Grace and Truth

This website is under construction !

Search in "Hausa":

Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 5 Miracles of Christ

This page in: -- Arabic? -- Cebuano -- Chinese -- English -- French -- Georgian -- German? -- HAUSA -- Igbo -- Indonesian -- Kirundi -- Russian -- Somali -- Telugu -- Ukrainian -- Uzbek -- Yoruba

Previous booklet -- Next booklet

01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI

5 - Mu’ujjizai Goma na Kristi cikin Kur’ani5.01 -- Mu’ujjizai Goma na Kristi cikin Kur’ani

5.02 -- The miracles of Christ - a proof for his divine mission?

Muhammadu ya so ya ja ra’ayin Krista da suke a kasar Larabawa zuwa cikin Musulunci. Ya basu shaidar abubuwan daya ji daga wurin bayi wadanda Krista ne, daga wurin wakilan Ikklesiyun arewacin Yemen, daga wurin matafiya daga Habasha, daga wurin abokansa “Hanifa” wadanda yanzu Krista ne. Labarin Dan Maryamu da mujjizansa sun bashi sha’awa. Ya gane kuma wadannan mu’ujjizan sun fi karfin ikon mutun saboda haka ya kirasu shaida (bayyinaat) na ikonsa na Allahntaka (Surorin al-Baqara 2:87, 253; al-Ma’ida 5:110; Zukhruf 43:63; al-Saff 61:6).

Muhammadu ya fadi mu’ujjizai guda tara da Musa yayi a Misrah, wadanda suma ya kirasu Shaida (surorin al-Baqara 2:99; al-Asra’ 17:101). Amma mu’ujjizan Musa jerin horo ne da azaba da Allah ya gana wa Masarawa saboda a tilasta su su saki ‘ya ‘yan Yakubu daga bauta. Mu’ujjizan Yesu a Kur’ani kuwa albarku ne daga wurin Allah da zasu jagoranci ‘ya ‘yan Isra’ila su dogara ga Isa su kuma yi masa biyaya.

Abinda ya rage wa aya zaki shine Muhmmadu bai iya yin Mu’ujjiza ko mai kyau ko mummuna ba. Bai iya gane abinda ya sa yawancin Yahudawa suka taurare zukatansu, basu karbi Dan Maryama ba amma sun Kishi.

5.03 -- Shaidar Kristi (bayyinaat)

● Cikin sura al-Baqara mun karanta cewa Isa bai iya yin mu’ujjizansa ba ta tare da taimakon Ruhu na Mai Tsraki ba (sura al-Baqara 2:87). Muhammadu ya yi tunanin cewa Allah ya aiko da Jibra’ilu ya karfafa Dan Maryama saboda ya iya yin manyan mu’ujjizansa Da wannan Magana, Muhammadu yace Kristi bai iya yin wani mu’ujjiza da ikon kansa ba. In zai yi wannan aiki, yana bukatar dan sako daga wurin Allah, wanda ya kira Ruhu na Mai Tsarki.

Akan yi kuskuren juya wannan lakabi a ce “Ruhu Mai Tsarki”. A Kur’ani Allah da kansa shine “Mai Tsarki”, kuma ruhu bawansa ne kawai. Ruhu Mai Tsarki bashi da tsarki na kansa kuma bashi da halitta na Allahntaka shi halittan madaukaki ne. Ruhu na Kur’ani ya sha bambam da Ruhu Mai Tsraki na Bishara, ko da shike Muhammadu ya zaci cewa Ruhu na Mai Tsarki shine ainihin Ruhu Mai Tsarki wanda ya karfafa Dan Maryama. A haka Muhammadu yayi kamar a kaikaice ya yarda da dayantakan Trinity Mai Tsarki, domin a Kur’ani ukun nan-Allah, Ruhunsa da Kristi sun aikata mu’ujjizan tare!

Muhammadu bai iya gane cewa Yahudawa sun ci gaba da kin amincewa da shaida ta Manzannin Allah, a maimakon haka, ya kirasu makaryata ya ma kashe wadansu (Sura al-Baqara 2:87).

● A cikin wannan surar (al-Baqara 2:253) Muhammadu ya shaida cewa akwai bambanci tsakanin Manzannin Allah, Ya fi son daya fiye da dayan kuma ya ba Yesu babban matsayi. Allah yayi Magana da Musa fuska-da-fuska wanda bai yi haka da Muhammadu ba. Muhammadu ya karbi wahayinsa daga bakon ruhu wanda daga bisani ya kirashi Jibra’ilu. Muhammadu da kansa bai taba ganin Allah ba, ko ma ya ji muryarsa. Bai taba saduwa da Allah ba.

A Fadin Kur’ani, Allah ya ba Dan Maryama Matsayi sama da Musa, domin ya bashi shaidu na (bayyainaat) tawurin ruhu na Mai Tsarki. Muhammadu ya kada kai bisa ga magabtaka da fadace-fadacen da ke tsakanin Yahudawa da Krista bacin duk wadannan dama da suke dasu (Sura al-Baqara 2:253). A cikin wannan rashin jituwa, Muhammadu ya ga kaddarar Allah ce da Islama zata zama addini na uku da zai fito yayi nasara bisa guda biyun da suke fada. Muhammadu bai sani ba cewa giciyayyen Dan Allah da baratar da masu zunubi da yayi, wanda baya bukatar nagargarun ayuka shine makasudin abinda ke kawo fada tsakanin Yahudawa da Krista Musulmai da Yahudawa sunfi kusa da juna fiye da Krista da Musulmai!

● A cikin sura al-Ma’ida mun karanta daya daga cikin jawabai hudu na Allah wadanda yayi akan Kristi a cikin Kur’ani (Sura al-Ma’ida 5:110). Ya ce: “ka tuna da ni’imata a kanka kuma akan mahaifiyarka, a lokacin da na karfafa ka da Ruhul kudusi”. Sa’annan jerin mu’ujjizan da Isa yayi suka bi baya sun karasa da cewa Allah yakare Isa daga hannun ‘ya ‘yan Israila yadda basu iya kashe shi ba, ko da shike ya zo masu da shaida (bayyinaat.) Amma sun ki shi sun ce, “yana sihiri ne’.

A wannan aya Kristi ya sake bayyana a wanda ke da baiwa kuma ya sami taimako daga ruhun Allah. Wannan ya tabbatar da cewa a Kur’ani Dan Maryama bashi da halitta ko iyawa na Allahntaka. A nan take Muhammadu ya shaida mu’ujjizan Isa irin wadanda ba a iya kwaikwayonsu ya kirasu shaida ta ikon da Allah ya bashi. Muhammadu bai fahinci irin Tawali’u na Krista yayinda ya bada duka girma da daukaka ga ubansa yana cewa, “Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abinda ya ga Uba na yi. Domin duk abinda Uba ke yi, haka shi Dan ma ke yi” (Yahaya 5:19).

● A cikin sura al-Zukhruf mun ga bayyani irin ta kasashen gabas na shida ta Kristi (sura al-Zukhruf 43:63): Ya kusanci Yahudawa da “hikima saboda ya bude idanunsu ga dalilin da suke da sabani da dashi. Watakila an ya yi labarin koyaswar Yesu a Matiyu 7:1 – 28, ya kuma bayyana wannan jawabi a matsayin kokarine na kawo salama tsakanin Krista da Yahudawa. A nan, Isa ya nemi mika wuyansu da biyayya ga Umurnansa.

● A fadin sura al-Saff, Isa ya zo wurin ‘ya ‘yan Israila don ya tabbatar musu da cewa ba a gurbata Attaura ba (Sura al-saff 61:6). Wannan bayyani na Musa akan manufan zuwan Isa ya bamu dama mu nuna wa Musulmai cewa ba a canza Baibul ba, domin, a cewar Kur’ani, aikin Kristi na farko shine ya tabbatar da rashin kuskuren Attaura.

Ko ta yaya, manufan zuwan Isa na karshe da manufan mu’ujjizansa a fadin Kur’ani, shine alkawari wanda Dan Maryama ya bayyana cewa bayansa akwai wani. Wanda zai zo, manzon Allah wanda aka fi yabawa. Da wannan annabci, Muhammadu ya sa maganarsa a cikin bakin Isa! Tun daga wannan lokaci, Musulmai suna ta binciken Baibul saboda su sami inda aka boye sunan Muhammadu wanda ma’anarsa shine “Wanda aka Yaba”. Malamai na Musulmai da yawa suna zaton Muhammadu ne Ruhu mai Taimako (Parakletos) wanda aka alkawarta. Don su sa wannan kalma na Hellenanci ya je daidai da ma’anar Muhammadu, musulmai suka canza wasulan “Parakletos” zuwa “Pariklytos” wanda ma’anarsa shine “wanda aka girmama shi sosai”. A sakamakon haka musulmai suna tuhuman Krista akan boye ko yin karya akan annabcin Isa game da Muhammadu a Linjila ko kuma ma share sunan Muhammadu daga Baibul.

