b. Sun soki hannaye da kafafuwa na. - 24 33 19:18, 20:20
17: Mutane na yi mini muguwar kallo - - 35 -
18a. Sun raba tufafina a tsakaninsu 35 24 34 23
18b. Sun yi caca da tufafina 35 24 - 24
1. Allahna Allahna, don me ka yasheni? 46 31 - -

Duk wanda ya duba, ya kuma yi tunani akan wadannan annabce – annabce a Tsohon Alkawali a kan mutuwar ubangiji Yesu akan giciye, zai gane:

  • Ta yaya Yesu zai sha wahala yayinda mutanen sa basu yarda da shi ba, amma sun raina shi kuma sun yi masa ba’a? A sashen gabas ta Tsakiya, in an raina mutum, wannan cin mutunci ya fi mutuwa zafi.
  • Ta yaya aka jajjaga jikinsa an yi masa raunuka amma bai yi kuka ba?
  • Yaya Ruhun Kristi ya sha wahala yayinda Allah Ubansa ya yashe shi saboda zunuban mu! Ba zamu iya gane zurfin wannan kuka da yayi. “Allahna Allahna, don me ka yashe ni?” (Zabura 22:2).

Wadansu masana suna da tunani cewa ba zai yiwu a ce Allah ya yashe kaunataccen dansa ba! Amma Yesu ba makaryaci bane. Ya ce: “Ka yasheni”.

Tunanin mutuntaka na cewa: in Allah ya yashe shi, wannan zai nuna cewa Yesu yayi zunubi kenan!

Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana a fili: shi wanda bashi da zunubi ya dauki zunuban mu. Nawayan zunuban dukan duniya na a kansa. Don zunuban mu ne Allah ya yashe shi.

Wadansu sukance, Uban ya boye fuskarsa daga wurin Dan, wato wai Uba ya shar’anta shi domin zunuban mu.

Ko ta yaya, Littafi Mai Tsarki yace: Lallai ne ya yashe shi! Dayantakan Triniti ya rabu wannan shine mafarin shiga karshe da muna shiga cikin duhu. Matiyu da markus ne suka gaya mana wannan daga cikin kalmomi bakwai wadanda Yesu ya fadi akan giciye. Wannan kuka har wa yau ya zama sanadin faduwa ga Iklesiya a yau. Ko ta yaya, wannan kalma fiye da kowane kalmar Yesu na bayyana cewa an kamala cetonmu.

Yesu ya shaida da farko: “Allahna! Allahna! Yakubu yayi kokawa da Ubangiji a kogin Urdun, Ubangiji ya so ya bar shi. Amma Yakubu bai bar Ubangiji ya tafi ba ko da shike shi mai laifi ne. Ya daga murya “Ba zan barka ka tafi ba sai ka albarkace ni”. Ta wurin bangaskiyar sa Yakubu ya ci nasara bisa Ubangiji mai sharia kuma ya sami albarkun sa (Farawa 32:23-32). Yesu bai bar Allah wanda yake shari’a ya tafi ba. Ya dage ma ubansa, ko da shike uban ya riga ya barshi. Amma tawurin bangaskiya bai bar Uban ya tafi ba. Ya tada murya yayi adua, “Allahna! Kaine Allahna ko da shike ba na ganinka kuma. Ba zan barka ka tafi ba, sai ka ceci mabiya na! Bangaskiyar Dan cikin kauna da Amincin Ubansa ta ci nasara akan Allah mai shari’a. bangaskiyarsa ita ce nasarar da ta rinjayi duniya (1 Yahaya 5:4). Tawurin banaskiyarsa an cece mu (Yahaya 16:33)

Bayan famansa da Ubangiji madaukaki, Yakubu ya karbi sabon suna: Isra’ila! ma’anan wannan suna shine; yayi kokawa da Allah kuma ya yi nasara. Yesu shine Israila na kwarai ! yayi kokuwa da Allah domin ceton bil’adama kuma yayi nasara tawurin bangaskiyarsa ! ya rike Ubansa kam, har ma a lokacin cire zuciya, lokacin da yake nesa da shi. Yayi adua a sa’ar mutuwansa “Uba, cikin hannunka na danka ruhuna” ( Luke 23:46), ko da shi bai iya ganin Uba kuma ba.

In kayi nazari akan wadannan alkawura a Tsohon Alkawali, ka kuma ga cikarsu a Sabon Alkawali, zaka ga cewa dama sabon Alkawali na cikin Tsohon Alkawali.

Bawan Allah Mai Shan Wahala.

Da alaman alkawalin mutuwan Yesu don bil adama mafi muhimmanci a Tsohon Alkawali an saukowa annabi Ishaya ne, annabin fansa. muna shawartar masu karanta wannan ‘yar takarda da su haddace wannan wuri da aka saukar da wannan wahayi daga cikinta zaka iya samun karfi a ruhunka, dawwamammen ta’aziya kuma ka sami cikaken amsa da zaka ba musulmai masu kin giciye.

Amma ya daure da wahala wadda Ainihi tamuce
Radadi da ya kamata mu ne zamu sha shi
Mu kuwa muna tsammani wahalarsa
Hukunci ne Allah yake yi masa.
Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu
Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata
Hukuncin da ya sha ya ‘yantar da mu
Dukan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke
Dukanmu muna kama da tumakin da suka bata,
Kowannenmu ya kama hanyarsa.
Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa,
Hukuncin da ya wajaba a kanmu.

(Ishaya 53:4-6).

Wadannan ayoyi uku sune cibiyar dukar wannan babi. An karfafa wani dalibi musulmi a Kasabalanka da ya karanta wannan wuri a gaban abokansa, sa’annan an tambaye shi abinda yake tunani game da wanda wadannan ayoyi ke magana akansa. Ya dan dakata kafin ya bada amsa, sai yace “In wannan labari gaskiya ne, lallai wannan mutum yana da matukar kauna!” Wannan matashi musulmi yagane asirin da ke cikin bishara!

Me yasa wannan musulmin bai ki wannan ainihin bayanin shan wahalan Yesu da mutuwarsa ba? Abinda ya sa shine bai yi karo da wadannan kalmomi “giciye” da “Dan Allah”! ba. Ba a rubuta su a wannan wuri ba shi ya sa ya iya gane ainihin abinda ya faru a kan giciye. Ishaya 53 na magana akan bawan Yahweh wanda Allah ya shar’anta, ya sha wahala, kuma ya mutu a maimakon mutane masu zunubi. Filibbiyawa 2:7 ya tabbatar da wannan shaida kuma ta yarda da furcin Yesu wanda ya kira kansa mai yi wa kowa hidima (Matiyu 20:28; II Korintiyawa 8:9; Ibraniyawa 2:14, 17).

Menene Ishaya 53 Zai Iya Gaya Mana da Kuma Musulmai Duka?

Yesu ya kaskantar da kansa kuma ya dauki cututtukanmu, kuskurorinmu, zunubai, laifuffuka, son kanmu, ya daure shan wahalar horon mu cikin shari’ar Allah. Ubangiji da kansa ya jibga zunubanmu a kansa. Domin zunuban mu ne aka yi masa duka, azaba, rauni daga bisani aka kashe shi.

A sakamakon haka ya sulhunta mu da Allah an kuma warkar da miyakun mu domin ya dauke dukansu a jikinsa. Wannan sadakarwa ta mutuwa da yayi domin mu, cikakke ne, lamuni ne, dawwamamme har abada.

Dan rago na Allah wanda aka gana wa azaba zai yi zuriya mai yawa da zasu kamala shirin Allah na ceto har ma a tsakanin musulmai da Yahudawa. Zai ceci yawancinsu daga zunubansu kuma a ribato har da masu karfi a cikin su.

In ka haddace Ishaya 53 duka, daga aya daya zuwa goma sha biyu, zaka sami makami mai karfi da zaka yi shelar nasaran Yesu a bisa musulunci! Yana da muhmmanci a rubuta wadannan ayoyi a kananan takardu (Kada a sa giciye ko” Yesu Dan Allah) a raraba. Ta haka za’a yi nasara da musu akan giciyen Yesu.

Wadansu Ayoyi Game da Giciyen Almasihu a Tsohon Alkawali

In kana neman wadansu alkawura da anabci akan mutuwar Yesu a Attaura, Zabura da litattafan annabawa, zaka iya samum ayoyi da yawa da kuma cikarsu a Sabon Akawali:

Allah ya kashe dabbobi kuma ya zubar da jininsu a gonar Adnin don ya rufe tsiraicin Adamu da Hawa’u (Farawa 3:21).

Da na Hawa’u zai kuje kan maciji, shi kuma zai kuje diddigensa (Farawa 3:15; Wahayin Yahaya 12:4,5 15-17).

Wanda aka rataya akan itace yana karkashin la’anar Allah (Maimaitawar sharia 21:22, 23; Ayukan manzanni 5:30).

Sun bashi ruwan tsami don ya sha (Zabura 69:21; Matiju 27:33; Yahaya 19:29).

A hannunka na bada Ruhuna (Zabura 31:6; Luka 23:46).

Labulen haikali ya tsage (Fitowa 26:31-33; Matiyu 27:51).

Ba’a karya kashinsa ko guda daya ba (Fitowa 12:46; Yahaya 19:33-34).

Suka dube ni, wanda suka soka (Zakariah 12:10; Yahaya 19:37; Wahayin Yahaya 1:7).

Azurfa Talatin a Tsohon Alkawali

A daya daga cikin litattafan annabci na karshe a Tsohon Alkawali, akwai bayani na musaman na azurfa talatin wanda Yahuza Iskaryoti ya karba don ya ci amanar ubangijinsa (Matiyu 26:14-16).

Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakina, idan kuwa ba haka bane to, ku rike abinku! Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana. Ubangiji kuma ya ce mini, ka zuba kudin a baitulmalin Haikali”. Sai na dauki kudin da suka kimanta shine tamani na, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji! (Zakariya 11:12-13).

A wannan wuri, Yahweh, Ubangijin alkawalin, ya ce, “Tsabar Azurfa talatin din nan da aka sayeni da su!” Yesu Yahweh ne? ko Allah na alkawalin ya zama mutum ne cikin Yesu Kristi? (Ishaya 40:3-5; 60:1-2; Luka 2:11 d/s). An bayyana wa Zakariya cin amanar Yahuza akan azurfa talatin tuntuni kafin abin ya faru!

Dawwamammen gaskiya na boye a ayoyin Tsohon Alkawali da kuma ayoyin da ke bayyana cikarsu a Sabon Alkawali, wadanda ke shaidar mutuwar Yesu akan giciye. Duk wanda ke da bukatar sani ya iya ganewa. Kira na musamman a littafi na karshe a Baibul an yi shi har ga Musulmai da Yahudawa: “Duk mai kunnen ji, ya ji abinda Ruhu ke fada wa Ikklisiyoyi”. (Wahayin Yahaya 2:7 d/s).

7.04 -- Giciyen Yesu Kristi A Sabon Alkawali

Musulmai da yawa sukan yi shakkar amincewa da abinda aka rubuta akan shan wahalar Kristi da mutuwarsa akan giciye akan tarihi ne na gaske. Sukan yi murmushi da tunani: Kristi! Da gaske suke yi, amma sun bata cikin tunanisu kuma sun yaudara. Suna tsammani Allah uku ne kuma suna tunanin an gaciye dayansu! musulmai da yawa basu yarda cewa an giciye Yesu ba.

Har da haka ba dukan musulamai ne ke da iri wannan tunani ba. Wadansu suna shirye don su saurari abinda aka rubuta akan giciyen Yesu ko kuwa su kalla a majigi. Musulmai biyu sun kalli fin akan rayuwar Yesu. Bayan kallon daya ya ce wa dan’ uwansa: “Me ya sa malaman mu sukan ce mana ba a giciye Yesu ba? na ganshi da ido na arataye akan gungume yana mutuwa”. duk lokacin da muka sami dama, mu ba musulmi daya daga cikin labarin giciyen Yesu in suna da marmarin karantawa saboda su iya haduwa da Yesu cikin wadannan kalmomin.

Yesu Na Gabatar Da Kansa

Dan mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bauta, ya kuma bada ransa fansa saboda mutane da yawa” (Matiyu 18:11; 20:28; 26:63-64). Kimanin sau 80 a bishara guda hudun nan Yesu ya kira kansa “Dan mutum” ko dashike shi, tawurin wannan furci, ya bayyana a Ubangiji da mai shariar duniya a cewar Daniel 7:13-14, Ya bayyana mutuntakansa da bayyanuwarsa cikin jiki a matsayin bawa mai kaskantarda kai. Yin haka ya canza magwajin kowace al’ada: na farko ya maida kansa karshe sa’annan an yi wa na karshe alkawalin zai zama na farko. Wadanda suke manya zasu kaskantar da kansu, wadanda suka kaskantar da kansu kuwa, Allah cikin kaunarsa zai fifita su (Matiyu 20:26-27; 23:11-12; Markus 9:35; 10:44; Luka 22:26-27).

Duk wanda ya bi Yesu zai zama bawa, ba mai gida ba! Wannan ya isa ayi tunani akai, wannan tunani, kishiyar tunanin musulumi ne.

Allahnmu mai tawali’u ne, amma Allahn musulmai mai girman kai ne (Sura al-Hashr 59:23). Musulunci na girmama kanta kullayaumin amma Kristi da mabiyansa suna kaskantarda kansu ko wane lokaci. Giciyen Yesu na bukartar mu canza halayenmu, in ba haka ba, zai zama abin tuntube.

A addinin musulunci, dan ta’adda wanda yana shirye ya sadakar da ransa don ceton kasarsu kan kira kansa “maifansa” (fida’i). Kristi shine mai fansa na gaske (faadi) wanda ya sadakar da ransa don ceton dukan wadanda suka bishi daga shari’ar Allah, daga ikon zunubi, daga dabarun shaidan, daga mutuwa ta har abada. Yesu ya fanshemu daga duka ikokin iblis da suka daure mu. Shine bawan wanda aka yashe shi da kuma mai fansar bayin shaidan. Kaunar Yesu da tawali’unsa sune mabudan gane mutuwarsa a kan giciye.

Muhimmancin Shan Wahalan Kristi

Wadansu ayoyi a bishara wadanda ake gani suna kawo suka akan giciye zasu iya taimako ga musulmai masu tsatstsauran ra’ayi!

Bayan shaidar Bitrus (Matiyu 16:16) Yesu ya darajanta kakakin almajiransa, amma ya so ya zurfafa ganewarsa game da Almasihu mai mulki zuwa ga gaskiyar bawan Allah mai shan wahala. Ya bayyana masa cewa dole ne yaje Urushalima ya sha wahala, kuma ya mutu a can kuma ya tashi daga matattu a rana ta uku (Matiyu 16:21).

Bitrus kuwa, ya razana. Yana tsammani Yesu yana cikin bakin ciki, kuma ya karfafa shi: “Allah ya tsare ka daga irin wannan mugun abu! Wannan ba zai taba faruwa da kai! (Matiyu 16:22). Yesu ya kafa ma Bitrus ido ya kirashi shaidan, “Ka koma bayana shaidan …kai mai kawo tuntube ne gareni, ba ka tunanin abubuwa na Allah, sai na mutane (Matiyu 16:23).

Me ya kawo canji a tattaunawa tsakanin Yesu da kakakin almajiransa. Bitrus ya yi kokari ya hana giciye Yesu wanda shine manufar zuwansa ya zama mutum. Nan take, Yesu ya gane muryar shaidan a cikin kalmomin Bitrus, domin shaidan yana kiyayya da giciyen dan Allah, wurin da aka ci nasara da shi.

Irin wannan tsautawa za a iya yi wa Muhammadu wanda ya sa Allahn musulmai ya yi duk abinda zai yi don ya hana Dan Maryama mutuwa a giciye.

Yesu ya bayyana wa almajiransa sau uku cewa dalilin zuwansa a duniya shine don shan wahala da mutuwa. (Matiyu 16:21; 17 : 22-23; 20:17-18). “Muna tafiya Urushalima, kuma za a bada Dan mutum a hannun manyan Firistoci da malaman Attaura. Zasu kasheshi zuwa ga mutuwa kuma su mika shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su duke shi su kuma giciye shi. A rana ta uku zai tashi daga matattu, (Matiyu 20:18-19)!”

Yayin da Yesu ke fuskantar Urushalima yana kara gane gaskiyar shan wahalarsa da mutuwa har ma da tashinsa daga matattu. Yesu yafi gaban annabi shi kalmar Allah ne a cikin jiki. Kowane lokaci yakan yi magana da Ubansa cikin sama, wanda ke bayyana masa abubuwan da zasu faru nan gaba Babu kuskure.

Mutumin da tunaninsa ke daidai zai nuna rashin yarda. Zai ce,”

In Yesu ya san duk wadannan, me ya hana shi yin hijira kamar yadda Muhammadu yayi daga Makkah zuwa Madina? Me yasa Yesu bai boye ko ya bad da kammansa ba? Bukata ce daga Allah ta iza shi yin wannan. Ya sani cewa ‘yan adam ba za su sami ceto ba ba tare da ya mutu ba. Ya yi biyaya da nufin Ubansa a sama har ga mutuwa! Wannan bukata ya zama bako kuma abin kyama ga musulmai.

Yesu a Gatsemani

Yesu ya yi bakin ciki da kuka lokacin da ya fuskanci mutuwa, yayin da yayi adu’a a gonar zaitun a garun Urushalima. Almajiransa sun yi barci kuma basu iya taimakonsa da adu’oinsu ba. Harda haka, shi yayi adu’a, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka dauke mini kokon wahalan nan Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka” (Matiyu 26:39).

Yesu a mutum da ransa ya tauye daga shariar Allah wanda zai kai ga mutuwar sa. Amma a matsayinsa na Dan Allah ya ci nasara bisa nufin jiki, ya mika kansa ga nufin wanda ya kaunace shi. Giciyen Yesu ba yawon shan iska bane ko wasa, amma yaki ne tsakanin sammai da gidan wuta. Yesu ya yarda da nufin Ubansa ya maimaita adu’a na biyu da na uku: “Ya Ubana, in wannan bazai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufin ka” (Matiyu 26:42).

Da gaske “Musulunci” ko mika wuya ya zama a bayyane a wannan adu’a ta yaki wanda Yesu yayi. Babu wanda ya tilasta masa da mika wuya ga Ubansa, kaunar da yake da ita ta iza shi, shi kuma ya dogara ga cikakken jagorar Ubansa.

Kasawan Almajiran Yesu da Hakurinsa

Almajiran Yesu sun sami horaswa a makarantar Littafi Mai Tsarki wadda ba kamarta a duk duniya da koyon aiki a gaban malamin malamai. Da lokacin gwaji yazo, sa’anda aka kama Yesu, dukan su sun fadi jarrabawa. Sun gudu cikin duhu! Bitrus ya sare kunnin daya daga cikin sojojin da takobinsa, kuma ya yi musun sanin Yesu har da rantsuwa (Matiyu 26:56, 69 – 75).

