Home -- Hausa -- 01. Conversation -- 1 Great Commission
01. ZANCE DA MUSULUMI GAME DA KRISTI
1 - Babbar Umarnin Yesu Ubangijinmu
1.01 -- BABBAR UMURNIN YESU UBANGIJIN MU
“Lokocin da suka ganshi, suka yi masa sujada, amma wadansu sun yi shakka. Yesu ya zo garesu yayi magana da su, cewa, ‘Dukan iko an mallakar mani a sama da duniya. Kutafi fa ku almajirtar da duka al’ummai, kuna yi musu baftisma cikin sunan Uba, da na Da, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su bi duka abubuwan da na umurceku; gama, ina tare da ku ko yaushe, har zuwa iyakacin zamani Amin”.
(Matiyu 28:17-20).
1.02 -- Kiran Yesu
Bayan wanda aka giciye kuma ya tashi daga matattu ya gama sulhunta duniya da Allah, Ya so ya wadatarda cetonsa ga kowa a ko’ina a cikin duniya ta hanunun almajiransa. Bayan yayi kafara don zunuban duka ‘yan adam, mai nasara bisa mutuwa da hades ya kira mabiyansa da masu yi masa sujada wadanda har zuwa wannan lokaci suna da shakka, ya basu izini da suje suyi shelar cetonsa ga duka al’ummai. Duka almajiransa kuwa sun warwatsu a lokacin gwaji. Babu ko dayansu da ya cancanta ya zama ma’aikacin Kristi. Kiran da Yesu yayi musu ne ya sa suka cancanta su zama manzannin alherin sa.
1.03 -- Duka Iko Sama Da Kasa
Kristi ya bayyana wa mabiyansa cewa. Ubansa wanda ke cikin sama ya bashi duka iko bisa malai’ku da mutane, bisa manyan haskoki da kananan halittu har masu kankanta kamar kwayar zarra.
Yaya madaukaki ya yi kasadar mallakarwa dansa dukan ikonsa? Bai ji tsoran ko zai yi tawaye ba? Uban ya san dansa kwarai shi mai tawali’u da kaskantar da kai daga zuciyarsa ne, bai mai da kansa kome ba. Ya bada kansa sadaka don masu zunubi. Yakan girmama Uba kamar yadda Ruhu Mai Tsarki yakan daukaka Dan, Allahnmu mai tawali’u ne, don wannan dalili ya iya mallakarwa dansa duka iko na sama da duniya. Wani ruhu wanda ya sha bambam da na Allah yana iko bisa Musulmai. An rubuta a Kur’ani cewa baza a iya samun alloli biyu ba domin ba shakka daya zaifi daya girma (Sura al-mu’minun 23:19). A cikin daular Usmaniyya, bayan mutuwar sultan, akan kashe dukan ’ya ’yansa maza a bar wanda ya fi karfi da hikima don ya gaji gadon sarautar. Akan yi haka don a hana yin fada akan wanda zai gaji sarautar. Ruhun tawaye na da rinjaye a addinin musulunci. Daya daga kyawawan sunaye 99 na Allah shine” mai alfahari, mai alfarma” (Sura al-Hashr 59:23).
Akwai sabani tsakanin Yesu da abinda muka karanta a baya. Bai yi amfani da ikonsa don gina mulkin duniya da kudin haraji ko karfin soja ba. Maimakon haka ya warkar da dukan marasa lafiya da suka zo wurinsa, ya fitarda iskoki ya tada matattu, ya gafarta zunubai ya kuma zuba wa mabiyansa Ruhu Mai Tsarki. Ya fara gina mulki na ruhaniya. Ya dukufa wajen gina almajiransa. Sunansa “Yesu” ya kasance manufansa: “zai ceci mutanensa daga zunubansu” (Matiyu 1:21).
1.04 -- Saboda Haka Kutafi
Lokacin da Yesu ya karbi dukan iko daga wurin madaukaki, Ya Umarci almajiransa da su tashi su fara aiki. Suna dogara ga karfin ikonsa mara iyaka yana so su daina boyewa, su fita su kai bishara cikin hanzari. Yana so mu sami yanci daga “Ni” wato mu daina duban kanmu amma mu dubeshi “Yesu”. Ya aikemu zuwa ga ‘yan’uwan mu da abokan harka. Yana bukatar mu da mu kai bishara har zuwa ga mutanen da suke ketare, tunda makiyayi mai kyau yakan bar 99 masu adalci ya je neman batacciyar tunkiyannan har sai ya samo ta. (Luka 15:14-7).
1.05 -- Jagora Na Ruhu Mai Tsarki
Wanda yake so ya bi umarnin Yesu yana bukatar Jagora na Ruhu Mai Tsarki, Wata kila zaka ce, “Wajen wa zan je? Bani da wanda zan je wurinsa! Ubangiji na baka amsa cewa”, “ku roka, za a baku” (Matiya 7:7-12; Luka 11;9-13; Markus 11:24) Muna da dama na rokon sa ya nuna mana musulmai wadanda suke neman sani wadanda Ruhu Mai Tsarki ya shirya zukatansu da tunaninsu.