5.04 -- Alamu Na Ban Mamaki Na Isa Da Muhammadu (‘Aayaat)

A cikin ayoyi guda uku na Kur’ani, an kira Mu’ujjizan Isa alamu (‘aayaat) na aikinsa na Alkahntaka (suroyin al-Imran 3:49 – 50; al-Ma’ida 5:114). Kalman da Muhammadu yayi amfani dashi a nan za a iya samunsa a cikin Bisharar Yahaya wanda yake bayyana Mu’ujjizan Yesu. A nan mun karanta, “Wannan ce mu’ujjizar farko da Yesu yayi ya kuwa yi ta ne don ya bayyana daukakarsa”. (Yahaya 2:11 – 12). Mutane da yawa sun gaskata sunan sa yayinda suka ga alamun daya nuna (Yahaya 2:23). Lokacin daya warkar da dan bafade daga nesa, Yahaya ya kira wannan warkaswa wani alama da Yesu yayi (Yahaya 4:54).Yayinda mutane suka ga wannan alama (na ciyar da mutnae 5000) sai suka ce, “Lalle, wannan shine annabin nan mai zuwa duniya!” (Yahaya 6:14). Yanzu fada Yesu ya ga sun zo a guje don su nada shi sarki, domin sun ga mu’ujjizan da yayi na basu abinci, sai ya janye.

Yesu bai aikata wadannan mu’ujjizai domin mutane su gaskanta dashi ba, amma domin su gane kaunar sa, ikonsa da ikonsa na Allahntaka. Yesu bai so mutane su bishi don mu’ujjizansa ba, amma ya bukaci tuba da sabontuwar rayuwa.Yesu ya fadakar da mutane yace “in ba mu’ujjizai da abubuwan al’ajabi kuka gani ba, ba yadda za ayi ku bada gaskiya” (Yahay 4:48) sau da yawa a Bisharu mun karanta yadda Yesu ya kwabi wadanda ya warkar da kada su fadi wanda ya warkarda su. (Matiyu 9:39; markus 3:12; 5:43; Luka 5:14; 8:56; 9:12).

Lokacin da aka tsananta Yesu kuma aka yi burgar za a kashe shi a Urushalima, taron mutane da yawa da suka zo kallon mu’ujjizai ne sun guje shi.Almajiransa ne kadai, wadanda suka suka furta zunubansu a gaban Yahaya mai baftisma, tawurin tuba an ladabtardasu, sune suka kasance amintattu ga Kristi. Sun ga daukakarsa lokacin da aka tsananta shi har ya mutu akan giciye. Sa’anda Yuhudawa suka gwada Yesu, sun bukaci alama daga gareshi don nuna ikonsa da aikin daya kawo shi, ya amsa musu yace: “ku rushe haikalin nan, ni kuwa in tadashi a cikin kwana uku” (Yahaya 2:18 – 22). Ya kara da cewa, “’yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za nuna musu, sai dai ta Yunusa” (Matiyu 12:39 – 40; 16:4).

Shaida da alamu da Muhammadu ya ba Isa a Kur’ani na kokarin kawo masa abinda ya riga ya ki. Saboda haka kada mu bayyana alamun Kristi ga Musulmi don mu’ujjizai ba ne amma mu jaddada cewa suna nuna girmansa, kaunarsa, tawali’unsa, tsarkinsa da ikon sa. Bari a girmama Kristi yayin da aka ambata mu’ujjizansa.. Duk warkaswa wanda bai kai mutum ga tuba da sabontuwa ba ya kasa kai waga zurfin bangaskiya cikin Yesu.

5.05 -- Kristi Yayi Magana Sa’anda Yana Jariri

Sau uku mun sami rahoton abin ban mamaki a Kur’ani game da jawabin da jariri Dan Maryama yayi lokacin da yake kwance a komin dabbobi. An fadi cewa yayi magana sau biyu (Surorin al-Imran 3:46; al-Maida 5:110). Cikkaken jawabinsa na samuwa a Sura Maryam (19:24 – 33). Labari mai ban al’ajabi na yadda Isa-jariri wanda ya iya yin Magana, malamai sun yi bayaninsa a hanyoyi dabam-dabam. Wadansu sun ce, Isa ya bukaci ‘yan mintoci ne, wadansu sun ce sa’oi na iya furta bakake, Kalmomi da jumloli babu kuskure. Bargonsa ya gama ginuwa a dan kankanin lokacin, haka suka fadi.

Me yasa Malamai na Musulunci sun gaskata kuma suna tattaunawa akan wannan abu mai faruwa bisa ga ikon Allah? Sun karanta cikin Kur’ani cewa Kristi “kalman Allah ne” cikin jiki. Madaukaki ya koya masa Attaura, Karin Magana na Suleimanu, Linjila, da kuma Littafi na ainihi a sama, kafin haihuwarsa (sura al-Al’imran 3:48). An haifeshi cikin duniya cike da sani, Ilimi da kuma iyawa. Dole ne ya furta kalmomin Allah kullum tun ranar haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa shi ya zama kamar bullowan wahayi ne daga wurin Ubangijinsa.

Kur’ani ya tabbatar da cewa Dan Maryama ba Kaman sauran Mutane bane, amma ruhun Allah ne cikin jiki. Ya sauko daga wurin Madawwami (sura al-Im’ran 3:45) kuma yana da sani sosai ya iya daukan abubuwa na ruhaniya fiye da kowane dan adam.

Wadannan maganganu a cikin Kur’ani sun zo kusa da fahintar Krista na bayyanuwar Dan Allah cikin jiki a cikin Linjila. Amma a nan an haifi Yesu a ainihin Mutum jariri a nannade cikin tsummoki. Uwarsa Maryama bata gaya wa Luka Likita, ba Hellene wani abu game da jawabai na danta wadanda yayi nan da nan bayan an haifeshi ba, domin a jariri bai iya yin Magana ba don yana bukatan lokaci ya ginu (Luka 2:40-52).

A ina irin wannan labari ya fito? A cikin bishara ta yarantaka a Afokrifa na Mutanen Siriya da Krista ‘yan Koftik, za a iya samun irin wannan ambato. Iyaye mata sukan yi wa jariransu wakoki game da jariri Yesu saboda su rarrashe su suyi barci. Yau an san inda aka sami labarin jariri Yesu mai yin Magana.

Muhammadu ya ji irin wadannan labaru na yara daga wurin bayi daga Siriya da Krista ‘yan Koftik kuma ya yarda dasu! Ya gaskata wadannan labaru fiye da shugabannin Ikklesiya wadanda basu hadasu ba a cikin Linjila domin tatsuniyoyi ne basu faru ba. Saboda haka Muhammdu ya bayyana a matsayin mai neman gaskiya ne ba annabi ba. Bai iya bambanta tatsuniya da gaskiya ba.

Game da abinda jawabin jariri Dan Maryama ya kunsa (sura Mayam 19:24 – 33), da farko dan ya so ya karfafa uwarsa domin ta haifeshi babu aure. Ta sani za a iya jifanta da duwatsu. Saboda haka jariri Isa ya karfafata da albishir cewa ta haifi mutum wanda fitacce ne a kalkashin itacen dabino a Hamada.

A harshen larabci wani kalma na fitacce shine “Suriyun” jam’inta shine “Surawaa”, “asriyaa” ko “saraat” (duka sun samu tushe daga S-R-W a cikin Larabci). Amma makaranta Kur’ani masu kishi sukan canza wasula da ma’anan wannan kalma zuwa ‘yar karamar korama (wanda a larabci “sariyun” ne) in an dauke shi daga S-R-Y da jam’oin ‘asriyat’ ko ‘suryaan’.

Musulmai masu karatu sun ji haushi don Isa tun yana jariri an fifita bisa Muhammadu, saboda haka sun canza wasulan da ma’anan daga fitacce zuwa ‘yar karamar rafi ko dashi ke yadda suka juya bashi da ma’ana sosai.

Wannan sabon jariri ya gaya ma uwarsa da ta girgiza itacen dabino, nunannun ‘ya ‘yan dabino zasu fado, sai ta ci saboda ta sami karfi daga wahalar haihuwa. Wace irin dabara ceta Makiyayi! Taruwan maza basa iya girgiza itacen dabino. Ta yaya karamar uwa zata iya aikata wannan bayan haihuwa? A zamanin Muhammadu, rayuwan Makiyaya ya nunka na mata da uwaye wahala sau biyu.

A karshen jawabinsa na farko Isa ya gaya ma uwarsa abinda zata fada wa duk wanda ya tambaye ta game da asalin wannan sabon yaro. Ita kuma ta yi wa Allah alkawalin yin azumi kuma baza ta yi ma kowa Magana a wannan rana ba.Ta haka, zance na farko na cewa jariri Isa ya koya wa uwarsa zanba, dabara da kuma karya don ceton ta daga hatsari.

Rahoton ya cigaba da nuna yadda jariri yakare uwarsa daga mutanen kauyensu masu jin haushi tawurin gabatar da kansa a matsayin annabi mai albarka a cikin jawabinsa na jarirantaka a Kur’ani.

Wadanda sun duba wannan labari sosai zasu ga an gwama mafarki da gaskiya wanda ya zama wahayi. Duka Kur’ani an cakuda gaskiya ne da tatsuniyoyi.