Menene Yesu ya yi? Yaya ne ya magance kasawan kaunatattunsa? Yayi musu adu’a lokacinda yake rataye a giciye: “Ya Uba, kayi musu gafara, don basu san abinda suke yi ba” (Luka 23:34). Ya kamala aikin ceton duniya duka shi kadai a karshen shan wahalarsa yayi kuka. “an gama” (Yahaya 19:30).

A wannan lokaci kuma ya baratar da almajiransa kasassu ba da sanin su ba. Ya ceci dukan duniya har da Yahudawa da musulmai. Yesu ba zai sake mutuwa ba kuma don Musulmai da Yahudawa! Ya yi kauna kuma yana kaunar dukan mutane har ma da wadanda ke magabtaka dashi. Suma yana jiransu.

Wani hafsa a cikin sojan Roma ya tabbatar da cewa da gaske ne “Sarkin Yahudawa” ya mutu, ya soke shi da mashi a tsakanin hakarkarin sa. Wannan suka kawai ya isa da zai kashe Yesu. Har da haka, azaban da ya sha akan giciye ya riga ya kamala manufar ta. Suka da aka yi da mashi ya zama tabbaci na mutuwar Yesu. Yaya kuma Muhammadu zai ce, “Basu kashe shiba! Basu giciye shi ba! Ya batane garesu kamar haka” (Sura al-Nisa 4:157)?

Lokacin da Yesu ya tashi daga matattu, ya bayyana ga almajiransa da suka buya don tsoro, bai tsauta musu don gudun da suka yi ba, amma ya gaishe su “Assalamu Alaikum” (Yahaya 20:19). Lokacin da basu gama gane cewa shine ba, ya nuna musu raunukan da aka yi masa a hannaye da kafafunsa, da kuma raunin da aka yi masa a hakarkarin sa. (Yahaya 20:20). Daga nan suka yarda cewa Yesun da aka giciye kuma an bizne shine yake tsaye a tsakiyarsu rayayye!.

Bayan haka Ubangiji rayayye ya fara koya musu kuma shirin ceto a Tsohon Alkawali. A cikin wadannan kwana 40, Ya nuna musu cikin Attaura, Zabura, da Annabawa cewa dole ne Almasihu ya sha wahala kafin shiga cikin daukakarsa (Luka 24:26-27). Ya bude turnaninsu, saboda su gane rubutacciyar maganar Allah kuma ya tabbatar musu da cewa, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu” (Luka 24:46).

Yesu da kansa na nuna mana hanyar da ta dace ta yi masa hidima a tsakanin musulmai. Yayin da musulmai masu neman sani wadanda a wani lokaci sukan rasa marmarin jin maganar Allah su gudu kamar yadda almajiran Yesu suka yi: Nawayar ya ta rataya a wuyan mu shine na sake tattara su a sake daukan su a tushe a koyaswar Littafi Mai Tsarki kamar yadda Yesu ya yi da almajiransa.

Babbar Nasara

Bayan Yesu ya shirya manzaninsa don shafewan Ruhu Mai Tsarki a sakamakon mutuwar sa a giciye, almajiran suka tambayeshi, “Ubangiji, a kwanaki masu zuwa ne zaka kafa mulkin Allah a Israila a matsayin Almasihu?” Har wa yau suna nufin mulkin duniya ne! basu riga sun gane koyaswar Yesu akan mulki na duniya ba. Bayan kwana 40 na horaswa ta musamman daga hannun Ubangiji rayayye, sun sake fadi gwadawar! Har wa yau suna cikin tunani a duniyance, a siyasance kuma a cikin jiki. Har da haka, da suka karbi ikon Ruhu Mai Tsarki, sun sami sabon wahayi, kuma wa’azinsu ya canza. Sun sami gabagadi da suka yi shelar gaskiya cikin kauna. Sun bayyana wa taron jama’a masu sauraronsu cewa su masu kisa ne, cewa da taimakon sojojin Romawa ‘yan mulkin mallaka suka kafa wa Almasihu Yesu kusa a kan giciye (Ayukan Manzanni 2:23).

Menene amsar Yahudawa masu sauraro? Ba komai! Ko uffan! Ba wanda ya ce: “yi shiru! Bamu kashe shi ba, bamu giciye shiba!” a maimakon haka suka yi shiru. Wannan shiru na Yahudawa tabbaci ne cewa da gaske ne aka giciye Yesu. In da suna da hujjar karyata zancen giciyen Yesu, da sun nuna kan amincewa da abinda almajiran suka fada. Amma sun yi shiru. Ka tuna dama sun taba yin kuwwa

A giciye shi, a giciye shi” (Matiyu 27:22-26; Yahaya 19:15).

Bitrus da manzanni sun yi ta kiran mutane zuwa ga tuba a lokuta dabam-dabam kuma sun shaida gaskiya ta Almasilhu giciyayye a gaban taron mutane a haikali, bayan da aka warkar da gurgu, da kuma a gaban majalisar Yahudawa. Ba firist ko malaman attaura wadanda suka karyata, shaidarsu, domin da su aka giciye Yesu. Sun zama shaidu (Ayukan Manzanni 2:36; 3:13-15; 4:10; 5:30, 7:52 d/s).

Duk wanda ya gane abubuwanda shaidar manzanni a cikin ayoyin nan bakwai na Ayukan manzanni zai iya haddasawa, da shirun da Yahudawan nan suka yi zai iya samun kwakkwaran shaida na cewa giciyen Yesu gaskiyane. Musulmai suna da ganewar cewa babu mutumin da zai yarda a kira shi mai kisan kai ba sai in an tabbatar da wannan laifin! Wadannan ayoyi bakwai na shaida zahirin giciyen Kristi.

Zamu kuma iya gane cewa manzannin Yesu basu iya yin shaidar giciyen Yesu da tashinsa daga matattu a matsayin babbar nasara daga Allah ba sai da Ruhu Mai Tsarki ya shiga zukatansu. Da ba Ruhu Mai Tsarki ba, da basu iya yin kome ba.

Duk kokarin bayani da koyarwa a lokocin da muke yi wa musulmai bishara, amfaninsa kadanne sai in Ruhu Mai Tsarki ya ganar da su, kamar yadda Dokta Martin Luther ya rubuta, “Na sani bazan iya bada gaskiya ga Yesu Kristi Ubangijina, ko kuwa in zo wurinsa tawurin ilimi ko ikona ba, amma Ruhu Mai Tsarki ya kira ni tawurin bishara, ya bude mini sani tawurin baye bayensa, ya tsarkakeni, kuma ya ajiyeni cikin sahihiyar bangaskiya, kamar yadda yana kira kuma yana tara dukan Krista masu bada gaskiya a duniya ya kuma rike su a dayance cikin bangaskiya”.

Adu’a don shiryawa da budewa da kuma sake zukatan musulmai tawurin Ruhu Mai Tsarki na da muhimmanci kamar yin shaida cikin hikima game da tashi daga matattu na mai ceto.

7.05 -- Rubuce-Rubuce Akan Giciyen Wanda ba a Baibul Aka Samu Ba

Musulmai da yawa basa so su saurari shaidar Baibul domin an koya musu cewa an riga an gurbatadda Baibul. Domin irin abokai wadanda aka yaudaresu kamar haka, musamman in masu ilimi ne, sai mu nemi shaida na giciyen Yesu a rubuce- rubuce na zaman duniya wadanda basu da alaka da koyaswar Krista.

Sanannun masana tarihin nan biyu na zamanin da, sun yi rubutu akan Yesu dan Yusufu ba Nazare. Daya daga cikinsu shine Tasistus a cikin Littafinsa mai suna “Annals”, Na biyu wato Filabiyus Josefus a Littafinsa mai suna “Yakin Yahudawa “ (The Jewish War). Josefus yayi bayani sosai akan Yesu da kuma giciyensa a kalkashin Bilatus a Litafinsa ta uku, sura 3:3. An yarda da Litattafan tarihi, kuma zasu iya taimakon Musulmi ya sake tunani akan batun Mutuwar Yesu.

Haka ma Littafin Tarihi na Yahudawa (Talmud) da aka rubuta a Beljum (Belgium). Yahudawa sun dade a Beljum a tsakanin Krista wanda ya zama musu tilas su rika ba Krista amsa yayin da ake basu laifi a kan giciye Yesu. Sun rubuta cewa, dan Yusufu, ya mutu ne kawai. Wannan rubutu a cikin Talmud ya bambanta da kiyayya da Yahudawa masu tsatstsauran ra’ayi suka yi wa Yesu wadanda suka dauki shawara cewa “A shafe sunansa daga doron kasa,kada a sake jin sunansa a tsakanin mutanen mu!”.

An sami hoto na yin ba’a da aka zana a jikin bango a Roma. Ga yadda hoton yake. Mutun mai kan Jaki an rataye shi a kan babbar giciye. A kalkashin giciye, ga wani sojan Roma na tsugune yana yi wa giciyayyen sujada sa'annan sauran sojojin na yi masa ba’a. Wannan hoton Yesu na nuna a bayyane cewa masana Ilimin Zaman duniya na Roma sun riga sun san da labarin giciyen Yesu kuma suna tattaunawa afili akansa. Sojojin Romawa da yawa sun fara yin imani da Mai ceto wanda suka kashe.