Duk wanda ya sami irin wannan mai neman sani kada ya dage sai yayi magana ba tare da yin bincike akan tunaninsa, ko abinda yake ji ko wahalar da ya sha. In ma mun kai ga haka, ka da mu bashi amsar damuwarsa kai tsaye, amma daga cikin zuciyarmu mu roki Yesu ya gaya mana abin da yake so ya gaya wa mutumin. Zamu iya rokon Yesu ya bamu abinda zamu fada. Yesu da kansa zai sa maganarsa ta shiga ta yi aiki cikin mai neman gaskiyan nan.
Ka auna kanka. Kana jin marmarin yin magana da makwabcin ka, abokin aiki, matar ka ’ya’yanka ko kuwa wani mutum game da Yesu? Ka nemi sanin nufin Yesu da umurninsa game da kai. Kada kayi dari-dari da yin biyaya. In kana jin tsoro, ka roki Yesu ya zuba maka kauna da karfinsa don kayi nasara kan tsoron da ke cikinka. Mutane dayawa suna jiran shaidar ka fiye da yadda kake tsammani! Amma addu’oin ka da farko na da muhimmanci fiye da shaidarka.
1.06 -- Menene Muke Da Shi Da Zamu Iya Bayarwa
Duk wanda yake son abokansa su saurare shi, ya kamata ya basu abinda suke nema. Malami na kwarai yana da sani fiye da almajiransa kuma zai iya yin abinda bazasu iya yi ba, amma suna da marmarin su sani kuma su yi abubuwan da yake yi. Ba sa sa rai ga jin manya – manyan kalmomi, amma suna so suga ko malaminsu yana da iko na ruhaniya, kuma, ko yana aikata abubuwan da yake koyarwa. Sa’annan zasu taru su jishi.
Krista suna da abinda zasu rarraba da wadanda ba Krista ba, Krista sun sani cewa Allah Ubansu ne, Yesu mai cetonsu, Ruhu Mai Tsarki mai taimakonsu ne. Tawurin alheri ya barataddamu. Ya bamu Ruhunsa kyauta. Tawurinsa muna da salama da farinciki mara matuka. Ya zuba kaunan sa (Romawa 5:5) ya kuma bamu ma’anar rayuwar mu. Ya bayyana gaskiyar ga mabiyansa (Yahaya 14:6) ya kuma ba su bege na rayuwa nan gaba. Ya taba mu da ikonsa mara matuka. Mu manta da kasawarmu, cikin adu’a mu ci gaba da yin shaida akan abinda Ubangijin mu yayi mana. Dole ne mu ba duniya abin da suke nema. Ma biyan Kristi sun karbi rai na har abada daga dan rago na Allah. Ka gaya wa makwabtan ka.
1.07 -- Duka Mutane
Biyaya da umurnin Yesu ya sa ana ta bishara a duk duniya tun kimanin shakaru 2000 da suka wuce. Manzannin sa sun fara da yin bishara a garuruwan da ke kewaye da tekun mediteraniya da Farisa. Sa’anna wa’azin ceto ya matsa zuwa Turai da Asiya ta tsakiya, har zuwa kasar Sin. Lokacin da aka gano Amirka da kuma hanyar ruwa zuwa Indiya. Ubangijinmu rayayye ya bude duk kasashe na duniya domin masu bishara. Yau, ‘ya ‘yan Ibrahim, Yahudawa da Musulmai, suna fuskantar kalubalen ko su karbi Yesu ko su kishi. Har da kasashe ‘yan gurguzanci, kamar kasar Rasha da Sin an shige su da bishara. Muna so ku sani cewa daya bisa uku na mutanen duniya ne ke kiran kansu Krista. Dokancin mutanen duniya basu san mai cetonsu ba. Akwai sauran aiki. Ba zamu zauna muna hutu ba. Kowane almajiri na Yesu an kira shi don ya bada tasa gudumawa cikin kokarin kai bishara ga duniya duka.
1.08 -- Yada Addinin Musulunci
Addinin Krista ba shine addinin da ke yaduwa kadai a duniya ba Kur’ani ya bada umarni kashi biyu cewa”
“kuma ku yake su har wata fitina ba zata kasance ba kuma addini duk kansa ya kasance na Allah…” ”(Sura al Anfal 8:39; al-Baqara 2:193)
Sama da ayoyi dari a cikin Kur’ani na iza musulmai su hada kansu suyi jihadi. Zaka iya karanta “Lalle ne, Allah ya sanya daga mummunai rayukansu da dukiyoyin su, da cewa suna da aljanna, suna yin yaki a cikin hanyar Allah, saboda haka suna kashewa ana kashe su” (Sura al-Tawba 9:111).
Abin takaici, Krista ma sun fara jihadi da mulkin mallaka, irin wadannan mugayen ayuka sun saba wa dokar Yesu Kristi wanda ya ce wa Bitrus, “ka mai da takobinka a wurinsa wanda ya dauki takobi, ita zata kashe shi” (Matiyu 24: 52).