5.06 -- Isa Ya Halicci Tsuntsu

Daga Litattafan Afokirfa an sami wannan labari: Dan yaro Isa ya gina tsuntsu daga yumbu, ya hura masa lumfashi ya kuma yi rai ya tashi! (Surorin al-Imran 3:49; al-Ma’ida 5:110). Za mu so mu mance da irin wannan tatsuniya ta Dan Maryama, amma ba za muyi haka ba don an bada shi a sura wurare uku.

A cikin sura Al’Imran Isa ya gaya wa ‘ya ‘yan Isra’ila “zan halitta muku kamannin tsuntsu daga yumbu”. A cikin sura al-Ma’ida Allah, bayan tafiyan Isa sama ye tabbatar da cewa, “ka halicci kamannin tsuntsu daga yambu” wannan mu’ujjiza an tabbatar dashi a Kur’ani a matsayin ya auku ne da abinda ke aukuwa. Wannan tabbaci kashi biyu ya sa wannan bayyanin na da muhimmanci.

A duka wadannan wurare mun ji cewa Isa ya iya halittar abu mai rai daga abinda bashi da rai. A cikin Larabci, kalma “halitta” (khalaqa), Allah ne kadai zai iya. Shine kadai ya halicci komai. Amma wannan muhimmiyar kalma na “halitta” an lakaba wa Isa. Shi kadai ne cikin ‘yan adam ne wanda ya zama mahalicci a fadin Kur’ani wanda ya iya halitta rai daga mataccen abu. Kristi a cikin Islama ya bayyana a mahalicci.

Muhammadu, ya iyakace wannan daraja ta Dan Maryama sa’anda ya ce “da taimakon Allah”! Sau da yawa a cikin Kur’ani in yana Magana akan mu’ujjizan Kristi. Saboda haka zamu iya tambayan musulmai masu zurfin tunani, “ka gaskanta cewa Kristi da yardan Allah ya iya halittan tsuntsu daga abu marar rai”? Zai iya baka amsa “tabbas Kur’ani ya tabbatar da wannan sau biyu”! Mu kuma zamu fada masa cewa dan Maryama Mahalicci ne na musamman da iznin Allah!

Wannan labari na yarantakan Kristi na da wani abin ban mamaki kuma. Isa ya dauki wannan tsuntsu daya gina da yumbu ya hura masa lumfashi. Wannan yumbu ya sami rai, tsuntsun ya tashi ya tafi. A fadin Kur’ani, Isa na da “Lumfashin bada rai” a cikinsa – da iznin Allah.

A cikin Baibul, Allah ya hura “Lumfashin rai” cikin Adamu, haka aka halicci mutm na farko (Farawa 2:7). A daren Ista Kristi ya lumfasa wa firgitattun almajiranse ya ce musu “Kukarbi Ruhu Mai Tsarki” (Yahaya 20:22). Sa’annan almajiransa suka farfado, domin Kristi ruhu ne mai bada rai (1 Korintinyawa 15:45).

Muhammadu a bayaninsa bai je da zurfi ba. Lokacinda Isa ya hura lumfashi cikin wannan abu mara rai, abin bai zama mutum ba, ko kuwa haifaffen dan Allah, amma wani abu Kaman tsuntsu! Muhammadu bai yi musun cewa Yesu yana da Ruhu mai bada rai na mahalicci ba.

Labarin halittan tsuntsu ya ba malamai masu yin sharhi akan Kur’ani ciwon kai, don in Isa ya iya ya halicci tsuntsu rayayye daga abu marar rai, da yardan Allah, to, shi yana bisa duka mutane har ma Muhammadu. Wadansu masu juyi sun rubuta, “Isa ya so ya halicci dabba mai kafa huda ne ko kuwa tsuntsu mai firiya amma duka basu yiwu ba. Amma sakamakon wannan kokari shine “jemage” wanda ba tsuntsu bane ba dabba bace. Zamu iya ba irin wadannan masu kawo suka amsa”, Jemage shine tsuntsu da aka gina shi musamman, don yana dauke da motsi irin na radar a bakinsa wanda yana taimakonsa yayi firiya da dare Kaman jirgin sama.

5.07 -- Warkar Da Makafi

Bayan mu’ujjizai biyu wadanda akwai rashin gaskiya a ciki wanda dan yaro Isa yayi wadanda Muhammadu ya dauko labaran daga Afokirfa ne, mun cigaba da karanta game da Kristi wanda Allah ya hakikance cewa ya warkar da makafi da yawa (Surorin al-Imran 3:49; al-Ma’ida 5:110).

A cikin wannan rahoto zamu iya ganin jinkai na Kristi zuwa ga musakai wadanda basa iya ganin hasken rana kuma suna tuntube cikin duhu. Dan Maryama a fadin Kur’ani bai aikata mu’ujjizai don neman alfarma wurin sarakuna da masu mulki ba amma don taimakon marasa lafiya, matalauta da marasa galihu. Kauna da jinkansa sun sa shi ya aikata wadannan alamu.

Kalma ta “warkarwa” da larabci shine (bari’a) wanda yana da nasaba da “barata” ko “tsarkakewa”. In cuta ta zama horo ne daga Allah don boyayyun zunubai, to, Kristi ba warkar da cutar kadai yake yi ba, har da zunubin ma yana kawas wa.

Yesu bai bude idanun mutane da wuka mai kaifi ba ko kuwa wata na’ura, ko magani ba, amma da Kalmar bakinsa. Bai yi sihiri ko amfani da iska ba don’yantar da masu shan wahala da bakin ciki daga ‘ikon duhu tawurin kalmansa mai iko Kaman ba, yadda ya saba muhammadu ya kara da cewa “da Iznin Allah” ko ta yaya, kowa zai iya sanin ikon Yesu Kristi da kaunarsa zuwa ga wadanda ba a kula da su ba cikin Littafin musulmai.

Daga Kur’ani musulmi ba ya iya sanin yadda , inda, a ina ne ko kuwa wanene Yesu ya bude idanunsa ba, saboda haka kuwa nassi na Kur’ani na bukatan shaida ta wadanda suka gani a cikin Linjila. Yakamata mu bude ma musulmai masu sha’awa irin wadannan wurare, amma kada mu karanta musu da kanmu. Mu karfafa su su karanta da kansu, saboda su bi Littafi Mai Tsarki su kuma ga Yesu cikin idanun zukatansu. Da haka zasu gane cewa Yesu bai taba tilasta kowa ya karbi taimako ko warkaswa ba, amma yakan jira sai mabukacin ya zo wurinsa ko ya kirashi don neman taimako. Yesu ya so ya dora nawayan neman warkewa akan wadanda suke shan wahala, sai sun roka a warkarda su. Ya falkadda su don su dogara gareshi da ikonsa saboda ya iya kwance nauyin kayansu. Da wuya mutum kan sami warkaswa in bai dogara ga likitan Likitoci ba. Kristi baya tilasta wani karban alherinsa ba, amma yakan gina yarda, bangaskiya da kauna zuwa gareshi mai fansarsu. Yesu ya nuna hakkin mutum a cikin aikin warkaswa tawurin fadi “Bangaskiyarka ta warkar da kai” (Matiyu 8:22; Markus 5:34; 10:52; Luka 7:50; 8:48; 17:19; 18:42). Duk wadannan bakin abu ne ga musulmi. Bai san mai ceto ba ko mai taimako. Dagora ga Kristi, mai Fansarsa a hankali za a gina shi har ya ginu a cikinsa a ruhaniyance.

5.08 -- Isa Ya Warkar Da Kutare

Rahoto biyu na Kur’ani akan tsarkakewa da warkasda kutare, shaidar Isa da ta Allah sun tabbatar da wadannan Mu’ujjizai (surorin Al’Imran 3:49; al-Ma’ida 5:110). Kalmar da aka yi amfani da ita ta warkar da kutare an rubuta ta a mufuradi ne, amma ma’anarta a Jam’i ne wanda ya hada duka marasa lafiya. Kamar yadda ya kasance da makafi, ba a yi nufi Kristi yayi mu’ujjiza daya bane kawai, amma jerin warkaswa na ban mamaki wadanda Yesu yayi wa kutaren.

In ka taba saduwa da irin wadannan masu shanwuya a Indiya, da gutsurarrun yatsotsi da munanan fuskoki suna gudu zuwa gidan mai don suyi bara, zaka fahimci kaunar Yesu, zatinsa da nasararsa bisa kyama da tsoro na kamun cuta, bai kori kutaren don kazantattu ne ba, amma yayi Magana dasu har ma ya taba wadansun su. Ya gina gada ta bangaskiyarsu saboda sugane: “wannan Yesu yana kauna ta!” Yesu na da karfi fiye da kuturta! Zai iya kuma warkar da ni (Matiyu 8:1 – 4; Markus 1:40 – 45; Luka 5:12 – 16).

Lokacin da Yesu ya warkarda kutare goma ya sa rai da su zama da bangaskiya mai girma. Sun gaskata wanda ya furta kalma zuwa garesu cikin kaunar Allah wanda suka ji shi tawurin sa. (Luka 17:11 – 19).