Akwai wadansu alamu a tarihi na giciyen Yesu da zai sa kowane Musulmi cikin tunani. A zamanin mulkin sarki Jamal Abd al- Nasser na kasar Misrah, Fafa Roma John Paul na 23 ya so ya wanke hannun Yahudawan da suke a wannan Zamani daga laifin kisan Yesu. Shi shugaban kasar Misrah ya mayar wa Fafa Roma da martani cikin fushi a Talabijin da cewa, “mun gane markircin ka! Kana so ka baratadda duka Yahudawa da Isra’ila! Baza mu taba yarda da wannan ba! Mun san Wandanda suka kashe Kristi: Yahudawa suka giciyeshi ba wani ne ba”. Bishof bishof, limamai, fastoci, shugabannin addini musulunci da duk wani mai hankali suka yi murmushi. A bayyane yake, Jamal Abd al- Nasser yana shirye ya yarda cewa akwai kuskure acikin Kur’ani don ya tabbatar da laifin Israila!

A bisa ga shari’ar Musulunci, Alkalin shari’a na jami’ar al-Azhar a Alkahira ko wani cibiyar addinin Musulunci, ya kamata ya nuna kin amincewa kuma ya gyara kuskure da ke cikin furcin Nasser cikin wata daya, kokuwa wannan kuskure zai zama abin karba ga yawancin musulmai. Ko ta yaya, kila malaman suna tsoron shugaban kasan ne, mai mulkin kama karya ne ko kuwa sun rufe ido ne basa son su baratadda Israi’la. Muhimmiyar abu a nan shine, shiru ma magana ne. Shirun da malaman musulunci suka yi a bisa shari'ar musulunci ya nuna cewa sun sani cewa an giciye Yesu. Har da haka basu fita a fili sun nuna amincewarsu ba don sun san wannan zai saba wa sanannun ayoyin Alkur’ani. To don su ba israi’la laifi sun yarda su aikata mafi kankantar laifi.

A yau, Yahudawa masu sassaucin ra’ayi da wadanda suke dan dama-dama wadanda suka ware kansu daga wurin masu tsatstsauran ra’ayi, suna zama a kasar Isra’ila. Yawancin su suna amfani da ikon Allah wanda yafaru tawurin Yesu don su dawo da wannan babban dan’uwa batacce zuwa ga mutanensa, sun tabbatarda haihuwan Yesu a Nazarat amma suna tunanin ko haihuwarsa tawurin fyade ne daga wani sojan Romawa. Sukan tattauna akan mu’jjizansa da koyaswarsa. Amma me suka rubuta akan mutuwarsa? Sun musanci giciyensa kamar Muhammadu? Sun bayyana kisar Yesu a kuskure ne na shari’a! Basa musun giciyen Yesu. Duka Yahudawa da Murya daya zasu iya su musanci giciyen Yesu saboda su wanke kansu daga zargi na shekaru 2000 a kansu. Amma sun sani zahirin da ke cikin tarihi ba a canza wa. Kowane lokaci a bayyane suke.

7.06 -- Ayoyin Alkur’ani da Suke Kwatanta Mutuwar Yesu

In ka bincike bayanin Muhammadu game da mutuwar Isa a Kur’ani zaka sami rikice –rikice da cigaba da taurare zuciya akan zancen giciye. Da farko an yi kamar an dan yarda da mutuwar Yesu amma daga bisani aka musance shi. Har da haka akwai rauni a wadannan ayoyi, ba sai an fito a fili ba za a iya gane wani abu game da giciyen Yesu. Mun kawo wadannan ayoyi don yin amfani da su lokacin yi wa musulmai bishara.

An ba ́’ya’yan Israi’la laifi sau goma a Kur’ani don kisan annabawan da suka yi Sura al-Baqara 2:61, 87, 91; Al Imran 3:21, 112, 181, 183; al-Nisa 4:155, 157; al-Maida 5:70). ‘Daya daga cikin wadannan surori na cewa”…. Muka bai wa Isa dan Maryama hujjoji bayyanannu, kuma muka karfafa shida ruhi mai tsarki. Shinfa, koda yaushe wani manzo ya je muku tare da abinda rayukar ku ba su so, sai ku kangara,wani bangare, kun karyata, kuma wani baugare kuna kashewa (Sura al-Baqara 2:87).

An rubuta yawancin ayoyin Kur’ani lokacin da Muhammadu ke Madina. Bai musanci kisan annabawa ba a Tsohon Alkawali amma yayi amfani da kisan don zargin Yahudawa. Har wa yau bai taba tunanin za’a iya jifar Yesu dan Maryama da dutse ba ka da shike ya hada shi cikin annabawan da Yahudawa suka kashe. (Sura al-Baqara 2:87; al-Nisa’ 4:157). Bayanin Kur’ani na kokarin nuna mutuwan Yesu ma.

Mutuwar Yesu a Kur’ani

Akwai wata aya a suratul Maryam wanda in an gane shi sosai, ya kusa zama shaidar Krista ne a Kur’ani. A wannan aya, Isa ya gabatarda kansa, kuma ya bada labarin rayuwarsa a takaice a jumla daya: “kuma aminci ya tabbata a gareni a ranar da aka haifeni da ranar da nake mutuwa da ranar da ake tayar da ni ina mai rai” (Sura Maryam 19:33)

Muhammadu ya nuna wannan amincewa saboda ya baratadda uwarsa Maryama kuma ya nuna cewa danta ba shege bane. Haihuwarsa tagomashi ne da salama daga wurin Allah. Anan, Bayyanuwar Kalmar Allah da Ruhunsa cikin jiki ya haskaka a Kur’ani (Sura Al’mran 3:45; al-Nisa 4:171; Maryam 19:20; al-Anbiya 21:91; al-Tahrim 66:12 d/s). wannan kuma amsa kuwwa ne na wakar mala’iku a saurukan Baitalami (Luka 2:14).

Kristi ya bayyana a Kur’ani a matsayin mutum mai kawo salama. Bai yi zunubi ba (Sura Maryam 19:19), Bai yi mugunta ba (Sura Maryam 19:32) Bai yi yaki ba, kisa ko Maganar banza ba. Kristi mai kawo salama ne wanda shine ma’anar kalma “Musulunci” shine kadai musulmin kwarai, sarkin salama.

Wannan aya (Sura Maryam 19:33) ya bayyana zancen Mutuwar Yesu Kristi a fili. Wadannan kalmomi sukan zama da wuyar fasara ga malaman addinin musulunci. Sun karkace ma’anar ayar sun rubuta cewa, ba shakka dole ne Isa ya mutu, amma ba a rayuwarsa ta farko bane a duniya amma bayan sake dawowarsa. Zai dawo ya fara kashe Dujal sa’annan ya kashe duka aladu, ya tuttage duka alamar giciye. Bayan haka zai yi aure, ya haifi ‘ya’ya, ya musuluntar da duka mutane har ma da Krista. Bayan wannan ne zai mutu! Mutuwarsa zai zama “Sanin sa’a ta karshe” (Sura al-Hajurat 49:61). Bayan an bizne shi kusa da Muhammadu a Madina, Allah zai bayyana a ranar shari’a, ya tada Muhammadu da Almasihu daga matattu su zauna a gadon shari’a su shar’anta duniya.

Kyakkyawar sanin nahawu zai taimaki mutum ya yi nasara bisa wannan murda-murda. Aya ta 33 bata da kalmar “Saufa” wanda zai iya maida mutuwar Isa ya zama da nesa, amma a maimakon haka, tana maganar mutuwa ta kusa wato haihuwa, mutuwa, tashin sa. Duk sauran bayani, mafalkai ne ko karerayi don su rufe gaskiyar mutuwar Yesu.

Akwai aya makamancin wannan a sura Maryam akan Yahaya mai Baftisma, wanda zai rage wa Yesu girma zuwa matsayin Yahaya. A nan Jibra’ilu, dan sakon Allah ya ce “Kuma aminci ya tabbata a gareshi a ranar da aka haifeshi da ranar da yake mutuwa da ranar da da ake tayar da shi yana mai rai.

Sanannen abu ne cewa an yanke kan Yahaya mai bafitsma, ya mutu, aka kuma bizne shi.

An bayyana mana wannan tabbataccen abu a inda da farko aka bayyana mana haihuwa, mutuwa da tashin isa daga matattu. Koda shike, a bangaren Isa, malamai sun juya ma’ana saboda kada a yarda da batun mutuwar sa a kan giciye.

Wata kila Muhammadu ya gabatar da Isa tare da Yahaya saboda ya musanci Allahntakar Isa. Amma har da haka, ya bar Isa ya gabatar da kansa kamar wanda an bashi “wahayi” daga sama sa’annan Yahaya, Malaika Jibra’ilu ne ya gabatar da shi. A Kur’ani, Isa shine gaba da Yahaya. Dan Maryama ya bayyana a Ruhun Allah cikin jiki, a Kalmar Allah wanda ya zama mutum, amma Yahaya da ne wanda aka haifeshi kamar kowane yaro an kuma san Ubansa da uwarsa.

A cewar Kur’ani, Isa yayi rayuwarsa bai taba yin zunubi ba (Surorin al’Imrana 3:45; al-Nisa 4:171; Maryam 19:19 da sawransu). Saboda haka bai mutu don nasa laifi ba. Wannan ya yarda da fasarar da ta yarda dacewa ya dauke zunuban duk ‘yan adam, ya mutu a maimakonsu ya kuma sulhunta ‘yan adam da mahaliccin su tawurin mutuwarsa. A cikin Kur’ani, Isa ya tabbatar mana da cewa salamar Allah zata kasance a kansa har ran da zai mutu.

Mafi Yaudara

Wata aya a Kur’ani da ta nuna wannan ra’ayi na Muhammadu akan mutuwar Kristi, za’a iya samu a sura Al’Imran: “kuma (Kafirai) suka yi makirci, Allah kuma yayi musu (Sakamakon) makircin, kuma Allah ne mafi alherin masu saka wa makirci. A lokacin da Ubangiji yace: Ya Isa! Lalle ni mai karbar ranka ne, kuma mai dauke ka ne zuwa gareni (Sura Al’Imran 3:54-55).