Yaduwar addinin musulunci mafi girma ya auku a karo biyu: na farko ya kai tsawon shekaru dari. A wannan ne aka ci nasara a kan kasashen gabas, arewacin Afirka, Spain da wadansu bangarori na Asiya ta tsakiya.
Karo na biyu ya zo ne lokacin da aka mamaye mangolawa, Yawancin zuriyar Genghis Khan suka musulunta don nasarar da aka yi a kansu. Sun ci nasara akan Asiya ta tsakiya sun yi mulki har zuwa kasar Sin, Arewacin Indiya, Mesafotamiya da Rasha. Turkawan daular Usmaniyya da yan’uwansu sun yi nasara da Konstantinoful a shekara to 1453 sun kuma kewaye Vienna sau biyu amma a banza. Matsalolin da ke addabar kasashen gabar wadanda ba’a iya warwarewa ba na da tushe daga rusashshiyar mulkin daular Usmaniyya da tayi mulki na wajen shekara dari hudu.
Karo na uku na yaduwar musulunci ya fara a shekar ta 1973 da karuwar kudin mai kuma musulmai suna shiga kasashe da yawa. A yau, fiye da kowane karni za’a samun musulmai da yawa mazauna kasashen da an san su kasashen Krista ne. Har yaushe Krista zasu cigaba da barci suna mafarkin samun kasar da ta tara mutane masu al’adu dabam-dabam.
Yawancin musulmai sun nace da cewa musulunci addini ne mai hakuri da salama, Ayoyi da dama a Kur’ani na karfafa nuna wa juna bangirma da ayuka nagari (sura al-Baqara 2:256; al-Ankabut 29:46 d.s). Da gaske ne za a iya samun wadannan ayoyi a Kur’ani, amma sun sami asali ne lokacin da Muhammadu da mabiyansa basu da yawa. Wannan kira ta yin hakuri tuntuni an soke an kuma canza su da wadansu ayoyi daga Allah wadanda suke kiran Musulmai su dauki makamai su yaki abokan gabansu har sai sun ci nasara da su (Sura al_baqara 2:191; al-tawba 9:29 d.s.) A fuskar shariar Musulunci, ayoyi na ainihi wadanda suke kiran musulmai su yi hakuri ba’a aiki dasu. Duk da haka, wadannan ayoyin da aka soke ana amfani da su don neman goyon bayan musulunci a wuraren da musulmai basu da rinjaye. Sau da yawa Muhammadu yace “Yaki yaudara ne”. an gina aikin yada musulunci a kan yaudara ba akan gaskiya ba. Allah da kansa shine mafi yaudara (Sura al-lmrau 3:54; al-Anfal 8:30)!
1.09 -- Umarnin Yin Baftisma Zuwa Cikin Triniti
Yesu bai koyar da wani ra’ayi wanda fanko ne game da Allah ba. Bai bayyana wani Allah wanda yake nesa, mai girma, wanda ba a ganin shi ba. Dan Allah ya bayyana mana sunan Ubansa sau 187 a cikin litattafan Bishara guda hudu kuma ya bamu Ruhansa Mai Tsarki wanda Allah ne na gaskiya. Yesu kuma yayi shaida cewa “Ni da Uban daya ne (ba biyu ba)! (Yahaya 10:30; 17:21-22). Ya umarci almajaransa da su yi wa duk wadanda suka bada gaskiya gareshi bishara da baftisma, ba cikin sunayen alloli uku ba, amma a cikin sunan Allah daya wanda shine Uba, Da, da Ruhu Mai Tsarki. Ukun nan cikakken dayantaka ne, kamar yadda Yesu ya ce, “Uban yana cikina Ni kuma a cikin Uban” (Yahaya 14:10-11).
Bisa ga fadin masu sharhi akan Kur’ani dabam-dabam, cewa Muhammadu yayi magana akan baftismar Krista har ya kirashi” rini irin tasu” (al-sibghat). Ya gane cewa Krista daban suke da sauran mutane a kasar Larabawa. Basa sata, basu da girman kai, kowannensu na da mata daya, masu tawali'u ne kuma suna kaunar magabtansu. (Sura al-Imran 3;199; al-ma’ida 5:66, 82; al-An’am 6:90; Yunis 10:94; al-Nahl 16:34; al-Hadid 57:27; al-saff 61:14 d.s). Ya nuna yarda cewa wadannan halaye masu kyau, Krista sun iya nuna wa saboda sabontuwa ta ruhaniya da suke samu tawurin yin baftisma, tasirin bishara da kuma kakkarfan alkawari da Allah (Sura al-Ma’ida 5:110; Maryam 19:88; al-Ahzab 33:7).