Abinda Kur’ani ya gaya mana gaskiya ne da ke bukatar bayani daga Bishara da kuma namu shaida: cewa ya tsarkake mu daga duka zunubi da kazamta.

A warkaswar kutare zamu iya bayyanin yadda gafarar zunubai yake. A wadansu kasashen Musulunci an dauki kuturta a matsayin horon Allah ne bisa ‘yan tawaye ko kuwa boyayyun zunubai. A nan rahoton Littafi Mai Tsarki akan warkas da mai ciwon inna da Yesu yayi zai taimaka. Ya sa rai Yesu zai furta kalma ta “warkaswa,” amma a maimakon haka ya ce, “Dan a yi farinciki, an gafarta maka zunubanka” Yayinda malaman Attaura sun zaci Yesu yayi sabo ne, ya juya garesu yace, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? Wanene ya fi sauki? A ce, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi kayi tafiya’? Amma domin ku sakankance Dan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya - “sai y ace wa shanya – yyen – “Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida”. Shi kuwa ya tashi ya tafi gida” (Matiyu 9:1 – 8).

5.09 -- Tada Matattu

In ka karanta dan gajeren labari wanda aka tabbatar sau biyu a Kur’ani cewa Yesu ya iya tada matattu, lumfashinka zai iya tsayawa na dan lokaci (surorin al-Imran 3:49; al-Ma’ida 5:110). A cikin wadannan ayoyi biyu zaka same shi a jam’i ne ba mufuradi ba! A Larabci wannan na nufi an tada mutane fiye da daya daga matattu. A bu mai kyau ne mu haddace nassoshi a Linjila da suka yi Maganar tada yarinya, matashi da babban mutum daga matattu wadanda Yesu yayi, kuma ka karanta wadannan nassoshi ga musulmi mai Sha’awar haka. (Matiyu 9:18 – 26; Markus 5:21 – 43; Luka 7:11 – 17; Luka 8:40 – 56; Yahaya 11:1 – 45).

Kur’ani yayi amfani da salon Magana kashi biyu a kan tada matattu da Yesu yayi. Cikin sura al-Imran (sura 3:49) ya ce, “I na rayar da matattu”.

A daya ayar (sura al-Ma’ida 5:110) Allah ya tabbatar cewa, “lokacin da kake fitar da matattu”.

In ka san wani Musulmi wanda ya nuna sha’awa cikin addinin Krista ka iya yi masa wannan tambaya bisa ga wadannan shaidu cikin Kur’ani, “Wake da ikon tada matattu”? Zai amsa ba wani “sai Allah”. In ka sake tambaya, “yanzu kana cewa Kristi Allah kenan? Tunda ya tada matattu a kalla uku? Zaka iya jin shi yace “A uzu billahi”! In ka cigaba da tambaya, “Amma a kur’ani akwai ayoyi biyu inda Kristi ya tada matattu, “za ka iya jin amsarsa bayan haka za a ce “da izini na!” Kristi bai iya tada matattu ba, Saboda haka Allah ya aiko masa Jibra’ilu don ya karfafa shi, saboda ya iya kamala mu’ujjizai na tada matattu don ya girmama Allah! In ka cigaba da yambaya a hankali, “amma ka gaskanta cewa Allah da Ruhu Mai Tsarki da Dan Maryama tare ne suka tada matattu? Za ka ji cikin shakka, “kwarai, an bayyana wannan a Kur’ani” Zaka iya ce masa, “ka bada gaskiya akan aikin dayantaka da aikin Triniti, ko dashi ke bai tabbatar da shi yadda yake ba. Bai zama dole ba musulmi ya amince da dukan ra’ayin mu ba. Amma zai iya zama taimako gareshi ya ji saboda abubuwan da aka tabbatar a Kur’ani, don ya fara tunani a wata hanya.

Zahiri na Dan Maryama ya tada matattu abin mamaki ne wanda zai sa ka tambayi kanka abinda ya sa Muhammdu ya sa wannan shaida a kur’ani. Wata kila don ya nuna cewa addinin Islama na da dangantaka da addininsa.

Mun gaskata shaida na wanda ya ci nasara da mutuwa a Kur’ani zai yi aiki Kaman yisti, kuma zai bude idanun ruhaniya na musulmai, saboda su sansance Kristi na gaskiya wanda yake da rai madawwami a cikinsa. Sa’annan su fahimta cewa Kristi zai iya bada rai madawwami ga duk wanda ya roke shi. Gaskiyar da Kristi ya tada matattu ya zama kalubale ga duk ‘ya ‘yan Ibrahim, Yahudawa da Musulmai. “Wanda ya gaskata da Dan, yana da rai madawwami. Wanda ya ki bin Dan kuwa, ba zai sami rai ba” (Yahaya 3:36; 1 Yahaya 5:12).

5.10 -- Masanin Abu Duka

A cikin sura al-Imran zamu ga wani bakon aya, a fadinta Isa ya gaya wa Yahudawa zai bayyana masu abinda suka ci asirce da kuma dukiyar da suka boye a tukunya.

Wannan labari da akwai shakkar aukuwan sa na da bayyanai iri-iri. Yahudawa da yawa basa bin dokan Musa Kaman yadda ake bukata, kuma asirce sukan ci harantattun abubuwa. Wadansu basa azumi a ranakun da a ka ka’ida sai su ci abinci da suka ga dama a asirce. Wadansu sukan tara dukiya su boye a maimakon bada su sadaka ga fakirai da baki daga Makka.

Al-suyuti a sharhinsa, ya bayyana: Isa sa anda yana yaro yana wasa da sauran yara sai ya ce da su, “Zan iya yi muku annabcin abubuwanda iyayenku sukan ci in ba ku a gida da abubuwan da sukan boye muku”. Sa’anda ‘ya ‘yan nan suka tambayi iyayensu, iyayen suka yi mamaki, “Wanene ya bude muku wannan asiri”? Yaran suka ce Isa ne, sai iyayen sun hana yaran zuwa yin wasa da Dan Maryama kuma sukan kullesu a cikin gida.

Lokacin da Isa ya tambayi iyayen yaran abinda yasa bai sake ganinsu ba sai suka ce ai basa gidane a wannan lokacin. Isa ya amsa musu yace, ‘Amma na ji su suna surutu a bayan gidajenku”, sai suka gaya masa “wadannan ‘ya ‘yan aladu ne da suka jin yunwa”. Sai Isa yace, “kuma da gskiya! Aladunku ne kadai suke kuka a bayan gida”. Sa’anda iyayen sun je su dubi ‘ya ‘yansu, sai ga Kalmar Isa ta cikin. Duka yaran sun zama aladu!

Wannan mugun labari na tunanin batanci an yi shi ne don kai wa Yahudawa wadanda basu taba kiwon aladu ba ne hari, da kuma Yesu da kansa, saboda a hana yara zuwa wurin Isa don zai bayyana gaskiya. Ko ta yaya wannan nassi na kur’ani na tabbatar da cewa Isa na iya ganin kowane boyayyen abu. A fadin Muhammadu, Isa na da idanun da babu abinda zai iya kare su ganin duka asiri. A cikin Bishara ta Yahaya zamu iya karanta cewa Isa ya iya gani har hanji da tunanin mutane. Ba sai an fada masa wani abu akan kowane mutum ba “Ya san abinda ke cikin zuciyar kowane mutum” (Yahaya 2:24 – 25).

A cikin wannan aya, Kur’ani na tabbatar da cewa Isa masanin abu duka ne amma akwai kaskure daga karshe. Isa ba abinci ne da dukiya yake gani da idanunsa na mai fansa ba. Yana bude boyayyun zunuban mutane kuma yana sanin wadanda suke bidan adalci, tsarki da gaskiya. Yana ao yayi, ya tsarkake ya kuma sabonta kowa, kuma baya so ya kwace dukiyansu.

Muhammadu ya sha wahalar shirya dagantaka tsakanin ‘yan gudun hijira wadanda suka zo daga Makkah da ainihin mazauna Madina. ‘Yan gudun hijira daga Makkah basu da aikin yi, basu da gidaje kuma basu da wani gado daga ‘yan ‘uwa. Sabanin haka, musilmai ‘yan asalin Madina sun cigaba da karuwa cikin arziki. ‘Yan asalin Madina sun ajiye ‘yan gudun hijira a gidajensu da alkwarin zasu kula dasu Kaman ‘yan ‘uwansu na jiki amma abin bai yiwu haka ba. Mutanen Madina sukan ci abinci mai kyau sa’anda ‘yan gudun hijira suka fita, kuma sukan boye arzikinsu don kada masu hijiran su gani. Muhammadu ya ji labarin irin wannan hali kuma yana so ya kwace wannan dukiya. Sai yace, “In Isa ya sake dowawa zai fada muku abubuwan da kuka ci a asirice da abubuwan da kuka boye a gidajenku domin yana iya ganin kome”.