A fadin Kur’ani, Yahudawa sune ma yaudara sun yi kokarin kashe Isa asirce, amma Allah ya ga makircinsu. Allah kuma ya fisu yaudara ya sa Isa ya kubuce musu cikin salama sa’annan ya daukeshi zuwa sama a wurinsa.

Menene wannan “babbar zamba” da aka ce Allah ne yayi a fadin Kur’ani? Ya ceci Kristi daga mutuwa ta kisa tawurin jifa da duwatsu ko ratayawa akan giciye! Ta haka Muhammadu yayi dabarar kau da zancen giciyen Kristi tawurin kin fadin wani abu akai, Kalmomi guda uku fitattu da ke nuna wannan babbar yaudara a wannan aya.

Don a kau da giciyen Kristi, Muhammadu ya kira Allah “Mafi makirci duka”. Baibul yayi amfani da wadannan Kalmomi akan” Maciji ne a aljanna (Farawa 3:1)! Yayin da ruhun musulunci ya fuskanci giciye, dole ne zai shaida ko wanene shi! Dole ne Allah na Kur’ani ya bayyana kansa a gaban giciye da cewa shine” uban ma yaudara” (Khair-ulmaakirin)! Mu yi kokarin gane illar wannan batu na Kurani da abin da zai iya jawo mana da abokanmu. A Afisawa 6:11-20, Bulus ya dokaci dukan mabiya Kristi kada su kakkarya ikokin iblis da hikima ko iko nasu ba, amma su yi adu’a da bangaskiya kuma suyi hidima cikin sunan Yesu Kristi da kuma cikin ikon Ruhunsa. In da aka yi dabarar musun giciyen Yesu, sai mu bar dabara da tunanin mutuntaka mu shiga cikin duniyar ruhohi. Jinin Kristi ne kadai zai iya bamu kariya (I Yahaya 1:5; 2:2), Ruhunsa kuma shine ke bamu iko (Ayukan Manzanni 1:8).

Daya kalmar a cikin wannan aya itace “Mutawaffika”. Allah ya ce, “zan bar ka ka wuce”. Wannan kalma na da ma’ana da yawa. Tana bada ma’anar “yin barci a hankali” kokuwa Mutum ya kai ga karshen rayuwarsa cikin nasara”, Muhammadu yayi amfani da wannan rikitacciyar kalma don dadada wa Krista da musulmai rai. Ga Krista, Yesu ya mutu, ga musulmai bai mutu ba. A tunaninsu, an dauke Isa zuwa sama bai kuwa sha wahala ba. Muhammadu na da wayo. Yakan yi magana da kalma daya wanda ke da ma’ana biyu ko uku.

Tarjamar Kur’ani na Indonesiya da Turkiyya a wannan kalma sun yi amfani da ma’anar” zan bari ka mutu cikin salama” domin wannan shine ya fi kusa da tushen kalmar. Wadansu masu juya Kur’ani sun yi fama da wannan kalma don su gamshi malaman addinin musulunci.

Muhammadu yakan ce, “Yaki yaudara ce! Wato jihadi, wanda ya hada da mukabala da Krista da Yahudawa yana cike da yaudara da zamba . sai mu zama da hikima mu canza dabarunmu. Ba ko menene aka fada a cikin musulunci gaskiya ne ba.

Bayan Muhammadu ya fada cewa Allah yayi dabaran hana giciye Yesu, ya lumfasa kuma ya yi kokarin gamsar wadanda aka aiko su daga kasar Yemen ta arewa, wadanda (a cewar Tarihin Muhammadu daga hannun Ibn Hidham) Suka zo don su tattauna batun addini da shi a Madina. Ya sa Allah ya dauke Isa zuwa gareshi wadannan kalmomi ne na ban mamaki a Kur’ani. Kristi yana da Rai! Muhammdau a mace yake! A cewar Kur’ani Isa yana raye a yau tare da Allah Kuma yana magana da shi (Surorin Al’Imran 3:55; al-Nisa’ 4:158; al-ma’ida 5:110-111, 116-118; al-anbiya; 21:28 da sauransu). Muhammadu kuwa yana jira a Barzahu (Barzakh) don tashin matattu da ranar shari’a shi ya sa duka musulmai tilas su rika yi masa adu’a ya sami salama duk lokacin da suka kira sunan Muhammadu (Sura al-Ahzab 33:56).

Ruhun da ke goyon bayan musulunci yakan yi hakuri da Kristi wanda yake da rai kuma zai dawo. A iya hada shi a bangaskiyar musulunci amma ba zai taba yarda da giciye da Allahntakansa ba! Don haka, kashedi na Bulus da Yahaya sun shafi addinin Musulunci (Galatiyawa 1:8-9; I Yahaya 2:21 – 27; 4:1-5). Kowane tadi ko zance ta bishara da musulmai, kada ya tsaya a yin abokantaka kawai ba, amma ya hada da adu’oi don ‘yantar da su daga kangin iblis. Muhammadu ya san abinda ya sa ya dokaci mabiyansa da kada su rika mu’amala da mutanen da suke bin wadansu addinai musamman krista (Surorin Al’Imran 3:28; al-Nisa’ 4:89; al-Anfal 8:73; al-mumtahana 60:1,9). Kada mu ji tsoron saduwa da musulmai domin albarkar da ke cikin Almasihu na da karfi fiye da la’anar Muhammadu (Matiyu 5:44-45, Surorin Al-lmran 3:61 al-Tawba 9:29 da Sauransu)!

Ainihin kalmar da ya hada da ma’anar “yin barci a hankali” an sake yin amfani da shi akan mutuwar Kristi a Kur’ani (Sura al-Ma’ida 5:117). A wannan aya, Dan Maryama na Magana da Allah kaitsaye, bayan tafiyansa sama ya tabbatar mana da cewa ya barshi ya wuce ya kuma dauki nawayar almjiransa a maimakonsa. Mutuwar Kristi an gabatar da shi a Kur’ani a hanyoyi biyu, daya kaman zai faru ne nan gaba, dayan kuma kaman ya riga ya mutu saboda makircin Kur’ani ya tabbatar da cewa ba a giciye Kristi ba, amma Allah ya dauke shi ne zuwa sama.

Musu na Karshe Akan Giciye Kristi

Aya guda daya tak da ta musanci giciyen Isa kai tsaye (Sura al-Nisa’ 4:157) na nuna yadda Muhammadu ya kai makura a kan ra’ayinsa na gaba da mutuwar Kristi. Wannan aya ta soke duk wahayin da ya karba a baya wadanda sun nuna yiwuwar giciyen Dan Maryama. Wannan kiyayya na kisan Kristi an nuna shi a magana mai ma’ana biyu saboda haka wannan ya bada fili don shakka ko tarjama da kan zama da sabani da wadansu. A sura al-Nisa’ mun karanta: “Da fadarsu: “Lalle ne mu, mun kashe masihu Isa dan Maryama manzon Allah; alhali kuwa basu kashe shi ba, kuma amma an kamanta shi ne a garesu. Lalle ne wadanda suka saba wa juna a cikin sha’aninsa, lalle ne, suna shakka daga gareshi, ba su da wani ilimi face bin zato, kuma basu kashe shi ba bisa ga yakini. A’a Allah ya dauke shi zuwa gareshi, kuma Allah ya dauke shi zuwa gareshi, kuma Allah ya kasance mabuwayi, mai hikima” (Sura Al-Nisa’ 4:157 – 158)

Akwai taraku da yawa a wadannan ayoyin.

  • Da walaki Yahudawan da suke a Madina sukan yi shaida a fili cewa Dan Maryama ne Masihu na gaskiya kuma manzon Allah! Basu taba gaskanta haihuwar Yesu daga budurwa ba, ko bayyanuwarsa cikin jiki. Yahudawa sun ki yarda cewa shine Masihu sun kirashi abokin Ba’alzabub, sarkin aljannu (Matiyu 12:24; Markus 3:22-27; Luka 11:14-23). Wadannan kalmomi a Kur’ani baza su taba samun tushe daga wajen Yahudawa ba, domin basu taba amincewa da Yesu Manzon Allah bane, amma sun share sunansa gaba daya.

    Mai yiwuwa ne za’a iya yin tunanin cewa Yahudawa sun gargadi Muhammadu da kada ya ci gaba da damunsu kuma sun yi masa burgar zasu kashe shi in bai daina ba kamar yadda suka kashe (a cewar kur’ani) Masihun sa Isa. Mai yiwuwa cikin gatse suka kira Isa da lakabin Masihu saboda suyi wa Muhammadu burga.
  • Yahudawa suna da yawa a Madina sun yi wa Muhammadu burga, haka ma attajiran Makkah. Amma ya huce da wadannan kalmonmi cewa “Allah mai aminci ne. Bashi yiwuwa Allah ya bada amintaccen sa Isa a hannun Yahudawa. In ba haka ba zai iya yin tunanin cewa ni ma zan iya fadawa a hannun su”. Saboda amincin Allah da nasa kariya, ya yi biris da burgarsu kume cikin fushi ya amsa musu “Basu kashe shi ba! Basu giciye shi ba!”
  • Babu inda Muhammadu ya ce ba’a kashe Yesu ko an giciye shi ba. Shi dai ya nanata cewa ba Yahudawa ne suka kashe Kristi ba! Wata kila ya ji cewa Yahudawa basa giciye abokan gaban su, amma sukan jejjefe su ne da duwatsu. A karkashin mulkin Romawa, Yahudawa basu da ikon kisa. Saboda haka Muhammadu a wani bangare yana da gaskiya! Yahudawa basu kashe ko sun giciye Yesu ba! Wannan magana a Kur’ani, a cikin wannan ganewa, gaskiya ne, wannan yarda zai rage matsala tsakanin Krista da Musulmai.