Duk da haka, Muhammadu ya shiga kai hari gadangadan a koyarwarsa da rubuce-rubucensa gaba da Allahntakan Yesu Kristi da na Ruhu Mai Tsarki; shaidar bangaskiyarsa wanda ke a hagunce na cewa “Babu allah sai Allah!” Umarnin Yesu wanda ya bayar ayi baftisma cikin sunan Uba, Da, da Ruhu Mai Tsarki yakan zama kaman sabo a kunnen Musulmai. Tunda a musulunci babu Ruhu Mai Tsarki kamar a bishara, haka kuma musulmai baza su iya sanin Uba, Da, da Ruhu Mai Tsarki a (I Korintiyawa 12:3; Romawa 8:15-16).
1.10 -- Baftisma Na Bada Kariya Da Kuma Majingina Ne
Bulus ya rubuta, “Alherin ubangijin mu Yesu Kristi da kaunar Allah da zumuntar Ruhu Mai Tsarki, su kasance tare da ku” “(II korintiyawa 13:14). Baftisma na bamu daman saduwa da Allah da kuma kakkarfan abin jingina cikin Triniti Mai Tsarki. An shigar damu cikin Uba, Da, da Ruhu Mai tsarki tawurin baftisma. Allah da kansa ne garkuwanmu. Wanda yake cikin kauna, yana cikin Allah, Allah kuma yana cikin sa, sai mu yafa dukan makaman yaki na Allah don mu zama masu karfi “cikin” Ubangiji, sa'annan mugun ba zai iya cin zarafin mu ba. (1 Yahaya 4:15; Afisawa 6:10-17d.s.).
Masu yin asiri a addinin musulunci basu koshi da ra’ayin sanin Allah wanda ba’a iya ganewa ko bayyanawa ba a cikin addininsu, sun kuma ki kaddara kashi biyun nan a musulunci (aljanna ko gidan wuta). Sukan yi kokarin su taba Allah wanda ke nesa, madaukaki, wanda ba a iya taba shi ta wurin zulumi. Sukan yi kokari su same shi kokuwa su juya shi ya shiga cikin jiki. Yawancin lokaci sukan fadi kasa a kalkashin ikon iskoki tawurin sihirinsu. Allah a Musulunci yana nesa, ba a gane shi, saboda haka kowane kungiyar asiri zata iya shiga musulunci ba matsala. Babu ceto a addinin musulunci, akwai kira ne kadai zuwa mika wuya (shahada) a kalkashin mallakar Allah wanda yana da daman yaudarar wanda ya ga dama, kuma ya jagoranci wanda ya so ya jagoranta (Sura – al-An’am 6:39; al-ra’d 13:27; Ibrahim 14:4; al-Nahl 10:93; al-Fitr 35:8; al-Muddathir 74:31). Allah baya shiga alkawali da musulmansa. Yana daukansu bayinsa ne. shi ba uba bane, ko maiceto, ko mai taimako. Ya kan fatattake duk wanda bai yi biyaya da nufinsa ba (Sua al-Zuma 39:4; al-Hujurat 49:14 d.s.). Wanda ya mika wuya, akan yi masa kaciya don nuna alama ta dangantaka ta bawa da Allahnsa. Yin kaciya ga Musulmai shine maimakon yin baftisma a addinin Krista.
1.11 -- Baftisma Na Sada Mu Da Ikon Allah
Yahaya mai yin Baftisma yayiwa manzannin Yesu baftisma a kogin Urdun. Sun shaida zunubansu afili da kuma rashin cancantarsu da su tsaya a gaban Allah Amma Yesu ya tabbatar musu da cewa za’a yi musu baftisma da ikon Ruhu Mai Tsarki, cewa baza su cigaba da kasancewa da kumamanci, tsoro da rashin iya aiki ba, zasu sami jagora daga Allah (Ayukan manzanni 1:4-8; Yahaya 1:33-34).
A harshen Ibrananci kalmar da aka juya Allah shine “El” wanda yana nuna iko da karfi. Elohim jam’i ne na El, wanda za’a iya juya shi ya zama “Alloli masu karfi.” Kalma “Allah” a musulunci mufuradi ne wanda ya ke nufi. Shine ikon! Wannan sunan Allah a Larabci ba zai taba bada ma’anar Allah irin na Triniti ba. Zai iya bamu mufuradi ne kawai.
Yesu ya shaida cewa duka iko a sama da kasa an bashi. Ya kuma bayana cewa Ruhu Mai Tsarki ikon Allah ne. Allahn mu ikon nan ne ninki uku. Duk wanda aka yi masa baftisma cikin sunansa ya karbi dama da zai kasance hade da ikon Allah. Kuma zai ketara daga mutuwa cikin zunubi zuwa rayuwa cikin Ruhu wanda zai taimakeka kai ma ka tada wadansu daga mutuwa cikin zunubi. Bulus yayi shaidar wannan asiri. “Bani jin kunyar bisharar Kristi domin ikon Allah ne wanda yake kawo ceto ga wadanda suka bada gaskiya gareshi” (Romawa 1:16).
Bitrus ya gargadi Yahudawa da suke mamaki cewa, Ku tuba ayi ma ko wannenku bafitsma cikin sunan Yesu Kristi don gafarar zunubanku tawurin wannan zaku sami Ruhu Mai Tsarki (Ayukan Manzanni 2:38).