Mu yi tunani akan wannan shaida ta Kur’ani kuma yayinda muke ba Musulmai shawara ta ruhaniya, mu taimakesu su gane da cewa dukan mu muna bukatar gwaji da tona asiri tawurin kaunar Yesu Kristi da kuma tawurin gaskiyarsa da yawa. Kudaden Krista wadanda suka boye sun isa a yi amfani dasu a kai wa dukan duniya bishara, in za a iya iza mutane su rabu da dukiyoyinsu.

5.11 -- Tebur Daga Sama

A cikin Sura al-Ma’ida (5:112 – 115) zamu iya samun amsa kuwwar yadda Yesu ya ciyar da mutum 5,000 a musulunce. Zamu juya wannan nassi yadda yake, saboda ma iya fahimtar irin tunanin Muhammadu da halayyan musulmansu wanda zai zama tushen zancen mu da su:

“112, A lokacin da Hawariyawa suka: “Ya Isa dan Maryama! Shin, Ubangijinka yana Iyawa Ya saukar da kabaki a kanmu daga sama”?Isa yace, “ku bi Allah da takawa idan kun kasance muminai”.

“113, Suka ce: “Muna nufin mu ci daga gareshi ne, kuma zukatanmu su natsu, kuma mu san cewa lalle ne, ka yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga masu shaida a kansa”.

“114, Isa dan Maryama yace: “Ya Allah, Ubangijin mu! Ka saukar da kabaki a kan mu daga sama domin ya zama idi ga na farkonmu da na karshen mu, kuma ya zama aya daga gareka. Ka arzuta mu, kuma kaine mafificin masu arzutawa”.

“115, Allah yace: “lalle ne ni, mai saukar dashi ne a kanku, sa’annan wanda ya kafirta daga gareku, to, lalle ne ni, ina azabta shi, da wata azaba wadda bani azabta taga kowa daga talikai”.

Akan wannan irin labari daya fito daga tunani game da ciyar da mutum 5,000 zamu ambaci wadannan:

● Sau da yawa Muhammadu yakan bambanta Krista bisa ga girmansu kuma yakan kirasu almajirai (sabon shiga), masu dokin taimakawa ko yaki, masu imani da ke adu’a, mabiya da shaida (Al’Imran 3:52 – 53). A cikin labarin tebur daga sama Isa ya kira almajiransa sabobin shiga.

● A Kur’ani, ba a dauki Isa a matsayin “Ubangiji ba”, amma Allah shine Ubangijinsa. Isa kullum yana kalkashinsa ne.

● Bayan Isa yayi huduba mai tsawo a Hamada, almajiransa sun ji yunwa. Basu yi hakurin jiransa har ya wadatar musu da abinci ba, amma sun jarabce shi sun rena ikon Allah na ko zai iya taimakonsa. Ainihi basu gaskata kaunarsa ba amma sun so su gwada shi.

● Isa bai kalubalanci almajiransa su gaskanta ba, amma su ji tsoron Allah. Kaunar Allah da kuma dogaro ga alherinsa ba su ne manyan kawunan Magana a Islama ba, amma mika wuya ga Allah da tsoro da ban girma zuwa gareshi.

● Musulmai basu da tabbacin fansa kuma babu salama a cikinsu domin babu Ruhu Mai Tsarki a cikin wannan addini. An dauki Jibra’ilu a matsayin ruhu na Mai Tsarki, saboda haka musulmai na ta neman kwakkwaran shaidar bangaskiyansu. Sun so su zama shaidu na teburin ba na aikin Isa ba. Teburin da abubuwan da ke a kai sune sa zuciyarsu.

● Abin ban mamaki a nan shine, Dan Maryama bai yi adu’a ga Allah ba, amma ga “Allahumma” (Elohim). Wannan suna ga Muhammadu ya zama kamar Mabudi da ke taimakawa in za a sami amsar adu’a da wuri. Elohim sunan Allah ne cikin jam’i kuma yana dauke da yiwuwar dayantakan Triniti Mai Tsarki. A cikin Kur’ani Isa ya kira Allah na Tsohon Alkawali “Allah (Allahumma) Ubangijin mu”. Wannan na da sabani da “Ubangiji ya bayyana wa Musa sa’anda ya ce, “Nine UBANGIJI Allahnka”! Muhammadu ya so ya masuluntar da Allah na Tsohon Alkawali.

● Isa a Kur’ani ya kira wannan liyafa daga sama Idi na musamman don kowa da kowa, na duka almajiran Kristi manya da kanana. Watakila Muhammadu cikin tunaninsa ya hada jibin Ubangiji da mu’ujjizan ciyar da mutum 5,000. Ya kira wannan liyafa daga sama “alama ta mu’ujjiza. Sura ta biyar a Kur’ani ana kiranta “babba Biki” (al-Ma’ida).

● Dan Maryama ya kuma roki Allah ya wadatar wa mabiyansa abincin da suke bukata kullum. A cikin Islama, addini sana’a ne (sura Fatir 35:29 – 20) kuma dole a sami kyakkyawan nasara. Allah a cikin musulunci ba Uba bane amma sarkin musulmine wanda yana biyan bukatar musulmai in ya ga dama.

● Nan da nan Allah ya amsa adu’ar Isa, wanda abin yabo ne a Islama. Tun Isa bai gama adu’ar ba, sai Allah ya fara sauko wa almajiran Isa da suke jin yunwa wannan teburi sama.

● Wata mummunar illa a mu’ujjizan Isa ita ce. Allah yayi kashedi cewa zai hori duk almajirai masu shakka da rashin bangaskiya da mummunar horo mafi girma a wannan duniya da na gaba. An yi wannan burga har zuwa ga Musulmai sai in sun bada gaskiya cikin mu’ujjizan Isa yadda aka rubuta a Kur’ani.

● Malamai masu sharhi a Kur’ani sun tattauna akan ire-iren abincin da ke kan wannan tebur fiye da wanda ya wadatar da wannan abinci daga sama. Musulmai zasu so su sani ko akwai giya, naman alade da sauran harantattun abinci a aljanna, amma su mance da wanda ya kawo teburin. Yawancin su basu yi la’akari da cewa a Islama, Dan Maryama na da daman yin godo domin mabiyansa.

● Sa’anda ka gaya wa Musulmai cewa Yesu ga riko kifi biyu ne da gurasa biyar yayinda ya ciyar da mutum 5,000, zaka ga sun nuna rashin jin dadi don gurasa da kifi ba abinci ne na musamman da suke bida a aljianna ba ne.

● Amma in ka sa a zuciyar masu sauraron ka tunani na cewa Yesu ya yi godiya ne akan dan abinci da ke hannunsa, wannan abinci kuwa ya yalwata. Sa’annan zaka iya bayyana ma Musulmai cewa samun kudi da abinci basu ne shaidar gaskiya ba, amma bangaskiya da godiya zasu kawo albarku ga mutane da yawa.

● Mun sani cewa Yesu ne za a kafa masa ido ba mu’ujjizar yalwata gurasar ba. Ubangijin mu ya tabbatar mana cewa yana bada abinci kullum ga wadanda suke binsa, suna dogara gareshi da kuma yi masa godiya kafin ma su ga abincin. Wannan ya saba da abinda Kur’ani ke koyaswa. Alherin Allah Uba a Baibu zai iya kawar da tunanin sarkin musulmi wanda ke ceton wanda ya ga dama kuma ya karkatar da wanda ya ga dama.

● Muhimmiyar jawabi na wannan mu’ujjiza na Kristi a Kur’ani shaida ne cewa shi kadai ne matsakanci tsakanin Allah da mutane. A asirce, shine tsakiyar wannan babbar mu’ujjiza wanda kowane musulmi zai iya fahimta in ya yarda. Adu’a cikin sunan Kristi ya zama mai yiwuwa ga musulmai ma. Kristi ya bude mana kafa zuwa ga Allah. Babu wata hanya zuwa wurin Uba sai ta wurin sa, “Domin Allah daya ne, matsakanci kuma daya ne tsakanin Allah da mutane – Almasihu Yesu, mutum”. (1 Timoti 2:5, sura al-Anbiya 21:28).

5.12 -- Isa Mai Bada Dokoki

A Kur’ani akwai ayoyi da yawa wadanda sun shaida hukumcin Isa bisa Attura. Nassoshi guda biyu a ciki sun kira wannan hali da yadda yake fassara Tsohon Alkawali alama da shaidar aikinsa na Allahntaka (surorin Al’Imran 3:50 – 51; al-Ma’ida 5:46 – 47; al-Zukhruf 43:63). Wadannan ‘yan batutuwa akan mu’ujjizansa na aikin dokoki ya isa abin tunani.

● Allah ya aiki Kristi cikin duniya ya tabbatar da rashin kuskuren Attaura. Me yasa musulmai sun nace da cewa an gurbatar da Attaura? Kur’ani da kansa ya musanci wannan sau da yawa. A kari, Kristi Kalmar Allah ne cikin jiki haka kuma ya zama madadin Attaura a cikin rayuwansa. (Surorin al’Imran 3:50; al-Ma’ida 5:46 d/s).