    A duka duniya sanannen abu ne cewa Romawa sun giciye dubban bayi yantawaye da masu laifi baki. A haka wannan aya a Kur’ani na nuna cewa mai yiwuwa Romawa ne suka kafe Yesu a giciye. Yau musulmai masu budaddun zuciya wadanda suke so su gina gada da Krista sukan shaida yiwuwan irin wannan gurabtacciyar tarjamar Kur’ani.
  • Muhammadu yayi amfani da wani salon magana ya bayyana cewa Allah ya sa Yahudawa sun ga kamar an giciye Kristi ne (Shubbiha Lahum). Ya musanci giciyen Kristi wanda zahiri ne cikin tarihi, amma yace an sa shi ya zama Kaman wanda aka giciye (fatalwa).

Watakila Muhammadu ya ji daga wata kungiya ta Krista da suke zaune a chikin kwarin Nilu wadanda suka ce ba zai taba yiwuwa Allah ya zama mutum kuma ya biya bukatar mutuntaka ba. Sun yarda cewa Allah ya bayana a kamannin mutum ne amma bai zama mutum ba. Sun kuma koyas cewa Kristi. Wanda Allah ne na gaskiya, bashi yiwuwa a ce ya mutu ko an giciyeshi ba, amma an nuna kamar haka ne kawai! Lokacin da Muhammadu ya ji wannan karkatacciyar koyarwa nan da nan ya ga dama ya ce,” Abin tausayi ga Krista! Sun yi tunani da imani cewa Kristi ya mutu dominsu a giciye, amma an nuna musu ne suka ga kaman haka ne, ba a giciye shi ba. Kungiyoyin addinin Krista da dama masu kartatacciyar koyaswa suka rudar da Muhammadu.

Malaman addinin musulunci sun yi ta Karin gishiri akan juya wannan magana an sa shi ya yayata labaru irin wadannan a kasashen musulmai da dama kamar haka:

- Wadansu sun ce: Saminu ba kurane wanda sojojin Romawa suka tilasta ya dauki giciyen Yesu. Lokacin da aka kai wurin da za’a giciye Yesu sai aka yi kuskure aka giciye Saminu a maimakon Kristi. Dan Maryama ya tafi abinsa ba abinda ya same shi

- Wadansu kuma sun ce: Allah mai adalci ne! Ya sa kamannin Yesu a fuskar Yahuza, da haka aka giciye Yahuza. Isa kuma aka sa ya yi kama da Yahuza ya tafi abinsa lafiya. Lokacin da Krista na ainihi ya ji irin wannan kage zai nuna kin amincewa ya ce: “Kana tsammani Maryama, uwar Yesu, wacanda tana tsaye a kusa da giciye, bata iya bambanta danta da Yahuza akan giciye ba? Ko kana tunani Allah zai yaudari macen da ta fi duka mata a duniya da lahira (Sura al’mron 3:42) ya sa ta ta yi ta kuka na sa’oi da dama don maci amana wanda ke kan giciye yayin da danta ya riga ya tsere? Wannan tatsuniya ce kawai.

- Har wa yau wadansu sun ce: Da gaske an giciye Yesu. Bayan an giciye shi sai aka ga duhu ya rufe kasar, sai mutane da yawa suka gudu suka biye don tsoron aljanu. Sa’annan aka yi girgizar kasa wanda ta sa har sojojin Romawa suka gudu suka buya. Lokacinda kowa ya tafi an bar Yesu shi kadai, sai ya sauko daga giciye – kamar yadda ‘yan darikar Ahmadiya suka ce – ya tafi zuwa Kashmir, a can ne ya mutu. Har da haka a kabarin Isa a Srinaga, mun gani da Idanun mu, ba Kristi dan Maryama bane aka bizne, amma kakan wani iyali mai martaba a Kashmir, wanda shehun musulunci ne mai suna Isa, ’yan Ahmadiyya suka yi kuskuren cewa kabarin Kristi ne.

7.07 -- Alheri na Musamman na Yarda da Cewa Mutum Mai Zunubi Ne

Kokari don ka jawo hankalin musulmai game da giciyen Yesu cewa zahiri ne na tarihi bashi da amfani sosai muddin ba su ne suka nemi bayani ba. Babban matsala a bishara ga musulmai shine yarda da suka yi akan cewa basa bukatar mai fansa, matsakanci ko hadaya don zunuban su. Basu san yadda zunubansu ke da zurfi ba. Suna tsammani zasu iya yin ayuka nagari fiye da munana (surori Hud 11:114;al – Ankabut 29:7; al- Fatir 35:29-30). Babu wani amfani a yi musu bayani a kan giciyen Kristi muddin suna da tunanin cewa basa bukartar mai ceto. Sun amince cewa suna da nagarta.

Ka taimakesu su gane yadda su batattu ne kuma suna karkashin hukumcin Allah Kaman dukan ‘yan adam, wani lokaci ya fi muhimmanci fiye da a sa su gane daman samun barata wanda an wadatar ta wuri mutuwar Kristi a giciye. Bari su fara gane cewa in ba don taimakon Allah ba zasu je wuta.

Ayoyin Zabura na nuna tuba zasu iya taimako don gane wannan gaskiyar. (Zabura 6:2-10, 32:1-11, 38:2-32, 51:3-19 da sauransu). Muna bada shawara a bar Musulmai su haddace Zabura 51, saboda tunaninsu da lamirinsu su cika da ruhun tuba. Bangaskiyar Musulmi ba yakan ratsa daga kwakwalwa ne zuwa zuciya ba amma daga zuciya zuwa kwakwalwa. Wannan gaskiya ne.

Lokacin da aka ba wani babban malami na Musulmai wanda ya tuba ya karanta Zabura 51 a shiri na rediyo kamar yadda yake karanta Kur’ani, sai ya fara hawaye. Ba ya karanta ayoyin ba ne kadai, amma yayi adu’a na cewa shi mai zunubi ne. Zabura ta 51 makaranta ce ta tuba garemu duka. Ta na nuna mana ko wanene mu. Wadannan ayoyi sun zama jagora ainun ga duk wadanda suke tsammanin basa bukatar wani taimako.

Zabura 51:1 Mai zunubi a Zabura 51 ya roki jinkai da alheri. Dauda ya gane cewa samun gafaran zunubi jinkai ne daga Allah. Ya roki Allah ya wanke zunubansa, ba kawai wadansu kurakurai ba.

Zabura 51:2. Yaji a jikin sa da kuma ruhunsa cewa yana da dauda, ya roka a wanke shi sarai

Zabura 51:3 Gane babbar zunubin da yayi ya yi masa ciwo a zuciya, ya husata.. Ruhu Mai Tsarki bai bashi kwanciyar rai ba, bai iya yin tunani ko barci mai kyau ba.

Zabura 51:4 ya gane cewa zunubi tawaye ne ga Allah mahalicci da alkali. Ya amince da zunubi ba kuskure ne kawai ba, amma laifi ne ga martaba da Tsarki na Allah. Ya shaida cewa ko ta yaya ka shar’anta ni, kana da gaskiya. Ni na tsargu kwarai na kuma rasa damata”.

Zabura 51:5 Na kazantu gaba daya. Tun sa’adda Uwata ta dauki ciki na, na gaji zunubi a jiki da kuma ruhu wurin kakannina. An lalatar da ni tun ina saurayi. Jiki na, ruhu na, zuciya ta, iyawa ta, kome da kome muguta ne

Zabura 51:6. Ubangiji, kana so kaji gaskiyar. Na furta dukan zunubai na na boye. Ka nuna mini a fili ko wanene ni.

Zabura 51:7 in zofa, wanda da ana amfani da shi don wanke miyaku zai taimaka, ka wanke ni ciki da waje. Ka wankeni sarai daga zunubi, sa'annan zan zama fari kamar auduga.

Zabura 51:8 Ka mayar mini da farinciki na, don fid da zuciya ba zai warware matsalata ba. Ka rushe fahariya ta, amma zaka iya kawo mini ta'aziya cikin rayuwa ta.

Zabura 51:9 Kada ka kore ni, ka furta kalma guda kacal zuwa gare ni, ka share dukan laifofina.

Zabura 51:10 Bani da bege! Sabon rayuwa ne zai iya cetona. Daga chikina ka halitta zuchiya mai-tsabta, ya Allah, ka sabonta daidaitachen ruhu daga cikina

Zabura 51:11 Kada ka yasheni daga gaban ka; kada kuma ka dauke ruhunka Mai-tsarki.

Zabura 51:12 Ka mayas mani da farinchiki na chetonka:

Ka tokare ni da ruhu na yardan rai. Ya kamata mu nemi alherin Allah da zai taimaki musulmai su gane zunubansu a ta kowace hanya. kamar yadda mu ma muna da bukata mu tuba tare da su. Wannan Zabura zai iya jagorantar kowane mai yin adu’a zuwa tuba har ya juya gane cewa zuciya mai tawali’u ne zai gamshi Allah.