Duk wanda ya karbi ikon Allah tawurin batisma da bangaskiya, ba ya yin aikin Allah da karfinsa ba amma cikin karfin ikon Ubangiji, kuma zai karbi Karin iko muddan ya roka. (Ishaya 40:29-31).
1.12 -- Biyaya Da Dokar Kristi
A kasashen Larabawa in ka ce kana “ajiye maganar Allah” wannan na nufin kana haddace maganar ke nan. Yawancin Musulmai sun riga sun haddace Kur’ani duka. A lokaci – lokaci Musulmai sukan tambaye mu abinda ya sa ba ma kaunar Allah domin ba ma kare maganar sa! Haddace maganar Allah ga musulmi shike nuna mutum yana kaunar sa. Krista nawa ne sun haddace daya daga bisharu hudu na Almasihu ko wa'azi akan dutse (Matiyu 5-7)? Da kyar wadansu kan kammala haddace Zabura 23 ko 103, ko kuwa albarku na Matiyu 5:3-12 ko I Korintayawa 13.
Krista na da zurfin tunani amma abinda ya sani kadan ne. Musulmi ya san abubuwa da dama amma tunaninsa kadan ne. A al'adarmu ta hikima, kula da yawan tunani wanda dole mu tuba mu juyo daga irin wannan hali, mu saurari maganar Allah mu kuma kiyaye (Luka 11:28). Duk wanda ya cika tunaninsa da ayoyin Littafi Mai Tsarki zai sami karfi na ruhu.
Ajiyar maganar Allah kadai bai isa ba. Yesu ya bayyana mana a fili “in kuna kauna ta, ku kiyaye umarnai na” (Yahaya 14:15). Wandanne ne `umarnai na Kristi? An koya mana muyi tunani akan alheri, barata, gafaran zunubai, albarku da kuma Yesu da kansa. Mutane kalila ne sukan yi bincike akan shari’unsa. Duk wanda ya karanta bisharu guda hudu, zai iya gane cewa akwai umarnai na Kristi wajen 500 wadanda ya bayar. Wadansun su sanannu ne ga Krista. “ka kaunaci makiyanka, ka albarkaci wadanda suka la’ance ka, wadanda suka tsananta maka kuma sukayi maka rauni, kayi musu aikin nagarta (Matiyu 5:44-47). “Ka gafarta yadda Allah ya gafarta maka” (Matiyu 6:12, 14-15)’. Kada ka shar’anta, saboda kai ma kada a shar’anta ka (Matiyu 7-1-5).
Chanza ra’ayi kabi Yesu na da muhimmanci ga mutum. Amma fa, canza rayuwarmu ya zama dole in muna so mubi Yesu. In babu tsarki, babu wanda zai ga ubangiji (Matiyu 5:8; I Tassalonikawa 4:3; I yahaya 3:1-3).
Wanene zai koya wa wani ya bi dokokin Yesu sa’annan shi bai fara binsu ba? Kiran da Yesu yayi na malamai, masu waazi da ‘yan aike shine a fara tuba. Yesu yana bukata muyi masa biyaya. In ba haka ba muna soke abubuwan da muke fadi da ayukan mu!
1.13 -- Ku Aikata Dukan Abubuwan Da Na Umarce Ku
Yesu ya ce, “ku koya musu da su aikata duk abubawan da na umarce ku”. Wannan yar kalmar “duka” zata iya sa mu tsargu. Wannene a cikin mu ya haddace dukan abubuwan da Yesu ya umarce mu da mu aikata? Wanene ke rike da dukan umarnai na Yesu a kowane lokaci? Wane ke koya ma ‘ya‘yansa, matasa da ikklesiya? Wanene ke cika dokokin Kristi a magana, aikatawa da tunani daidai? Babu wanda yake cikakke a wadannan. Dukan mu mun kasa a bin wannan doka ta Yesu. Ko mafi tsarki a tsakanin mu sai dai ya sunkuyar da kai ya ce “Ubangiji, kada ka shar’antani”. Dadin dadawa, in munyi tunani akan takaitawar dokan Yesu zamu ji mun kankance. Yesu yace: “Ku zama cikakku, kuwa, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne”. (Matiyu 5:48).” Babu wanda ya ke aika nagarta, babu ko daya!” (zabura 14:2-4; Romawa 3:19-28; 7;3-8: 4 d.s).
Mu mabiya Yesu mu yi rayuwarmu kullayomin cikin alherinsa mai kawo barata kuma da bukatar tsarkakewa tawurin jininsa. Duk wanda ya karanta I Yahaya 1:7; 2:6 cikin adu’a zai samu bayani da taimako daga wadannan umarnai na ubangiji.
1.14 -- Menene Manufar Dokan Kristi?
Yesu yana so ya daga mu sama har mu zauna mazauni daya da Ubansa. Manufansa shine ya tabbatar cewa alkawalan mahalicci na farko sun cika a rayuwar mu: “Allah ya halicci mutum cikin kamaninsa, a cikin kamaninsa Allah ya halicce shi; namiji da tamata ya halicce su” (Farawa 1:27). Yesu ne kadai ya iya cewa, “Duk wanda ya ganni ya ga uban”. (Yahaya 14:9). Yana so ya canza almajiransa zuwa kamaninsa.