● Allah da kansa ya koya wa Dan Maryama – kafin a halife shi cewa Attaura, Karin Magana ta Suleimanu, Linjila da Littafi na Asali da duka Litattafan da suka gabace shi (sura Al’Imran 3:49). Domin haka Isa ya iya zuwa wurin ‘ya ‘yan Israila da hikima ya kuma bayyana musu amsoshin tambayoyin da suka gagara a cikin Shari’a kuma yak au da dalilin da ke rarrabe su.

● A fadin Kur’ani, Kristi yana da iko ya canza ko ya soke wadansu dokokin Allah a cikin Attaura kuma ya ‘yantar da mabiyansa daga kanginsu. Shi yasa a Islama, Isa mai bada dokoki ne. Shi baya karkashin doka Kaman mai zartarwa. Wannan ma yafi gaban mu’ujjiza ga musulmai, domin a garesu, Allah ne kadai mai bada doka da mai bayyana Shari’a. A cewar Kur’ani, anba Kristi wannan aiki domin shi da kansa, Kalmar Allah ne cikin jiki. Shine gaskiyar Allahntaka da Shari’a a cikin jiki (Yahaya 13:34; surorin Maryam 19:21; al-Anbiya 21:91; al-Tahrir 66:21 d/s).

A cikin wadannan ayoyi na Kur’ani munji amsa kuwwa na Islama ga wahayi na Yesu, “kada kuyi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zone ba domin in shafe su ne ba, sai dai domin in cike su” (Matiyu 5:17 – 18) Ya kuma yi bayyani, “kun dai ji an fada wa matanen da… Amma ni na gaya muku! (Matiyu 5:21 – 48)”. Ba abinda ke shiga mutum ta baki ne ke kazanta shi ba, abinda ke fita ta baka yake kazanta mutum” (Matiyu 15:11 – 16 & 20).

Wata kila an gaya wa Muhammadu wadannan ka’idodi masu kawo sauyi wandanda Yesu ya koyar, amma bai fahince su a cikar Shari’a ba, amma ciccire wadansu kutatturai ne a Attaura don almajiransa. A hanya mai ban mamaki ya lakaba wa Isa dama ta soke dokoki da kafa sababbi a matsayin manzon Allah.

● Ba cin duk canje-canjen sharia’a da Dan Maryama yayi, ya tabbatar da zuciyar sujadan Musulunci. “Ji tsoron Allah”. Islama bata gudana tawurin kaunar Allah zuwa ga Mutane, ko kuwa kaunarsu zuwa gareshi. Allah ba uba bane kuma bashi da marmarin ya ceci duka mutane, amma Iko ne kadai da mulkin duka, a matsayin mai mulkin mallaka babu wanda ya isa ya tambaye shi ko ya nawaita masa wani abu. Musulmai kawai zasu iya durkusawa a gabansa su yi sujada cikin matukar bangirma.

● Yakamata a yi wa kowane manzon Allah irin wannan biyaya. Sau biyu a Kur’ani, Dan Maryama ya bidi Yahudawa, Krista da Musulmai: “ku yi mini biyaya” (surorin Al’Imran 3:51; al-Zukhruf 43:64). Wannan jumla na kabants da Islama! Kowa-da-kowa zai darajanta Kristi Yesu, su bada kansu gareshi kuma su kiyaye dokokinsa da kyau, kamar yadda suke tsoron Allah! Islama bata yin koyaswar, “ku gaskata alherin Allah, kokuwa ku karbi gafara ta Kristi ko ku kaunace shi domin shine ya kaunace ku da farko”, amma Isa kuwa ya bidi imani ta biyaya da mika wuya a kalkashin hukuncinsa Duk wanda ya fahimci wannan doka na Kur’ani zai samu a cikinta hanya mafi dadi na yi wa musulmai bishara. Dole ne musulmi ya fara koyon Dokar Kristi, kafin a koya masa alheri mai kawo ceto. Mu fara bincike dokoki 510 na Kristi a Bisharu hudu tare dashi mu gwada daidai da dokoki 613 na Musa a Linjila.Sa’annan mu yi rayuwa daidai da fadin dokar Kristi don zama misali kuma mu furta a gaban musulmi cewa ba ma iya cika duka dokokin ba shi ya sa mukan roki gafara kullayaumin. Bari musulmi ya sani cewa bashi yiwuwa mu cika duka dokokin Kristi tawurin karfin mu don ya umurce mu, “sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama ke cikakke” (Matiyu 5:48). Kuma “ku kaunaci juna. Kamar yadda na kaunace ku”. (Yahaya 13:34). Sa’annan kila ya gane cewa babu wanda zai iya cika dokar Kristi da iyawansa, amma yana bukatar gafara daga wurin Yesu da cetonsa kullum. Alherin Kristi Yesu ne kadai hanya zuwa wurin Uba (Yahaya 3:16; 14:4 d/s).

● Muhammadu yayi saurin tsaida wannan tunani mai hatsari sa’annan ya karasa da sa Kristi yace”, Allah Ubangiji na ne da Ubangijin ku. Ku yi masa sujada, shine bautar da ke daidai”. Bai bar Isa ya ce a Kur’ani: zan hau bisa zuwa wurin Ubana da Ubanku, wurin Allah na da Allan ku! A, a Muhammadu ya sa Isa a karkashin iko da hukunci Allah. Muhammadu bai yarda cewa Kristi Yesu Ubangiji ne da kansa zuwa daukakar Allah Ubansa ba. Bayan ya amince da wadansu ka’idodi na bangaskiyar Kristi, daga karshe ya ki amincewa da ginshikin ya kuma maida Dan Maryama bawan Allah, wanda zai jagoranci mabiyansa zuwa aljanna a “hanya faffada” ta Shari’a Musulunci.

Bacin wadannan dabaru na Islama, Muhammadu ya tabbatar da Kristi mai bada dokokin Allah wanda yana da daman ya bidi mika wuya daga wurin mabiyansa da duka mutane. Sai mu sa duka musulmai masu neman gaskiya su sansance da wannan furci na Kur’ani, kuma a taimake su ta hanyar kakkarya fahariya ta ruhaniya domin su karbi alherin Kristi wanda ke a wadace domin su.

5.13 -- Kristi Na Sabonta Mabiyansa

A cikin Kur’ani akawai ayoyi da dama wadanda ke nuna halayen Kristi a hanya mai kayu. Daga shaida ta Muhammadu mutum zai gane cewa Dan Maryama ya ‘iya canza masu girman kai su zama masu tawali’u da kuma masu son kansu su zama masu hidima cikin jinkai. Wannan shine mu’ujjiza mafi girma wanda Isa yayi a cewar Littafin Musulmai. Wannan canji bai faru sau daya kadai ba, amma yana faruwa kullum, tun da har yanzu an ambaci Kristi fiye da sau 50 a cikin Kur’ani. Wadansu daga cikin wadannan ayoyi ba a ambaci Kristi kadai ba har ma Yahudawa (surorin Al’Imran 3:55 – 113 & 114; al-Hadid 57:27; al-Tahrir 66:114 d/s).

A cikin sura al-Imran mun karanta ganinda Muhammadu ya yi wa tawagar Kristi daga Arewacin kasar Yemen (wadi Nadjran), wadanda suka tattauna dashi akan addini a Madina na tsawon kwana uku. Yayi kokarin jan ra’ayin wadannan Krista don su musulunta ya kuma bar Allah yace wa Isa”zan fifita ma biyanka bias marasa imani har zuwa ranar tashin matattu” (Sura Al ‘Imran 3:55).

Muhammadu da Musulmansa sun yi sha’awar tawagan mutane 60 daga Arewacin Yemen da yadda suka yi ado mai kyau. Muhammadu ya ga cewa al’adarsu ta fi tasa amma yana so ya jawosu cikin Islama. Ya lura da yadda sun riga sun ci gaba a rayuwa na tattalin arziki bisa matsafa da arna. Amma tabbas cikin shawarar sa bai bayyana musu gaskiyar ra’ayinsa ba na cewa Musulmai na gaba da Krista.

A wannan sura mun karanta game da bayi da ma ma’aikata wadanda sukan hadu da dare don su yi wa Ubangijinsu sujada suna rusunawa. Wadanna wata kila Krista ne na Otodoks domin babu wata Ikklesiya, har ma Yahudawa da suke rusunawa cikin sujadarsu. Muhammadu ya gane cewa wadannan Krista masu rike alkawari ne da Allah kuma rayuwarsu ta yi daidai da bangaskiyarsu. Ya kira su “Nagargaru” wadanda Allah zai basu lada (sura Al’Imran 3:113 – 114). Wannan babbar shaida ce game da Kristan da aka zalunta a Hidjaz!

A cewar sura Al’Imran Muhammadu ya sadu da Krista wadanda basu da girman kai kuma suna fadin ayoyi daga Baibul basa karban kudi, abinda ya bambanta su da Yahudawan Madina wadanda kafin su fada masa wani abu daga Talmud ko Mishna sai ya sayi kaya daga wurinsu (Al’Imran 3:119). Sau da yawa a fadin Kur’ani, Krista sun yi kokarin yi wa Muhammadu bishara amma a banza.