Wadansu ma’ikatan Kristi sukan yi amfani da Dokoki goma, zunubin Adamu (Farawa 3:1-4, 16) da musamman wahayin Ishaya 6:18 don kakkarya fahariyar masulmai. Lokacin da Ishaya ya gane Tsarkin Allah, wannan firist da annabi mai martaba ya fada da karfi cikin tsoro” Kaito na! Gama na lalace; da shike ni mutum mai lebuna marasa tsarki ne, ina kwa zamne a tsakiyar mutane masu lebuna marasa-tsarki: gama idanuna sun ga sarki mai-runduna” (Ishaya 6:5).

Mu roki Yesu ya bayyana kansa ga musulmai masu son kansu, saboda su kaskantar da kansu su gane babbar kauna da tsarki na Ubangiij su roki jinkansa. In basu yarda da zunubansu ba, da wuya mutum ya tuba har ya sami gafarar zunubai. Shi ya sa ya kamata mu bayyana ma’anar zunubi ga musulmi, kafin muyi masa magana akan giciye. Ganewa da amincewa akan wannan baiwace ta alheri daga wurin mai ceton mu (Romawa 2:4). Mu yi adu’a domin wannan baiwar.

Dukan Musulmai Zasu Shiga Wuta?

Akwai muguwar aya a cikin Kur’ani wadda ta ce dukan musulmai zasu wuta! Wutar kaddarar su ce ta dole. A cikin sura Maryam Muhammadu ya razana duka musulmai: “Kuma babu kowa daga gareku sai mai tuzga mata. Ya kasance wajibi ga Ubangijinka, hukumtacce. Sa’annan kuma, mu tsar da wadanda sukayi aiki da takawa, kuma mu bar azzalumai a cikinta gurfane: (Sura Maryam 19:71-72).

Wadansu masu yi wa Allah hidima sun gane cewa wadannan ayoyi sun sa musulmai da yawa sun dawo cikin hankalinsu. Sa zuciya na ceto daga wuta ga musulmai na iya yiwu wa ne daga aikata abububuwan da shari’ar musulunci ta bukata. Yesu ne kadai ya sha wahala domin mu don kada a shar’anta mu ko a kashe mu (Yahaya 3:18-23; 5:24 da Sauransu). Kaunarsa na bayyana son kai, fahariya da zunubanmu, saboda mu karbi ceto da rai madawwani wanda ya bamu da godiya.

7.08 -- Dan Rago Na Allah

A lokacin da Yesu ya ba musulmi iko ya gane zunubansa, sai mu nuna masa Dan rago na Allah wanda shi kadai ne magani, domin ya dauki zunubin duniya, har da laifin duka musulmai (Yahaya 1: 29-34; I Yahaya 2:1-2 da sauransu).

Lokacin babbar sallah, a karshen aikin hajji a Makkah, musulmai a kasashe dabam-dabam sukan yanka raguna, tumaki, rakuma a kowane iyali don su tabbatar cewa albarkar Allah ya kasance a garesu, ko da haka basu san ma’anar jinin hadaya a Tsohon Alkawali ba, ko kuwa yiwuwan kafara domin zunubanmu, da sulhu a wurin zubar da jini, saboda haka zai iya zama taimako ga musulmai a koya musu dokokin zunubi da hadaya ta konawa a Tsohon Alkawali (Firistoci 4:4, 14, 24, 33 da Sauransu), ko game da bunsurun Azazel a babban rana ta sulhu (Firistoci 16:6-10). Ta haka zasu matso kusa da Allah na gaskiya mai tsarki, kuma su gane manufan hadaya da ake yi da dabbobi a da a cikin Tsohon Alkawali da kyau.

Tunani mai zurfi a kan dan rago na idin ketarewa kamar yadda Yesu ya kafawa almajiransa ta gabatar da cin jibin ubangiji zai iya kai mutum ga kyakkyawan ganewa a kan sulhu da Allah tawurin hadayar da Yesu Kristi yayi na kansa.

Nassi mafi muhimmaci a Tsohon Alkawali akan ganewa da imani cikin Dan Rago na Allah shine wahayi na “Bawan Ubangiji” a cikin Ishaya 53:4-12. wannan bishara a cikin Tsohon Alkawali ta zama madawwamiyar ta’aziya da taimako ga wadanda suke nema su karbi barata ta wuri alheri, lokacin da lamirinsu ya dame su. Bangaskiyar ministan kudi na sarauniya Kandakatu daga Habasha kyakkyawar alamace. (Ayukan Manzanni 8:26-39).

Bugu da kari, zaka iya yin amfani da dokar Kur’ani ga Ibrahim wanda Allah yayi na kada ya yi hadaya da dansa Isiyaku. A nan Allah ya ce masa; “kuma muka yi fansar yaron da wani abin yanka, mai girma” (sura al-saffat 37:107)

Jumlan nan ta yanke sharia ta kau da duk kokarin Muhammadu na yin biris da batun sulhu da Allah. Wannan irin wahayi ya yarda da yiwuwar sulhu da Allah tawurin layya.Cikkaken fansa da aka yi wa Isyaku ba an kamala shi tawurin imaninsa ko ayukansa nagari ba, amma tawurin alheri ! Akwai bukata mu sa musulmai su san wannan muhimmiyar aya a Kur’ani, don yadda take magana a kan hadaya maigirma da an riga anyi kafin mutuwar Dan rago na Allah. Har wa yau musulmai suna kokari neman sanin ko wanene ko kuwa menene wannan hadaya maigirma na Allantaka mai kawo sulhu don ceton Isyaku ke nufi. Mun san wannan asiri, Yesu Kristi shine dan rago na Allah na gaskiya, wanda ke dauke da zunubin duniya. Ya kuma ceci duka ‘ya ‘yan Ibrahim.

Wadansu Musulmai sa iya musu cewa Ismailu ne aka so a yi hadaya da shi ba Isyaku ba,don su komar da wannan albarkar abinda aka yi akan Larabawa da Musulmai (sura al-saffat 37:8-14). Har da haka, Kur’ani bai fadi sunan dan Ibrahim wanda aka so a kashe ba. Har zuwa lokacin al- Tabari, masu juya Kur’ani suna kiran sunan Isyaku ne. daga banya ne suka canza zuwa sunan Ismailu.

Musulmai masu tsatsauran ra’ayi zasu ki, wai cewa Kur’ani sau biyar ya ce a (surori al-Anam 6:164; al-Najm 53:38). “Kuma wani mai rai baya yin tsirfa face domin kansa, kuma mai daukar nauyi, ba ya daukar nauyin wani” (Sira al-Anam 6:164)

Wannan aya na kokarin fadi cewa babu wanda zai iya daukan zunuban wadansu wanda shi kansa yana da nauyin zunubi. A amsar wannan, mu sani cewa Kur’ani a wurare da dama ya shaida cewa Kristi bai taba yin zunubi ba. An tabbatar mana da wannan lokaci da aka dauke shi zuwa sama (Surori Al- imran 3:44, 45; al- Nisa 4: 158,171;Maryam 19:19; al-Anbiya 21:91; al- Tahrin 66:12 da sauransu). Bisa ga tsarki na Kristi, duka ayoyi na Kur’ani da suna kin- animcewa da yiwuwar kafara za’a iya amfani da su a tabbatar da gaskiyar yiwuwan wani ya dauki zunuban wadansu”. Wanda bashi da zunubi, zai iya tsayawa a madadin wadansu ya iya daukan nauyin zunubansu”.

Yesu da hadayan da yayi na kansa tawurin kauna na masu zunubi shine kadai amsa da sa zuciya na musulunci. Sunannan Yesu shine ya kasance shirinsa: zai ceci mutanen sa daga zunubansu. “(Matiyu 1:27) mutuwarsa domin mu ya bamu dama na samun jinkai alkawalin Kristi tabbatace ne.” Yi farin ciki, da, ’ya! an gafarta muku zunubanku (Matiyu 9:2; Luka 7:50 da Sauransu).

Muhammadu bai iya furta irin wannan jumla ba. Bai taba yin tunanin mutuwa a madadin musulmai ba. Mutuwarsa da ta zama a banza, don Allah ya dokace shi sau da dama ya roki gafarar zunubansa (Surorin Ghafir 40:55; Muhammad 47:19; al-Fath 48:2; al-Nasr 110:3).

7.09 -- Shaida Na Wadanda Suke Da Dandanawa

Bayan da aka bada Ruhu Mai Tsarki a sakamakon hadaya ta Kristi, manzannin Almasihu sun gane kuma suka yi shaida na fansa ta wurin mutuwar Yesu chikin kauna. Manzo Bitrus ya yi shaida: “domin kun sani aka fansheku, bada abubuwa masu wacewa ba, da su azurfa ko kwa zinariya, daga chikin irin zaman ku na banza abin gado daga ubanninku; amma da jini mai daraja kamar na dan rago mara-aibi, mara chikas, watau jinin Kristi” (I Bitrus 1:18-19).

Manzo Yahaya ya tabbatar da wannan batu “amma idan muna tafiya chikin haske, kamar yadda shi ke chikin haske, muna zumunta da junanmu, jinin Yesu Dansa yana tsarkakemu daga duka zunubi. Idan mun che ba mu da zunubi, rudin kanmu mukeyi, gaskiya kwa bata chikin mu ba. Idan mun fadi zunuban mu, shi mai alkawali ne, mai-adalchi kuma, da zashi gafarta mamu zunuban mu, shi tsarkakemu daga dukan rashin adalchi” (1 Yahaya 1:7-9).

Manzo Bulus ya rubuta: “Gama maganar giciye wauta che ga wadanda suke lalachewa; amma gamu da ake chetonmu ikon Allah che…. Amma mu muna wa’azin Kristi giciyaye, abin tuntube ga Yahudawa, wauta ga Al’ummai; amma ga wadanda an kira, da Yahudawa da Hellenawa, Kristi ikon Allah, da hikimar Allah” (I Korinthiyawa 1:18,23-24).