A kalkashin Tsohon Alkawali, Allah ya umurta, “ku zama da tsarki domin ni mai tsarki ne” (Firistoci 11:44; 19:2). Yesu ne ma’auni na rayuwa wanda ya zama makasudin rayuwar ruhaniya na kowane mai binsa.
A kalkashin Sabon Alkawali Yesu ya umurta, “Ku kaunaci junanku kamar yadda na kaunce ku! (Yahaya 13;34). Ya mayar da kaunarsa ma'auni garemu. Yesu da kansa shine dokarmu. Bulus ya rubuta cewa mu yafa Yesu, wanda shine sabon halitta. Bari mu lullube kanmu da shi. Muna da dama na zama cikin Kristi, kimanin sau 175 ne zaka iya samun wannan magana a Sabon Alkawali. Bulus ya gane wannan asirin: idan kowanen mu yana cikin Kristi, sabon halitta ne. Tsofaffin al’amura sun shude, gasu kuwa sun zama sabobi (II Korintiyawa 5:17-21).
1.15 -- Dokar Muhammadu
Kalmomin Yesu; “ku koya masu su bi duk ababuwanda na umarce ku” in an yi masu ‘yan gyare gyare za’a iya samun su a Kur’ani! Ko da shike akwai bambanci sosai tsakanin dokar Kristi da ta Muhammadu. Ko da shike da gaske ne manyan malaman nan hudu a harkar shari’ar musulunci sun zabi ayoyi kimanin 500 wadanda suka zama ginshikin shari’ar. Amma wannan ya hada da ayoyin da sukan tsorata mutane.
“Kada ku riki makiyina kuma makiyin ku masoyi, kuna jefa soyayya zuwa garesu” (Sura al-Mumtahana 60:1)
“Ku auri abinda yayi muku dadi daga mata, biyu-biyu, da uku-uku, da hudu-hudu, sa’annan idan kunji tsoron baza kuyi adalci” (Ku auri) guda (Sura al-Nisa 4:3)
“Kuma wadanda kuke tsoron kiyonsu, to, kuyi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a cikin wuraren kwanciya kuma ku doke su” (Sun al-Nisa 4:34)
“Kakarbi sadaka daga dukiyoyinsu ka tsarkake su, kuma ka tabbatar da kirkinsu da ita (Sura al-Tawba 9:103)
“Kuma barawo da barauniya sai ku yanke hannuwansu bisa sakamakon da suka (sura al ma’ida 5;38) tsirfata, akan azaba daga Allah”
Duk wanda ya gwada dokar Kristi da ta Muhammadu zai gane cewa ruhohi dabam –dabam na mallakar kowace doka. A dokar Muhammadu babu kauna, ba sulhu da Allah, babu sadakarwa don wadansu kuma babu tsarki na Allah da ya zama ma’ auni ga kowa.
Daga bisani, Muhammadu ne da kansa abinda dokarsa ta kunsa. Rayuwarsa (sunna) an daukeshi a matsayi na biyu a abubuwan da suka zama tushen dokokin Musulunci. Kowane musulmi yayi rayuwarsa yadda Muhammadu yayi. In ba haka ba shi ba cikakken musulmi bane. Muhammadu yayi yakoki 29 ya kuma auri mata goma sha biyu ko fiye da haka.
1.16 -- Manufar Dokar Muhammad Na Boye Dana Yesu
Manufan dokar musulunci, sharia, shine zaman lafiya na al’umman musulmai wanda za’a sami kasa ta addini wanda musulunci ke mulki. Musulunci ba addinin da ke bambanta bangaskiya da siyasa bane. Za’a iya gudanar da mulki mai kyau idan an mai da shi a kalkashin shari'ar musulunci. Shari’ar musulunci za’a iya kafa ta idan akwai kasa ta musulmai. Manufan musulunci shine kafa kasa ta addinin musulunci. Kowane bangare na addinin musulunci girma yake yi.
Yesu yace, “masarauta ta ba ta wannan duniya ba ce” (Yahaya 18:36-37). Ikklisiyarsa, tare da wadanda ya kira daga al’ummai, sune suka zama masarautarsa ta ruhaniya a duk inda suke. Zumuntar almajiransa ne mafarin mulkinsa mara matuka (Yahaya 13:34-35). An kalubalance su dasu zama gishirin duniya da kuma hasken duniya. Yesu bashi da manufar kafa gwamnatin addinin Krista amma shi canza mabiyansa su yi biyaya da umarninsa kuma su yi tasiri a duk kasashen da suka sami kansu.
1.17 -- Ina Tare Da Ku
In dan sakon Yesu Kristi ya kaskantar da kansa, ya gane kasawarsa, ya furta, Yesu yakan gaya masa” bude idanun ka kaga! Ina nan, ina raye! Bazan barka kai kadai ba! Ina kaunar ka! Zan taimake ka! Zan rike ka har zuwa tsufarka!”