Cikin sura al-Ma’ida an bambanta Krista da Yahudawa. An zaci Allah ya saukar wa Muhammadu:

Lalle ne kana samun mafiya tsananin mutane a adawa ga wadanda suka yi imani, Yahuwa ne da wadanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kana samun mafiya kusantarsu a soyayya ga wadanda suka yi imani sune wadanda suka ce: Lalle mu ne Nasara:. Wannan kuwa saboda akwai kissisuna da ruhubanawa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, basu yin girman kai”. (sura al-Ma’ida 5:82).

Muhammadu ya sansance tawali’u na Kristi da mabiyansa wadanda basu girmama kansu ba. Muhammadu a wannan lokaci ya fahimci cewa wannan irin kyan rayuwa baya fito daga warinsu ba amma daga wurin shugabanninsu na ruhaniya wannan aya ya bada amincewa da tawali’u na Krista a zamanin Muhammadu.

A sura Hadith zaka iya karanta bayani mai zurfi akan Krista. Muhammadu ya bar Allah ya bayyana cewa.

Sa’annan muka biyar a bayansu da manzannin mu; kuma muka biyar da Isa Dan Maryama, kuma muka bashi Linjila kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan wadanda suka bishi da rubbananci”. (sura al-Hadid 57:27).

Muhammadu ya bambanta Krista iri-iri: Ya gane ma nema gaskiya a almajirai, masu dokin yaki da mataimaka wadanda suke shirye su je yaki don kare sabon koyaswa, masu imani kuma suna sujada da adu’a suna kokarin rayuwa bisa ga abinda suka gaskata, musulman kwarai wadanda suka bada kansu ga Allah da manzonsa (Kristi) kuma suna masa biyaya cikin kome, mabiya wadanda suna kokarin aikata abinda yayi suna binsa ko a cikin halin kakanikayi, sune shaidun wadanda suka ga abubuwan da yayi kuma shirye suke su mutu don shaidarsu. Sun roki Isa abu guda, cewa ya rubuta sunayensu a cikin Littafin rai a sama (sura al-Imran 3:52 – 53).

A cewan Muhammadu, ba duka Krista ne sun dandana dukan manyan mu’ujjizan da Yesu yayi ba sai dai “Manzannin sa”. Muhammadu ya ji a ransa cewa Allah yayi wata mu’ujjiza da wadannan tare da su. Ya sa wani abu a cikin zukatansu wanda yake da shi wato tausayi da jinkai, har ma ga magabtansu! Yayin da Muhammadu yayi tunani game da asalin wannan baiwa ya gane cewa daga Linjila ne, cewa tausayi da jinkai a cikin zukatan mabiya Kristi sun samu ne daga cikin wannan Littafi. Amma bai sansance da ikon Ruhu Mai Tsarki ba wanda Bulus ya rubuta, “Allah ya kwarara kauna tasa a zukatanmu, ta Ruhu Mai Tsarki da aka bamu”. (Romawa 5:5).

Muhammadu ya yarda da Krista na kwarai. Ba don ya san Waraqa b.Naufal, dan ‘uwan Khadijah matarsa ta farko wanda dattijo ne a gidan adu’a a Makkah ba, amma yana sane da dandanawar musulmai 83 wadanda suka sami mafaka a Abisiniya lokacin da aka tsananta wa musulmai a Makkah. Halin da Krista na Abisiniya suka nuna ya sa Krista suna da daraja a Kur’ani fiye da yadda muke tsammani. Ko ta yaya, Krista na Abisiniya sun gaza don basu yi ma wadannan ‘yan gudun hijira bishara ba, Sa’anda Musulmai suka koma Madina bayan Islama tayi karfi, mutanen Habasha 230 sun riga Musulunta, amma musulmi daya ne a cikinsu ya zama Krista. Wannan dayan ma ya mutu jim kadan baya tubansa (watakila an kashe shi ne).

A cikin sura al-Saff an kira “Mataimaka da kuma abokan aikin Allah” lokacin da suka dauki alkawalin yin aminci ga Isa cikin gwajin da ya sha kuma suna shirye don yin yaki domin sa. Allah ya tabbatar musu da nasara bisa abokan gabansu (sura al-Saff 61:14).

In ka karanta wadannan ayoyi a Kur’ani zaka ga cewa Muhammadu ya ga cewa Isa ya canza mabiyansa suka zama kamarsa. Suna kaunar abokan gabansu, suna albarkatar wadanda suka la’antasu suna yin nagargarin ayuka zuwa ga wadanda suke zaginsu da kuma tsananta musu. (Matiyu 5:44). Masu kaskanci ne da tawali’u ba masu hadama ba, amma suna adu’a wurin taruwansu, wani lokaci har da dare in da bukata. Littafinsu shine cibiya da asalin sujadarsu. Wadannan Krista ba baki bane, amma Larabawa ne daga arewa, kudu da yammacin kasan Larabawa. Kristi ya aikata mu’ujjizarsa mafi girma a cikinsu: suna rayuwa bisa ga abinda suka gaskanta kuma sun zama sabobin halitta tawurin alherin mai cetonsu. A yau Musulman da suka zama Krista zasu iya ganin kansu a wannan sabuwar hanya yadda aka fadi a Kur’ani. Wadannan ayoyi zasu taimakesu sa’anda suke zance da ‘yan ‘uwansu da suke cikin musulunci.

5.14 -- Ayatollah Na Gaskiya

Sau biyu an fadi a Kur’ani cewa Kristi Yesu da uwarsa manyan alamu ne da Allah yayi (surorin al-Anbiya’ 21:91; al-Sajda 32:50). Sau daya an bayyana cewa Isa “alama ne ga mutane da jinkai na Allah” (sura Maryam 19:21). Wadannan ayoyi guda uku sun tabbatar da asiri na Kristi a Kur’ani kuma sun takaita dalilin duka mu’ujjizansa. Manufan mu’ujjzansa shine su bayyana shi Isa wanda ya aikata su.

Kalmar da aka juya alama daga Larabci it ace “ayatun” wanda kuma na nufi “mu’ujjiza” in ka karanta wannan kalma tare da Allah zasu baka lakabi na girmamawa “Ayatollah”! Kristi Yesu shine alamar mu’ujjiza na Allah! Nassin na ma kuma ya nuna manufarta: ga mutane! Bari kowa ya ga iko da kaunar Allah a cikin Dan Maryama. Babu wani annabi, sarki ko Firist wanda yake da wannan lakabi na girmamawa a cewan Kur’ani, har ma Muhammadu. Kristi shine mu’ujjiza wanda ba makamancin sa wanda duka mutane zasu yarda da shi. Sauran Ayatolloli sun karbi lakabinsu daga wurin mutane ne.

In muka yi tambaya, me yasa Dan Maryama ya zama alama na Allah mafi girma a cikin Kur’ani, zamu sami amsa a cikin abinda aka gaskata a cikin Islama cewa Allah ya halicci Isa cikin Maryama tawurin kalmarsa, ba da taimakon namiji ba. Allah ya hura ruhunsa cikin jikinta. Saboda haka Kristi ba mutum bane kadai daga wurin mace, amma, a cewar Kur’ani shi kuma ruhu ne daga wurin Allah a jikin mutum. Yau, Yesu yana raye tare da Allah. Muhammadu matacce ne. Kristi Yesu shi ne kadai mutum wanda za a iya kiransa “ruhu daga wurin Allah” da kuma “Kalmar sa da ya zama jiki”. Saboda haka Kristi cikin azanci shine alama kuma Allah ga duka mutane.

Daga wannan halitta biyu-mutum na kwarai da ruhu na kwarai daga wurin Allah-aka aikata duka alamu da mu’ujjizansa a fadin Kur’ani:

 • Shine Kalmar Allah cikin jiki. Ya iya yin Magana tun yana jariri.
 • Shi mahalicci ne, yana da lumfashi mai bada rai-da izinin Allah.
 • yana cike da jinkai don marasa lafiya da masu bakin cikin. Ya warkar da duk wadanda suka zo wurinsa.
 • Shine Likitan likitoci na duka duniya-da izinin Allah!
 • Shine mai nasara bisa mutuwa, don ya tada matattu-da izinin Allah!
 • Shine mai ganin abu duka-da idanunsa zai iya ganin kowa da kome!
 • Yana da daman yin godo a matsayin matsakanci tsakanin Allah da mabiyansa.
 • Ya sauko da abinci daga aljanna domin mabiyansa kuma yana basu abincinsu na kullum!
 • Shi mai bada dokoki ne kuma ya tabbatar da rashin kuskuren Attaura. Ya canza dokakin Allah ya kafa sababbi.
 • Hakkinsa ne ya bida a gaskanta shi kuma duka mutane su yi masa biyaya har da musulmai.
 • Ya canza halin sonkai daga wurin mabiyansa ya cika su da kauna da kaskantadda kai.

Wadannan alamu a cikin Kur’ani Kaman madubi ne da ke haskaka ayuka da halayen Isa, Dan Maryama. Suna nuna cewa shine mu’ujjizan mu’ujjizai.