Rev. Iskandari Jadid ya yi shaida, “Sa’anda ina matashi na sha wahala daga wurin mata hudu wadanda uba na ya aura da jayayya wanda wadannan iyalai namu guda hudu a gida daya mukan yita yi. A cikin natsuwa da tunani na gane abinda Yahaya ya rubuta” Gama Allah yayi kamnar duniya har ya bada Dansa, haifaffe shi kadai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalache, amma ya sami rai na har abada” (Yahaya 3:16).

A Indiya akwai wata mace wacanda bata iya karatu ko rubutu ba, kuma ta haifi ’ya’ya da yawa, wannan mace ta roka ayi mata baftisma, bayan maigidanta wanda da musulmi ne ya zama Krista. Fasto yayi dari-dari akan yi mata baftisma don yana tsammani tana yi haka ne don ta gamshi maigidanta ne. Lokacinda ya tambaye ta abinda ya sa ita musulma tana nema a yi mata baftisma, sai ta amsa cewa, “Yesu Kristi ya gafarta dukan zunubai na a kan giciye kuma ya sa rai madawwami a cikin zuciyata”.

Wace Shaida kai kake da Ita?

Wace aya ta littafi Mai Tsarki take nuna bangaskiyarka sarai? Menene zaka iya fada wa wani akan wanda ya mutu akan giciye dominka? Mu dauki lokaci muyi tunani da adu’a game da shaidarmu zuwa ga musulmai a kasashenmu. Suna cigaba da yaduwa Ba ka ji motsuwa a zuciyarka na marmarin kai bisharar ceto ga musulmai ba har su gane sarai?

7.10 -- Tambayoyi

In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan

Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.

Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.

  1. Me yasa yawancin Musulmai suna tunanin cewa giciyen Kristi ba gaskiya ba ne?
  2. Me yasa wadansu musulmai suna aza Yahuza ne aka giciye a maimakon Kristi?
  3. Sau nawa ne Kur’ani ya maimaita cewa “Babu wanda zai iya daukan zunubin wani”?
  4. Me yasa musulmai sun ce Allah na da ikon gafarta wa wanda ya ga dama, a lokacin da ya ga dama kuma baya bukatar kafara?
  5. Me yasa Musulmai suna bege (na banza) cewa nagargarun ayokansu zasu shafe munanan ayukansu?
  6. Ta yaya bangaskiyar Musulmai akan kadara ke gaba da ceto tawurin bangaskiya cikin Kristi?
  7. Me yasa giciye ya kasance “haram” ga duka musulmai koda shike suna da jajilci a Kur’ani da shari’a?
  8. Menene zai iya zamana a ruhaniyance a bisa zahirin da ruhun dake gaba da giciye ya daddaure Musulmai?
  9. Me yasa Yesu ya ambaci macijin jankarfe wanda Musa ya daga a jeji don bayyana cewa baza’a iya samun ceto ba sai in an ratayeshi akan giciye? Yesun da aka giciye na nuna kwatancin duka muguntar maciji kenan?
  10. Menene dan rago na idin ketarewa ya kawo wa Ibraniyawa bayi a Masar Kuma me yasa Yesu shine Dan rago na idin ketarewa namu? Daga wane hatsari ne zai iya tsare mu kuma me yasa zamu ci namansa?
  11. Anabce-anabce nawa zaka iya samu a Zabura 22 wadanda Yesu ya cika a cewar Bisharu? Wannene a cikin wadannan anabce-anabce kana tsammani zai rinjayi musulmai su yarda cewa da gaske ne aka giciye Kristi?
  12. Me yasa Yesu yayi adu’a “Allah na, Allah na, don me ka yashe ni”? da gaskene ubansa ya rabu da shi? An raba dayantakan Triniti kenan wajen giciye Kristi? Menene ma’nar wannan adu'a?
  13. Me yasa kalmomin Ishaya 53:4-7 suna dauke da alkawarai a Tsohon Alkwali wadanda suka fi rinjayar mutane suna bayyanawa filla-filla cewa Yesu shine kafarar mu? Ka hadace wadannan ayoyi?
  14. Menene azurfa talatin ke nufi a wahayin Zakariya da yadda aka cika wannan anabci a Sabon Alkawali? Yesu Yahweh shine Ubangiji?
  15. Me yasa abinda aka rubuta a Matiyu 20:28 na da Muhammanci sosai kuma zai iya canza al’adu da gargajiyar kowane mutane?
  16. Me yasa Yesu bai boye ba ko ya gudu ko yayi hijira zuwa kasar Lebanon ko Siriya ba ko das hike ya san abinda ke jiransa a Urushalima?
  17. Menene bambancin da ke da Muhimmanci tsakanin adu’ar Yesu ta farko da ta biyu a gonar Getsamani?
  18. Me yasa bayan tashin Yesu daga matattu ya sake zuwa ya tattara almajiransa da suka guje shi don ya koya musu daga Tsohon Alkawali abinda yasa ya zama tilas ne ya mutu?
  19. Bayan Almajran Yesu sun karbi ikon Ruhu Mai Tsarki, ta yaya suka kalubalanci Yahudawa? Menene shirun da Yahudawa suka yi har da sukan da manzanni suka yi musu ke nufi?
  20. Me yasa yakan zama da wuya musulmai su gaskanta labarin giciyen Yesu da ceton da aka kanmala domin su? Menene zai zama adu’armu domin su?
  21. Me yasa Labarin Yesu da mutuwarsa da masanan tarihin nan wato Tasitus da Flavius ke da muhimmanci ga Musulmai?
  22. Wace shaida za’a iya samu a hoton mutum-mutumin da ke nuna mutumin da aka giciye da kan jaki a gida na karkashin kasa a Roma?
  23. Me ya sa jamal Abd-Nasser ya tabbatar tawurin hanyoyin sadarwa cewa Musulmai ai sun san ainihin wanda ya giciye Kristi? Me ne ne ke iya faruwa in an kai wannan magana gaban shari’a?
  24. Ta yaya Litattafan Yahudawa na zamani ke bada labarin giciye Yesu.
  25. Sau nawa ne Kur’ani ya gaya mana yadda Yahudawa suka kashe annabawa?
  26. A fadin rikitacciyar shaida ta sura Maryam 19:33. Menene Yesu ya fada akan haihuwarsa da mutuwarsa? Wace ma’ana ta Littafi Mai Tsarki zamu iya ba wannan aya?
  27. Wane yarda ne ko bambance- bambance ne zaka iya samu a tsakanin shaidar Kristi (sura Maryam 19:33) da rahoton Jibra’ilu akan Yahaya a (sura Maryam 19:15)?
  28. Me ya sa aka kira Allah “mafi girma cikin mayaudara” a cikin zance mutuwar Kristi? Wane sharhi ne Littfi Mai Tsarki yayi akan wannan magana?
  29. Menene babbar yaudarar da Allah yayi wanda yake dangane da Yahudawa da Krista?
  30. Ta yaya Muhammadu ya faranta wa Krista da musulmai rai gaba daya yana amfani da sashen magana wanda ba fi’ili a cikinta ya bayyana mutuwar Kristi? Wandanne ma’ana kashi uku za a iya ba wannan kalma?
  31. Me yasa Kur’ani ya tabbatarda komawar Kristi a sama amma ya musanci mutuwarsa?
  32. Menene a cewar Islama, Kristi nada rai amma Muhammadu matacce ne?
  33. Me ya sa furcin Yahudawa a sura al- Nisa’ 4;157 na da alaman tambaya kuma ba daidai ba ne?
  34. Me ya sa tsananin musun Muhammadu na cewa “basu kashe shi ba (da kuma) basu giciye shi ba” ya bamu dama ta musamman mu tabbatar cewa da gaske ne aka giciye Yesu Dan Maryama?
  35. Yaya malaman musulunci ke bayyana fadin Kur’ani cewa ba a giciye Kristi ba amma an sa shi ya zama kamar wanda aka giciye ne?
  36. Me ya sa yakan zama kokarin banza ne a tabbatar wa musulmi zahiri na giciyen Kristi in shi da kansa bai nema a yi masa wannan bayani ba?
  37. Ta yaya zamu jagoranci Musulmi ya gane cewa shi batacce ne mai zunubi?
  38. Ta yaya Kur’ani ya fada cewa dole dukan musulmai su shiga wuta?
  39. A bayanin Kur’ani na yadda Ibrahim ya yi hadaya da dansa ga madaukaki, me yasa kiran da Allah yayi wa Ibrahim a nan wurin ke bamu dama ta musamman mu bayyana wa musulmai irin mutuwan da Kristi yayi?
  40. Ta yaya zamu tabbatar wa Musulmai ainihin kishiyar wannan furci na Kur’ani” Babu wanda ke kaye da nauyin zunubi da zai iya daukan zunubin wani?”
  41. Ko Kristi Dan Rago na Allah yayi kafara don zunuban duka Musulmai yayinda ya mutu akan giciye, kokuwa dole ne Yesu ya sake mutuwa ta musamman don zunuban musulmai a hanya ta musamman? In Allah yayi cikakken kafara, to, me ya sa Krista ba sa gaya wa musulmai dama ta aljanna wadda ta su ce?
  42. A bisa ga dandanawar ka, wane labari ne na bishara game da wahala da mutuwar Kristi musulmai sun fi amincewa da shi?

Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.

Naku cikin Hidimarsa

Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.

Ku aika da amsoshin ku zuwa:

The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.

Ko

GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY

Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on July 24, 2020, at 12:51 PM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)