An ce Yesu ya taba nuna wa wani mabiyinsa a mafarki takon sawaye a yashi mai danshi yayi bayani cewa, “Duba na raka ka na tsawon lokaci har zuwa wannan lokacin” lokacin da sawayen suka bata a gangaren dutse mai hatsari, mai mafarkin ya tambaya,” me ya sa ka barni ni kadai a lokacin da nake bukatar ka? Ubangiji ya amsa yace, “na goye ka har zuwa lokacin da hanyar tayi kyau” kaunar Kristi yafi gaban tunaninka. Ya tabbatarwa dan sakonsa, “Babu wanda zai iya kwace su a hannu na” (Yahaya 10:28). Kasancewar Yesu madaukaki a ko ina zai karfafa mu mu tsaya cikin bangaskiya da ci gaba da yi masa hidima.
1.18 -- Zuwa Iyakacin Duniya
A yau, dubban mishanarai a kasashen duniya dayawa suna yi wa Yesu Almasihu hidima cikin aminci har ma a wuraren da makiyan Yesu suke mulki. An kona ikklesiyoyi, Krista masu kwazo an kushe su, ana yi musu burga da tsanani. Wadansu an gana musu azaba, wadansu kuwa sun gudu. Wadansu da yawa suna a boye. Tsoro kan kusa sa su kasa yin wani abu.
Amma Yesu ya tabbatar mana da cewa, “Abinda ya same ku, ni ya fara samu”. Zafin ciwo a kafa yakan fara zuwa a bargo ne kafin ya bazu a jiki. Yesu, wanda shine kan ikklesiya, shine yakan fara jin ciwon da ma’aikatansa suke ji, kafin su suji. Dan rago na Allah na tareda mu cikin kuncin mu har zuwa karshe. Yau akwai shan wahala da dama domin Kristi, amma daukakan da ke biye yafi gaban wahalar da muke sha.
1.19 -- Har Zuwa Rana Ta Karshe
A cikin baftismar ka Yesu yayi maka alkawali cewa zai kasance da kai kowane lokaci a rayuwarka muddan baka kauce ba. “Har cikin hatsari ko mutuwa, zai kasance da kai,” Nine tashin matattu nine kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, koya mutu zai nayu. Wanda kuwa ke raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan? (Yahaya 11:25-26) Yesu yana so ya lura da kai har zuwa tsufarka har ma bayan ka mutu. (Zabura 23:4-6).
1.20 -- Ko allah yana tare da musulmansa?
An rubuta a Kur’ani cewa lokacin da Muhammadu ya gudu daga Makka zuwa Madina, ya buya a wani kogo sa’annan ya gaya wa Abubakar, “Dagaske, Allah na tare da mu”. Bayan wannan ne musulman da aka tsananta suka ji gwamman-gwamma. (Sura al-tawba 9:40).
Abin takaici shine, wannan Allah wanda ya ta’azantar da Muhammadu ba Allah na gaskiya bane domin Allahn Kur’ani ya fada sau 17 cewa shi bashi da da kuma, Yesu bai mutu a kan giciye ba. (Sura al-Nisa 4:157). Uban Yesu Kristi bashi tare da Musulmai. Sun musanci kafara ta mutuwar Yesu, kuma sunce wani ruhu, mai suna Jibra’ilu shine Ruhu Mai Tsarki. Ruhun da ke jagorantar musulmai yana iza su yin gaba da Krista. Mun bada gaskiya cewa banda Allah Uba, da Da, da Ruhu Mai Tsarki, babu wa ni Allah.
1.21 -- ‘Kalma Duka’ Sau Hudu A Cikin Babbar Sako
Yesu rayayye ya tabbabar wa almajiransa da DUKA iko a sama da kasa an bashi saboda haka, suje cikin duniya su almajirtarda DUKA al’ummai suna yi musu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. Su koya musu su kiyaye DUKA umarnansa; ya yi wa almajiransa alkawalin zai kasance tare da su har DUKA iyakacin zamani.
Yesu yana karfafa ka da ka dogara da wannan furci “Duka” saboda cin nasara cikin aikin da ya baka. Zai taimakeka ka kiyaye umarnansa, ba zai bar masu yi masa hidima su kadai ba. A karshe, za ka ganshi.
1.22 -- Tambayoyi
In ka yi binciken wannan ‘yar littafi a hankali, zaka iya amsa wadannan tambayoyi. Wanda ya amsa 90 bisa 100 na duka tambayoyi na ‘yan litattafai takwas a cikin wannan jeri dakyau za’a ba shi takardan shaida daga cibiyar mu a kan
Bincike a mataki na Gaba
a hanyoyi masa taimakowa akan magana da musulmai
game da Yesu Kristi.
Wanda karfafawa ne don hidima na Kristi a nangaba.
- Menene Yesu ke ba duniya bayan mutuwa da tashinsa daga matattu?
- Wannene ya cancanta ya zama dan sako na Yesu?
- Me ya sa Yesu ya kalubalanci har masu shakka a cikin mabiyansa a Babbar sako?