Za’a iya rarrabe Kristi ba baibul a cikin ayoyin Kur’ani. Muhammadu ya hada abubuwa da yawa daga bangaskiyar Krista a cikin Kur’ani ko za a ga Kaman yana daidai da bishara saboda a yaudari Krista su zama musulmai. Ba kowane lokaci bane yake nuna kiyayyarsa akan Allahntakan Kristi kokuwa zubar da zancen giciyen Yesu. Ya yarda Isa mai aikata mu’ujjizai ne cikin jinkai, mai warkar da cuta, mai tada matattu da mai bada doka. Ya nuna wannan yarda saboda ya jawo ra’ayin Krista zuwa Musulunci.

Daga yanzu muna da dama mu dauki murgudaddiyar shaida akan Krista daga Kur’ani mu kuma sa shi yadda yake a Linjila. Manufa ba don a nuna shari’a da alheri, dokoki da biyaya cikin bangaskiya ba, amma a nuna wa Musulmai Kristi na ainihi, saboda su ganshi, su kaunace shi, su gaskata shi, su rike shi, su karbi rai madawwami wanda yake bayarwa kuma su yi rayuwar albarkar Ruhunsa.

Saboda wannan, Yesu ya kira kansa hasken duniya, gurasar rai, hanya madaidaiciya, dawwamammiyar gaskiya, makiyayi mai kayu, kuringar anab na ainihi, tashin matattu da rai, sarki (da rawanin kaya), farko da kuma karshe. Kalmomin “Nine…” na Yesu a cikin Bishara zasu iya fahimtar da musulmi mai neman gaskiya ya gane cewa Yesu ba mai aikata mu’ujjizai ne kadai ba amma ainihi kaumar Allah da tsarkinsa ne cikin jiki.

5.15 -- Tambayoyi

In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan

Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.

Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.

 1. Mu’ujjizai nawa ne na Musa an rubuta a Kur’ani? Yaya suke da manufofinsu?
 2. Sau nawa ne zamu iya karanta game da shaida (bayyinaat) na Kristi a cikin Kur’ani? Menene halayensu da manufofinsu?
 3. Wanene Ruhu na Mai Tsarki wanda a fadin Kur’ani ya karfafa Kristi don aikata mu’ujjizansa? (surorin al-Baqara 2:87 – 253; al-Ma’ida 5:11 d/s).
 4. Tayaya Muhammadu yayi kokarin samun majinginan annabcinsa da shaida ta Kristi? (sura al-Saff 61:6).
 5. Sau nawa ne Muhammadu yayi amfani da kalma “alama” (aayat) dangane da mu’ujjizan Kristi a cikin Kur’ani? A ina ne a cikin Linjila zamu iya samu an fadi irin wannan kalma dangane da Mu’ujjizan Kristi? Ta yaya ma’anar wannan kalma ya sha bamban a cikin Litattafan biyu?
 6. Me yasa Yesu ya dauki nema na ganin mu’ujjizai a matsayin rashin bangaskiya ko kuwa kokarin gwada Allah a cewar Linjila?
 7. A ina ne Muhammadu ya ji wannan tatsuniya cewa “jariri Isa yayi Magana daga haihuwarsa? Me yasa Muhammadu ya yarda kuma ya gaskakata irin wannan labari?
 8. Ta yaya hada irin wannan labarin iska game da Isa a cikin wahayin Allah a Kur’ani ya tabbatar mana cewa Muhammadu ba annabin gaskiya bane?
 9. Menene jawabin Kristi na farko wanda ke cike da alamar rashin gaskiya a cikin Kur’ani ya kunsa?
 10. Tayaya Muhammadu yayi tunanin halittar tsuntu da Isa yayi sa’anda yake yaro?
 11. Me yasa wannan sashen Magana “Na halitta” a cikin bayanin Kur’ani na mu’ujjizan da Dan Maryama yayi yana da Muhimmanci a zancen mu da muslmai?
 12. Menene zamu iya ganowa daga cewa “Isa ya hura wa tsuntsun da ya halitta daga yumbu lumfashi” da kuma fadin Kur’ani cewa tsuntsun ya tashi? A ina ne a cikin Linjila zamu iya karanta cewa Yesu ya hura wa mutane lumfashi? Wane bambanci aka samu tsakanin Lamfashin Kristi a Kur’ani da Linjila?
 13. Ta yaya Muhammadu a Kur’ani yayi kokarin rage mukamin Yesu na aikata mu’ujjizans? Me yasa Yesu da kansa ya rage mukamin aikata mu’ujjizansa a cikin Yahaya 5:19?
 14. Makafi nawa ne Kristi ya iya bude idanunsu a fadin Kur’ni? A aikace, ta yaya ne ya bude idanunsu a tunanin Muhammadu?
 15. Ta yaya ake daukan ciwon kuturta a kasashe da dama a Asiya da Afirka?
 16. Har da menene ikon Kristi na warkar da kutare ya hada?
 17. Menene kulawa da Dan Maryama ke nuna wa mara lafiya da masu bakin ciki a Kur’ani ke bayyanawa?
 18. Matattu nawa ne a fadin Kur’ani Yesu ya rayaddasu?
 19. Me yasa Yesu ne kadai cikin ‘yan adam da ya iya tada matattu a cewar Kur’ani?
 20. Wane asiri ne zamu iya bayyana wa musulmai a bisa koyarwar Musulunci cewa Isa bai iya aikata mu’ujjizansa ba sai da taimakon Ruhu daga wurin Allah?
 21. Ta yaya Isa a Kur’ani ya bayyana a matsayin mai sanin abu duka? Ta yaya zamu yi amfani da asirin masanin abu duka cikin zancen mu da musulmai?
 22. Yaya ne al-Suyuti yayi sharhi akan Kur’ani sa’anda yayi amfani da hadisi game da Yesu don ya bayyana Isa Masanin abu duka ne?
 23. Menene ya zama a gareka abu mafi muhimmanci a labarin “Tebur daga sama” na Kur’ani wanda aka saukar wa mabiyan Isa?
 24. Me yasa Yesu yayi adu’a ya kira “Allahumma” ba “ya Allah” ba?
 25. Ta yaya Muhammadu ya tabbatar cewa Kristi yana da dama ya zama matsakanci tsakanin mabiyansa da Allah? Me yasa madaukaki ya amsa adu’ar Dan Maryama nan-da-nan?
 26. Me yasa Kristi ya iya canza Shari’ar Musa? Ta yaya zai iya barin mabiyansa su yi abubuwan da Allah ya haramta? A fadin Kur’ani, Kristi na da ikon zatarwa ne kadai ko har da na bada dokoki?
 27. Me yasa Isa yayi ta Magana akan “tsoron Allah” akai akai a Kur’ani kuma da kyar akan kaunar Allah?
 28. Menene umurnin Kristi a Kur’ani “ku yi min biyaya” zai zama ga duka musulmai? Me yasa zamu yi bincike akan dokar Kristi saboda yin zance da musulmai?
 29. Ta yaya Muhammadu yayi wasa da kalmomi don kokarin wofinta ikon Kristi da mai da shi musulmi mai tsoron Allah?
 30. Wadanne lakabi ne da sunaye Muhammadu ya kirkiro saboda ya bayyana matakai na girman mabiya Kristi? Me yasa ya kira su “Musulmai”?
 31. Wadanne halaye ne na Musamman Muhammadu yayi amfani dasu don bambanta mabiya Kristi? Daga ina ne ya sami wadannan halaye?
 32. Me yasa canji daga son kai na masu zunubi zuwa barorin Ubangiji masu salama ya zama “mu’ujjizan Kristi mafi girma”?
 33. Me yasa Isa ne a Kur’ani “Ayatollah na miji kadai” wanda Allah ya nada a duka tarihi? Menene ma’anar wannan lakabi kuma wane lakabi ne na Kristi za a iya samu daidai da wannan a Linjila?
 34. Ta yaya Muhammadu ya bayyana da kuma zurfafa lakabin Ayatollah na Kristi? Menene wannan zai iya nufi a Islama,cewa Kristi shine jinkan Allah a cikin jiki?
 35. Wadanne lakabobi ne da halaye guda goma na Kristi zaka iya samu daga mu’ujjizan Kristi a Kur’ani?
 36. Me yasa Muhammadu ya yaba Kristi a gaban wakilai na Krista da suka ziyarce shi?
 37. Ta yaya zamu iya amfani da mu’ujjizai na Isa a cikin Kur’ani su zama gada da zai sada mu da musulmai don bishara? Menene ya zama maka dole in zaka cimma burin ka a aikin ka tsakanin Musulmai?

Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.

Naku cikin Hidimarsa

Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.

Ku aika da amsoshin ku zuwa:

The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.

Ko

GRACE AND TRUTH
P.O. BOX 1806
70708 Fellbach
GERMANY

Kokuwa ta wayar e-mail zuwa: info@ grace-and-truth.net

www.Grace-and-Truth.net

Page last modified on June 03, 2013, at 08:39 AM | powered by PmWiki (pmwiki-2.3.3)