- Me ake nufi da Yesu ya karbi duka iko a sama da kasa?
- Me ya sa Uba bai yi fargaban dansa zai yi masa tawaye ba bayan ya danka masa duka iko da karfi?
- Me ya sa Yesu ya umarci mabiyansa su “tafi” ba su “zauna” ba?
- Ta ya ya zaka iya samun mutumin da ke jiran shaidarka, kuma tayaya zaka iya magana da shi?
- Ta yaya zaka iya tara almajirai kewaye da kai?
- Me ya sa wannan Babbar sako na jagorantar mu zuwa ga 'ya 'yan Isma’ilu da na Yakubu? Wani kasa ne ko addini da ba’a hada su a cikin shirin bishara ba?
- Kimanin mutum nawa ne bisa dari na dukan yawan mutanen duniya suna kiran kansu Krista a yau? A gaskiya, menene wannan ke nuna maka?
- Me ake nafi da yin baftisma cikin sunan Uba, da na Da, da na Ruhu Mai Tsarki?
- Yaya dayantakan Triniti Mai Tsarki ya bayyana cikin Babar sako?
- Ta ya ya zaka iya karbar iko da jagora cikin hidimar ka don Kristi?
- Me ya sa baftisma da maya haihuwa sune farkon rayuwar Krista?
- Menene banbancin yi wa wadanda ba Krista ba wa’azi da koya wa masu bada gaskiya?
- Wadanne darussa ne zamu koyawa masu bada gaskiya da aka yi musu baftisma?
- Umarnai nawa ne na Kristi zaka iya samu a bisharu guda hudu? Wadanne ne a cikinsu kake tsammani sun fi muhimmanci ga musulmi?
- Menene banbanci tsakanin barata tawurin bangaskiya kadai da bukatar aikata nagargarun ayuka tawurin biyayya ta bangaskiya wanda kyauta ce ta alheri?
- Menene ma auni na shari’a a Sabon Alkawali?
- Me ya sa umarni na uku a Babbar sako ya kakkarya fahariyar kowane Malami, mai bi ko mai hidima in zai fada wa kansa gaskiya?
- Me ya sa Yesu yayi alkawali, “gama ina tare da ku”?
- Me ya sa Yesu yayi alkawalin kasancewa da kai ko ina da kowane lokaci in kana hidima cikin sunansa?
- To yaya musulmai zasu bada gaskiya cewa Yesu (ISA) yana raye tare da Allah?
- Me yasa ya zama da wuya ga musulmai su yi tunani cewa alloli biyu zasu iya rayuwa tare har abada me yasa bai zama da matsala ga Krista ba?
- Ka rubuta Babbar umarni na musubi (da Hausa) a bayyane (kana nuna sura da aya) ka gwada shi da Babbar umurni na musulmai (da Hausa) a bayyane (kana nuna sura da aya) ka gwada shi da Babbar umurni na Krista.
- Ta wace hanya da kuma cikin wadanne kasashe ne musulunci ke yaduwa a matakai uku na girman musulunci. In an kasa yawan mutanen duniya bisa dari, kashi nawa ne musulmai a yau? Fadi yawan musulmai a kasar ku.
- Me ka gane da musulmi ya jure zama da mabiya wadansu addinai. Za’a dade ana wannan tafiyar? A wane lokaci kake gani zaifara rashin hakuri da wadanda addinin su ba daya ba?
- Me ya sa Muhammadu ya ki amincewa da dayantakar Triniti?
- Menene koyaswar Kur’ani game da baftisma ta Krista?
- Wadanne bambance bambace ne akwai tsakanin umarnai na Muhammadu (shari’a) da kuma umurnai na Yesu Kristi a Bishara?
- Menene manufar shari’ar musulunci da manufar Umarnin Kristi?
- Muhammadu ne ma aunin Shari’ar musulunci: menene wannan ke nufi ga Musulumi?
- Me yasa Muhammadu bai iya yi wa mabiyansa alkawarin,” Gama, ina tare da ku har iyakar zamani” ba?
- Menene kalma ta “DUKA” guda hudu a cikin Babbar Umarni ke nufi?
Duk wanda ke amsa wadannan tambayoyi an yarda masa ya tuntubi wani mutumin da zai iya taimakonsa amsar su. Muna jiran amsoshin tambayoyin ku tare da cikakken adireshin ku a takardunku ko e-mail. Muna yin adu’a domin ku, Ubangiji mai Rai, ya baku haske, ya aika, ya jagoranta, ya karfafa, ya tsare kuma ya kasance da ku dukan rayuwarku.
Naku cikin Hidimarsa
Abd al- masih da ‘yan uwansa cikin ubangiji.
Ku aika da amsoshin ku zuwa:
The Good Way Mission, Nigeria
Nguru Road,
P. O. Box 671, Maiduguri,
Borno State.
Ko
GRACE AND TRUTH
P.O.Box 1806
70708 Fellbach
GERMANY
Kokuwa ta wayar e-mail zuwa:
info@ grace-and-truth.net